An Gano Gargadin da aka Yi wa Donald Trump har Amurka Ta Fasa kai Hari Iran
- Wasu jami’an Isra’ila da kasashen Larabawa sun ba gwamnatin Donald Trump shawarar ta yi hattara kan batun kai manyan hare-haren soja Iran
- Sun nuna cewa duk da matsin lambar zanga-zangar da ake yi a Iran, tsarin mulkin kasar bai kai matakin da hari daga waje zai kawo sauyi nan take ba
- Shawarwarin sun zo ne yayin da Shugaba Trump ke dubi daban-daban kan yadda Amurka za ta tunkari rikicin Iran, ciki har da hanyoyin da ba na soja ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Jami’an Isra’ila da wasu manyan jami’ai daga kasashen Larabawa sun shaida wa gwamnatin Shugaba Donald Trump cewa bai dace a gaggauta kai manyan hare-haren soja Iran a halin yanzu ba.
Wadannan shawarwari sun biyo bayan ci gaba da zanga-zanga a Iran, lamarin da ya sanya Trump ke barazanar daukar matakin soja.

Source: Getty Images
NBC ta ce tattaunawar ta shafi manyan shugabannin siyasa da na sojan Amurka, inda aka nuna cewa akwai bukatar yin nazari mai zurfi kafin daukar matakin da zai iya tayar da rikici a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya.
Iran: Gargadin da aka yi wa Donald Trump
Jami’an Isra’ila da na Larabawa sun bayyana cewa, a fahimtarsu gwamnatin Iran na fuskantar matsin lamba amma har yanzu ba ta kai matakin rushewa ba.
Rahotanni sun nuna cewa sun yi imanin cewa hari daga waje a yanzu zai iya kasa cimma burin da ake nema na kawo sauyi cikin gaggawa.
Wasu daga cikinsu sun ce ya fi dacewa a jira a ga yadda zanga-zangar za ta kara raunana tsarin mulkin, ganin cewa halin da ake ciki na iya sauyawa cikin kankanin lokaci, ko dai zuwa karuwar rikici ko kuma sassauci daga bangaren gwamnati.

Source: AFP
Sun kuma yi gargadin cewa kai hari daga waje na iya bai wa gwamnatin Iran damar hada kan jama’a a karkashinta, lamarin da zai iya rage tasirin masu zanga-zangar.
Matsayar Donald Trump game da Iran
Shugaba Donald Trump ya bayyana a lokuta da dama cewa yana shirye-shiryen kai hari a Iran lura da abubuwan da ke faruwa.
Jami’an fadar White House sun ce shugaban kasa yana sauraron shawarwari daga bangarori daban-daban, amma shi ne zai yanke hukunci a karshe.
Rahoton New York Times ya nuna cewa mai magana da yawun fadar White House ya ce diflomasiyya ita ce zabin farko, amma ba tilas ba ne ta kasance ita kadai.
Trump ya ce abubuwa sun fara lafawa Iran
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi magana kan zanga-zangar da ake cigaba da yi a kasar Iran.
A bayanin da ya yi, Trump ya ce ya samu labari daga majiya mai tushe cewa an dakatar da kashe masu zanga-zanga a fadin kasar.
Hakan na zuwa ne bayan Trump ya ce yana duba yiwuwar kai hari da niyyar kai dauki ga Iraniyawa da suka shafe kwanaki suna zanga-zanga.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

