Daga Barazanar kai Hari, Trump Ya Ja da Baya, Ya Fadi Alheri game da Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa rahotanni da ya samu na nuna cewa gwamnatin Iran ta rage ko dakatar da kashe masu zanga-zanga
- Hakan na zuwa ne bayan barazanar da Donald Trump ya yi ta cewa zai kai hari Iran idan gwamnatin kasar ta farmaki masu zanga-zanga da suka cika tituna
- A gefe guda kuma, Iran ta dauki wasu matakai na tsaro, ciki har da rufe sararin samaniyarta ga jiragen kasuwanci, abin da ya ƙara nuna halin da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Shugaban Amurka Donald Trump ya ce rahotannin da suka zo masa sun nuna cewa hukumomin tsaro a Iran sun dakatar da kashe masu zanga-zanga da ke adawa da gwamnati.
Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Fadar White House, inda ya ce bayanan da ya samu sun nuna cewa ba a shirya aiwatar da kisan gilla ko hukuncin kisa ga masu zanga-zangar ba.

Source: Getty Images
Rahoton New York Times ya ce furucin Trump na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ce-ce-ku-ce kan kai harin sojoji daga Amurka zuwa Iran.
Abin da Donald Trump ya ce kan Iran
A cewar Trump, an shaida masa cewa “kashe-kashe na raguwa a Iran, har ma ana cewa an dakatar da shi,” yana mai cewa wannan bayanin ya fito daga wasu majiyoyi masu tushe daga bangaren Iran.
Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa shugaban Donald Trump bai bayyana majiyar da ta ba shi labarin halin da ake ciki a Iran ba kai tsaye.
Ya kara da cewa zai sake bincike domin tabbatar da sahihancin abin da aka fada masa, yana mai jaddada cewa zai “gani da kansa” idan bayanan sun dace da gaskiya.
Lokacin da aka tambaye shi ko hakan na nufin cewa matakin kai hari Iran ya zo karshe, Trump ya ce gwamnati za ta ci gaba da lura da yanayin, yana mai cewa an ba su bayanai daga wadanda ke da masaniya kan lamarin.
Barazanar hari Iran da zanga-zanga
Tun daga 2, Janairu, 2026 Trump ya sha bayyana cewa Amurka za ta iya kai hari kan Iran idan aka ci gaba da cutar da masu zanga-zanga.
A kwanakin baya, hukumomin tsaro na Iran sun dauki matakan murkushe zanga-zangar, inda aka ruwaito cewa an yi amfani da karfi.

Source: Getty Images
Sai dai saboda katsewar intanet a fadin Iran, ya kasance da wahala a tabbatar da ainihin yadda abubuwa suke gudana a fadin kasar.
Rahotanni sun nuna cewa zanga-zangar ta ragu idan aka kwatanta da makon da ya gabata, amma har yanzu ana ci gaba da nuna damuwa kan tsaro.
A baya-bayan nan, Trump ya bukaci masu zanga-zanga da ya kira “’yan kishin Iran” da su ci gaba da matsin lamba, yana cewa taimako na tafe, kalaman da suka kara tsananta fargabar kai hari.
Kasar Rasha ta gargadi Amurka kan Iran
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin kasar Rasha ta yi magana kan barazanar da shugaban Amurka ke yi a kan zanga-zangar da ake a Iran.
Gwamnatin Rasha ta yi gargadi da cewa kai hari Iran zai kawo matsala ga zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da sauran kasashen duniya.
Yayin da Trump ke barazana, Amurka ta fara janye sojojinta daga sansanonin da ta ke da su a wasu yankunan Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


