Magana Ta girma: Iran da Amurka Sun Nuna wa Juna Yatsa a Taron Tsaro na duniya
- Amurka ta bayyana a gaban majalisar dinkin duniya cewa Shugaba Donald Trump zai dauki mataki kan zargin kisan masu zanga-zanga a Iran
- Iran ta mayar da martani da cewa ba ta neman rikici, amma za ta mayar da martani a kan duk wani hari kai-tsaye ko a kaikaice da aka kai mata
- Kasashe kamar Rasha da Denmark, tare da shugaban majalisar dinkin duniya, sun yi kira da a yi taka-tsantsan domin kauce wa faɗaɗa rikicin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Amurka ta bayyana wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya cewa tana goyon bayan mutanen Iran masu zanga-zanga, tare da jaddada cewa Shugaba Donald Trump zai dauki mataki.
Maganar ta fito ne a zaman Kwamitin Tsaro da Amurka ta nema, yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan yiwuwar shiga tsakani a rikicin Iran.

Source: Getty Images
Reuters ta rahoto cewa gwamnatin Iran ta yi gargadi cewa za ta mayar da martani ga duk wani nau’in hari, tana mai zargin Amurka da ƙoƙarin tsoma baki cikin harkokinta.
Abin da Amurka ta ce a kan Iran
Jakadan Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya, Mike Waltz, ya shaida wa Kwamitin Tsaro cewa Shugaba Donald Trump mutum ne mai aikata abin da ya fada.
Waltz ya ce Amurka na tare tare da abin da ya kira “jaruman mutanen Iran,” yana mai cewa zanga-zangar da ke gudana ba wata makarkashiyar ƙasashen waje ba ce kamar yadda Tehran ke iƙirari.
A cewarsa, gwamnatin Iran na yada wannan magana ne saboda tsoron ƙarfin jama’arta da ke fitowa kan tituna suna neman sauyi a kasar.
Martanin Iran ga kasar Amurka
Mataimakin jakadan Iran a majalisar dinkin duniya, Gholamhossein Darzi, ya bayyana cewa ƙasarsa ba ta neman ta’azzara rikici ko fuskantar yaƙi.
Aljazeera ta rahoto cewa Iran ta zargi Waltz da ke wakiltar Amurka da ƙarya da karkatar da gaskiya domin ɓoye rawar Amurka a rikice-rikicen da ke haifar da tashin hankali a Iran.
Darzi ya jaddada cewa duk wani hari, kai-tsaye ko a kaikaice, za a fuskance shi da martani mai ƙarfi, daidai gwargwado, kuma bisa doka, yana mai cewa wannan ba barazana ba ce illa bayyana gaskiya.

Source: Getty Images
Matsayin Rasha da sauran ƙasashe
Jakadan Rasha, Vassily Nebenzia, ya zargi Amurka da kiran zaman Kwamitin Tsaro ne domin halasta tsoma baki da yiwuwar kai hare-hare don kifar da gwamnati mai cin gashin kanta a Iran.
A nata bangaren, wakiliyar shugaban majalisar dinkin duniya, Martha Pobee, ta isar da saƙon Antonio Guterres na yin taka-tsantsan domin kauce wa asarar rayuka da faɗaɗa rikici a yankin.
Trump ya yi magana kan Iran
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ya samu labari an daina kashe masu zanga-zanga a kasar Iran.
Trump ya bayyana haka ne kwanaki bayan ya yi barazanar cewa zai kai hari Iran domin ceto masu zanga-zanga da ba su kariya.
Duk da haka, shugaban kasar ya ce zai sake bincike domin tabbatar da abubuwan da ke faruwa da masu zanga-zangar Iran.
Asali: Legit.ng

