Masu Zanga Zangar Amurka na Fita kan Titi da Bindigogi, Trump Ya Damu
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce gwamnatinsa na sake nazari bayan jami’an shige da fice sun harbe Alex Pretti, ‘dan shekara 37, a Minneapolis
- Lamarin ya tayar da zanga-zanga a Minneapolis da wasu manyan biranen Amurka, inda hukumomin jiha da na tarayya ke musayar ra’ayi kan lamarin
- Gwamnatin Amurka ta kare jami’in da ya yi harbin, yayin da hukumomin gari da iyalan marigayin ke musanta zargin cewa ya yi barazana da bindiga
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa na “sake nazari” dangane da harbin da ya yi sanadin mutuwar jami'in lafiya, Alex Pretti da jami’an shige da fice suka harba.
Lamarin ya kara tsananta ce-ce-ku-ce tsakanin hukumomin jiha da na tarayya, musamman ganin cewa wannan shi ne karo na biyu cikin ‘yan makwanni da jami’an tarayya suka kashe wani dan kasar Amurka a zanga-zanga.

Source: Getty Images
Trump ya fadi hakan ne a wata hira da jaridar Wall Street Journal, inda ya kuma nuna yiwuwar janye jami’an tarayya daga birnin Minneapolis nan gaba, sai dai bai bayyana lokacin da hakan zai faru ba.
Martanin Donald Trump kan zanga-zanga
A cewar rahotanni, Trump ya ce an tambaye shi sau biyu ko jami’in da ya harba ya yi daidai, inda ya amsa da cewa gwamnatinsa na duba lamarin sosai kafin yanke hukunci.
Ya kara da cewa:
“Ba na son duk wani harbi. Ban son hakan.”
Sai dai Trump ya kuma nuna damuwa kan halartar zanga-zanga dauke da makami, yana mai cewa hakan ma ba abu ne mai kyau ba.
Ministar tsaron cikin gida, Kristi Noem, ta kare jami’in da ya yi harbi, tana mai cewa an harbi Pretti ne saboda yana nuna bindiga a lokacin da jami’an suka fuskance shi.
Ce-ce-ku-ce kan yadda harbin ya faru

Kara karanta wannan
Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame
Hukumomin yankin Minneapolis sun musanta bayanin gwamnatin tarayya, suna cewa bindigar da Pretti ya mallaka tana da lasisi, kuma an cire ta daga gare shi kafin a harbe shi.
Rahoton the Guardian ya nuna cewa sun jaddada cewa mallakar bindiga a bainar jama’a halal ne a jihar Minnesota muddin mutum na da izini.
Iyalan marigayin sun bayyana cewa Pretti na da izinin rike bindiga, amma ba su taba sanin yana fita dauke da ita ba. Sun ce abin da ya faru ya bar su cikin alhini da tambayoyi masu yawa.
Rundunar ‘yan sandan yankin ta tabbatar da cewa Pretti dan kasa ne mai bin doka, kuma ya cika sharuddan mallakar bindiga a jihar.
Zanga-zanga ta barke a fadin Amurka
Bayan harbin, dubban mutane sun fito zanga-zanga a Minneapolis da wasu birane kamar New York, San Francisco, Boston da Providence.
Rahotanni sun ce zanga-zangar ta biyo bayan wata babbar tattaki da aka yi a Minneapolis kwana guda kafin kisan, inda jama’a suka yi tir da yadda jami’an shige da fice ke gudanar da ayyukansu.

Source: Getty Images
Gwamnan Minnesota, Tim Walz, ya yi gargadi cewa Amurka na fuskantar wani muhimmin mataki a tarihinta, yana mai cewa irin wadannan abubuwa na iya canza alkiblar siyasa da tsaro idan ba a dauki mataki cikin adalci ba.
Trump na kashe 'yan ta'adda a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa suna nan suna cigaba da kashe 'yan ta'adda a Najeriya.
Trump ya yi magana ne a wani taron tattalin arziki da aka yi a birnin Davos na kasar Switzerland, inda shugabannin duniya suka hallara.
Amurka ta jaddada kudirinta na cewa za ta cigaba da taimakon Najeriya da kayan yaki domin ganin ta murkushe 'yan ta'adda baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

