Yadda Amurka Ta Dogara da Rahoton Inyamurin Dan Kasuwa Mazaunin Onitsha Wajen Kai Hari a Najeriya

Yadda Amurka Ta Dogara da Rahoton Inyamurin Dan Kasuwa Mazaunin Onitsha Wajen Kai Hari a Najeriya

  • Rahoto ya nuna Amurka ta dogara da bayanan Emeka Umeagbalasi, wani ɗan kasuwa daga jihar Anambra, kafin ta kai hare-haren jiragen sama a Najeriya
  • Umeagbalasi ya amince cewa yawancin bayanansa daga Google da rahotannin kafafen yada labarai ne, kuma ba ya yawan tabbatar da sahihancin alkaluman da yake fitarwa
  • Wadannan bayanai ne suka taimaka wajen rinjayar ‘yan majalisar Amurka da kuma Trump, wanda daga bisani ya amince da kai farmakin soja a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

New York, Amurka - Rahoton jaridar New York Times ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta dogara ne da bayanai daga wani Emeka Umeagbalasi, mai sayar da kayan ababen hawa a Onitsha, jihar Anambra, kafin ta kai hare-haren jiragen sama a Najeriya.

A watan Oktoba, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake sanya Najeriya a matsayin “ƙasar damuwa ta musamman” saboda zargin kisan kiyashi da ake yi wa kiristoci a kasar.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama mutum 3 da ake zargi da kashe matar aure da yaranta 6 a Kano

Amurka da binciken Umeagbalasi kan kisan kirista a Najeriya
Hotunan Umeagbalasi da ke rura wutar karerayin kisan kiristoci a Najeriya | The New York Times, Taiwo Aina
Source: UGC

A kalaman Trump a wancan lokacin:

“Addinin Kiristanci na fuskantar barazanar rayuwa a Najeriya. Dubban Kiristoci na mutuwa.”

Trump ya ayyana yakar masu kisan kirista a Najeriya

Kana ya bayyana tabbatar da daukar matakin kare mabiya addinin kirista a Najeriya ta hanyar yakar wadanda yake zargi da yi masu kisan kiyashin.

Wata guda bayan haka, Trump ya yi barazanar cewa ma’aikatar soja ta Amurka za ta kutsa Najeriya “da makamai a hannu” domin hallaka ‘yan ta’adda masu tsaurin bin Musulmi idan gwamnatin Najeriya ba ta dakile zargin kisan kiyashin ba.

A ranar 26 ga Disamba, Amurka ta kaddamar da hare-haren jiragen sama kan ‘yan ta’addan ISIS a Arewa maso Yammacin jihar Sokoto bias “bukatar hukumomin Najeriya.”

Batun Umeagbalasi da kisan kirista a Najeriya

Rahoton na New York Times ya bayyana Umeagbalasi a matsayin wanda ya kafa ƙungiyar International Society for Civil Liberties and Rule of Law (Intersociety).

Kara karanta wannan

Harin Amurka: An 'gano' inda 'yan ta'adda ke tserewa saboda ruwan wuta a Sokoto

Haka nan, ta ce ya kasance

“Wata majiya mai ban mamaki da ‘yan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Republican suka yi amfani da shi wajen yada ra’ayin cewa Kiristoci ne aka mayar da hankali wajen kashewa a Najeriya.”

Umeagbalasi da matarsa suna gudanar da wannan ƙungiyar ne daga cikin gidansu, kamar yadda ya bayyana yayin tattaunawa da wakilan jaridar.

‘Yan majalisar Amurka Riley Moore da Ted Cruz, wadanda Trump ya roƙa su binciki zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya, tare da dan majalisa Chris Smith na New Jersey, duk sun dogara ne da binciken sa.

Yadda Umeagbalasi ke tattara bayanansa

An ambaci cewa Umeagbalasi ya ce ya tattara bayanai kan mutuwar Kiristoci 125,000 tun daga 2009, bisa bincike daga kafar zakulo bayanai ta Google.

Haka zalika, ya ce ya dogara da rahotannin jaridun Najeriya, wasu majiyoyi, da ƙungiyoyi masu fafutuka irin su Open Doors, wanda Trump ya taɓa amfani da bayanan su.

Amurka da Umeagbalasi kan batun kisan kirista a Najeriya
Umeagbalasi zaune cikin shagonsa na sayar da kayan ababen hawa | Taiwo Aina, The New York Times
Source: UGC

Sai dai ya amince cewa bai tabbatar da bayanan da ya dogara da su ba, kuma bai cika zuwa yankunan da ake kai hare-hare ba. Sau da yawa yana ɗaukar addinin wadanda abin ya shafa ne bisa la’akari da wurin da harin ya faru.

Kara karanta wannan

An gano gargadin da aka yi wa Donald Trump har Amurka ta fasa kai hari Iran

Ya bayyana wa cewa tushen bayanan sa su ne “wuri da sararin inda abin ya faru”, kuma ya kira hanyar sa ta bincike “daya daga cikin tsofaffin hanyoyin dabi’a a duniya.”

Umeagbalasi ya dogara da guragun bayanai, galibi maras inganci

Umeagbalasi ya ce yana da digiri a fannin tsaro, zaman lafiya da warware rikice-rikice daga National Open University of Nigeria, kuma ya bayyana kansa a matsayin masani mai zurfi a bincike.

Rahoton ya kara da cewa ya yi ikirarin cewa akwai “shirin hallaka Kiristoci gaba daya a Najeriya”.

A cewarsa, akwai kusan coci 100,000 a kasar, kuma 20,000 daga cikinsu an daidaita su a cikin shekaru 16 da suka gabata, inda ya ce ya samo bayanan ne ta hanyar bincike a Google.

Dogaro da bayanai daga ‘yan majalisa uku; wadanda suka saba amfani da bayanan Umeagbalasi, Trump kawai ya kaddamar da hare-hare a Najeriya a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

A zahiri da kuma rahotanni na gaskiya ba hasashe da zato irin na Umeagbalasi, adadi da alkaluman sun bambanta da abin da Amurka ta dogara da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng