Bayan Kisan Kano, Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Gargadi kan Hukuncin Kisa
- Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan karuwar aiwatar da hukuncin kisa a 2025, duk da yadda kasashe da dama ke janyewa ko dakatar da shi
- Rahoton majalisar ya ce safarar miyagun kwayoyi da hukunta mutane kan laifuffukan da ba su kai a kirasu “manya” ba ne suka fi haddasa hukuncin kisa
- Ta ce sai dai a lokaci guda, wasu kasashe sun dauki matakai na rage ko soke hukuncin kisa, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce alama ce mai karfafa gwiwa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Duniya – Hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, OHCHR, ta bayyana karuwar amfani da hukuncin kisa a 2025 a matsayin abin da ke tayar da hankali.
Majalisar Dinkin Duniya ta dade tana kira da a soke hukuncin kisa a duk fadin duniya, tana mai jaddada cewa ‘yancin rayuwa hakki ne na asali da ya kamata a kare.

Source: Getty Images
Rahoton UN News ya ce a karkashin yarjejeniyar kasa da kasa kan 'yancin dan Adam, an tanadi cewa kasashen da ba su soke hukuncin kisa ba, su yi amfani da shi kawai a lokuta na musamman kan manyan laifuffuka mafi muni.
Hukuncin kisa na karuwa inji OHCHR
A cewar OHCHR, karuwar hukuncin kisa a 2025 ta samo asali ne daga hukunta masu safarar miyagun kwayoyi da kuma aiwatar da hukuncin kan abubuwan da ba su kai matsayin “manyan laifuffuka” ba.
Babban kwamishinan kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya ce hukuncin kisa ba ya hana aikata laifi yadda ya kamata.
TRT ta rahoto ya ce hukuncin na iya kai ga kashe mutanen da ba su aikata laifi ba, tare da jaddada cewa a aikace ana yawan aiwatar da hukuncin cikin wariya da rashin adalci.
Halin da ake ciki a yankunan duniya
Rahoton OHCHR ya nuna cewa babu wani yanki daya da za a ce shi kadai ke aiwatar da hukuncin kisa a duniya, domin ana ganin hakan a sassa daban-daban.
A Iran, rahotanni sun nuna cewa an kashe akalla mutane 1,500 a 2025, inda kusan kashi 47 cikin 100 ke da alaka da laifuffukan miyagun kwayoyi.
A Isra’ila, ana gabatar da kudurori a majalisa da ke neman fadada hukuncin kisa, musamman ta hanyar wajabta shi kan Falasdinawa kawai.

Source: Facebook
A Saudiyya, adadin hukuncin kisa ya zarce na shekarar 2024, inda aka kashe akalla mutane 356, yawancinsu kan laifuffukan miyagun kwayoyi. A Afghanistan kuma, an ci gaba da hukuncin kisa a bainar jama’a.
Amurka ta aiwatar da hukuncin kisa mafi yawa cikin shekaru 16, inda aka kashe fursunoni 47. A Somaliya an kashe akalla mutane 24, yayin da Singapore ta kashe 17.
Magana kan hukuncin kisa a Kano
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya magantu kan wadanda aka kama da zargin kashe uwa da 'ya'yanta shida.
Gwamnan ya yi alkawarin rattaba hannu domin yankewa wadanda aka kama hukuncin kisa matukar kotu ta zartar musu da hukuncin.
Hakan na zuwa ne bayan jama'a sun yawaita kira ga hukumomi su gaggauta shari'a da yankewa wadanda ke zargi da kashe mutanen hukunci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

