Iran: Trump Ya Fallasa Abin da Shugaban Faransa Ya Fada Masa kan Kasashen Musulmi
- Shugaban Amurka Donald Trump ya fitar da sakonnin sirri da ya musanya da shugabannin Turai kan Greenland da kasashen Iran da Syria
- A abubuwan da Amurka ta fitar, shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce sun yi daidai da Trump kan Syria tare da sha’awar yin aiki tare kan Iran
- Hakan na zuwa ne yayin da batun ikirarin Trump na cewa dole Amurka ta mallaki tsibirin Greenland na kara tayar da ce-ce-ku-ce a siyasar duniya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake tayar da kura a fagen siyasar duniya bayan wallafa sakonnin sirri da ya rika musanyawa da shugabannin Turai, musamman kan batun Greenland, Iran da kuma Syria.
Sakonnin da Trump ya fitar sun nuna yadda tattaunawar shugabanni kan manyan batutuwan duniya ke gudana a bayan fage da ba a saba gani ba.

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ke shirin halartar taro a birnin Davos na kasar Switzerland, inda ya ce zai sanar da shugabannin Turai cewa “dole Amurka ta mallaki” Greenland.
Sakon Faransa kan kasashen Musulmi 2
A cikin sakon da Trump ya wallafa ranar 19, Janairu, 2026, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya rubuta wa Trump yana mai bayyana dangantaka ta kusanci tsakaninsu.
CNN ta rahoto cewa Macron ya ce Faransa da Amurka suna tafiya kan manufa daya game da batun Syria, tare da nuna cewa kasashen biyu na da damar yin manyan abubuwa tare kan kasar Iran.
Sai dai Macron ya bayyana rashin fahimtarsa kan matakin Trump game da Greenland, yana mai kira da a gina hadin kai da yin wasu taruka na musamman a Paris domin tattauna manyan batutuwan duniya.
Wani sako da aka turawa Trump
Wani sako da Firaministan Norway, Jonas Støre, ya aikawa Trump, ya nuna damuwa kan batutuwan Greenland, Gaza, Ukraine da kuma haraji da Amurka kakabawa kasashe.
Støre ya ce kasashensu na son rage daukar zafi da rikice-rikice, tare da bukatar a yi hadin kai tsakanin kasashen Yamma domin tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta.
Ya kuma ba da shawarar yin wayar tarho kai tsaye da Trump domin tattauna wadannan batutuwa cikin natsuwa da Kwanciyar hankali.
Donald Trump ya yi martani mai zafi
Trump ya mayar da martani cikin sigar da ta jawo ce-ce-ku-ce, inda ya danganta matsayarsa da batun lambar yabo ta Nobel Peace Prize da bai samu ba.
Ya ce tun da Norway ba ta ba shi lambar ba duk da abin da ya kira “dakatar da yaki takwas”, yanzu zai fara tunanin abin da ya fi amfani ga Amurka maimakon zaman lafiya.

Source: Getty Images
Trump ya kalubalanci ikon Denmark kan Greenland, yana mai cewa ba ta da karfin kare yankin daga barazanar Rasha ko China, tare da jaddada cewa tsaron duniya ba zai tabbata ba sai Amurka ta samu cikakken iko da Greenland.
Iran ta yi muhawara da Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dinkin duniya ta yi zama na musamman game da abubuwan da Amurka ta fada a kan kasar Iran.
Wakilan Amurka a majalisar dinkin duniya sun bayyana cewa Donald Trump zai dauki mataki idan aka cigaba da kashe masu zanga-zanga a Iran.
Jakadan Iran a majalisar ya yi tir da abin da Amurka ta fada, yana mai cewa Tehran ba zai gaza ba wajen mayar da martani idan aka kai masa hari.
Asali: Legit.ng


