Zanga Zanga Ta Karu a Amurka bayan Hukumomi Sun Yi Harbi da Bindiga

Zanga Zanga Ta Karu a Amurka bayan Hukumomi Sun Yi Harbi da Bindiga

  • Wani jami’in gwamnatin Amurka ya harbi wani ɗan ƙasar Venezuela a Minneapolis yayin da ake ci gaba da takaddama yayin zanga-zanga
  • Lamarin ya faru ne bayan jami’an tsaro sun ce mutumin ya yi yunƙurin tserewa tare da ƙin bin umarni, abin da ya kai ga harbi a ƙafa
  • Harbin ya zo ne mako guda bayan kisan wata mata a birnin, lamarin da ya tayar da zanga-zanga da muhawara a kan siyasar Amurka a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Birnin Minneapolis ya sake shiga yanayin tashin hankali bayan wani jami’in gwamnatin Amurka ya harbi wani ɗan ƙasar Venezuela, lamarin da ya ƙara rura wutar rikici da suka biyo bayan kisan wata mata a makon da ya gabata.

Wannan sabon lamari ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar adawa mai ƙarfi ga matakan korar baki da gwamnati ke aiwatarwa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wani abu da ake zargin bam ne ya tarwatse da mutane a Adamawa

Masu zanga zanga a Amurka
Jama'a yayin zanga-zanga bayan harbin dan kasar Venezuela. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Financial Times ya ce jami’an tsaro sun tabbatar da cewa mutumin, wanda ya shigo ƙasar Amurka a shekarar 2022, ya samu rauni.

An harbi dan Venezuela a Amurka

A cewar bayanan gwamnati, mutumin ya yi ƙoƙarin tserewa daga jami’in tsaro lokacin da aka tsaida shi. An ce ya ƙi amincewa a kama shi, sannan an zarge shi da cewa ya kaiwa wani jami’i hari da wani abu mai kama da cebur ko sanda.

Rahotanni sun nuna cewa wasu mutane biyu sun shigo cikin lamarin domin taimaka masa ya tsere, lamarin da ya sa jami’in ya ji rayuwarsa na cikin hatsari.

Saboda haka, ne wasu rahotanni suka ce jami’in ya harba bindiga domin kare kansa, inda harsashin ya samu dan kasar Venezuela a ƙafa.

Rahoton TRT ya nuna cewa an kai mutumin asibiti domin kula da lafiyarsa, kuma an bayyana cewa raunin da ya samu ba zai zama barazana ga rayuwarsa ba, duk da haka, matasa na cigaba da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Zafin siyasa bai hana aiki: Abba ya fadi shirin gwamnati a kan matasa 50, 000 a Kano

Tasirin matakan da ake dauka a Amurka

Faɗaɗa ayyukan jami’an kula da shige da fice ya haifar da adawa daga mazauna birnin Minneapolis, inda ake yawan zanga-zanga da kira ga jami’an da su fice daga yankin.

A makon da ya gabata, wata mata mai suna Renée Nicole Good ta rasa ranta bayan wani jami’in kula da shige da fice ya harbe ta yayin da take cikin motarta.

Wasu masu zanga-zanga a Amurka
Jami'an tsaro na arangama da masu zanga-zanga a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahotanni sun nuna cewa kisan matar ya ya girgiza jama’a, inda ya janyo fushin ‘yan siyasa da dama da kuma rabuwar ra’ayi tsakanin jam’iyyun siyasa.

Kalli bidiyon yadda ake zanga-zangar a kasa:

Ana zanga zanga a kasar Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa matasa da sauran jama'a na zanga-zangar adawa da jami'an shige da fice a wasu biranen kasar Amurka.

Legit Hausa ta rahoto cewa wasu masu zanga-zanga su yi arangama da da jami'an tsaro yayin da tarzoma ta yi kamari a kan tituna.

Jami'an shige da fice sun yi amfani da borkonon tsohuwa da sinadarai masu saka kaikayi domin tarwatsa masu zanga-zanga a wasu birane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng