An Zargi Faransa, Kasashe 2 da Luguden Wuta a Nijar, Rasha Ta kai Dauki

An Zargi Faransa, Kasashe 2 da Luguden Wuta a Nijar, Rasha Ta kai Dauki

  • Gwamnatin sojin Nijar ta ce kasashen Faransa, Benin da Ivory Coast ne ke da alhakin kai hari kan sansanin soja da ke filin jirgin saman Niamey
  • Shugaba Janar Abdourahamane Tiani, ya yi ikirarin cewa harin ya samu goyon bayan shugabannin ƙasashen, inda ya yaba wa kasar Rasha
  • Rahotanni sun bayyana cewa harin ya jikkata sojoji huɗu tare da kashe mutane akalla 20 da ake zargin maharan ne, yayin da aka kama wasu 11

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Niamey – Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta zargi ƙasashen Faransa, Benin da Ivory Coast da ɗaukar nauyin wani hari da aka kai kan sansanin soja da ke filin jirgin saman kasa da kasa na Diori Hamani a birnin Niamey.

Zargin ya fito ne daga bakin shugaban gwamnatin sojin ƙasar, Janar Abdourahamane Tiani, wanda ya bayyana hakan a gidan talabijin na gwamnati.

Kara karanta wannan

An 'gano' wani shiri da masu juyin mulki suka yi domin hana Buhari ba Tinubu mulki

Abdourahamane Tiani da Emmanuel Macron
Emmanuel Macron a hagu, Abdourahamane Tiani a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta ce Tiani ya yi bayani ne bayan fashe-fashe da musayar wuta da aka ji a daren Laraba zuwa safiyar Alhamis a kusa da filin jirgin saman, wanda ke kusan kilomita 10 daga fadar shugaban ƙasa.

Nijar ta zargi Faransa da kasashe

A yayin jawabinsa, Janar Tiani ya ce Faransa ƙarƙashin shugaba Emmanuel Macron, tare da Benin da ke ƙarƙashin Patrice Talon da Ivory Coast ƙarƙashin Alassane Ouattara, ne ke bayan harin da aka kai.

Sai dai duk da ikirarin da ya yi, shugaban kasar bai gabatar da wata hujja kai tsaye da za ta tabbatar da zargin nasa ga kasashen ba.

Tiani ya bayyana kalamansa ne bayan ya kai ziyara sansanin sojin da ke filin jirgin saman Diori Hamani, inda ya ce gwamnati ba za ta yi shiru ba kan abin da ya kira tsoma baki daga ƙasashen waje ba.

An kashe mutane a harin Nijar

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An fallasa yadda aka shirya kashe Tinubu, Shettima da wasu mutum 2

Reuters ta rahoto cewa ministan tsaron Nijar, Salifou Modi, ya ce harin ya ɗauki kusan mintuna 30 kafin sojojin ƙasar su kai martani ta sama da ta ƙasa.

Ma’aikatar tsaron ta sanar da cewa sojoji huɗu sun jikkata yayin artabun, yayin da aka kashe mutane 20 da ake zargin maharan ne.

Baya ga haka, hukumomin tsaro sun ce sun kama mutane 11 da ake zargi da hannu a harin, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin domin gano cikakken abin da ya faru.

Daukin da Rasha ta kai Nijar

A cikin jawabinsa, Janar Tiani ya gode wa sojojin Rasha da ke sansanin, inda ya ce sun taka muhimmiyar rawa wajen kare yankin da aka ba su alhakin tsaro.

Gwamnatin Nijar ta ce haɗin gwiwa da Rasha na da muhimmanci wajen yaƙi da ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya da ke da alaƙa da al-Qaeda da ISIL, duk da cewa babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin har zuwa yanzu.

Abdourahamane Tiani
Shugaban Nijar tare da sojojin kasar. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A halin da ake ciki, ƙasashen Faransa, Benin da Ivory Coast ba su fitar da wata sanarwa ko martani kai tsaye kan zargin da gwamnatin sojin Nijar ta yi ba.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

An harbi sojojin Nijar a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan banga sun bude wa sojojin Nijar wuta yayin da suka tsallako Najeriya a iyakokin kasashen biyu.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun saba tsallake iyakar su shigo Najeriya domin diban ruwa ko wasu kananan bukatu.

Rudunar tsaron Najeriya ta sanar da cewa ta tattauna da Nijar kan abin da ya faru kuma an shawo kan lamarin cikin fahimtar juna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng