Ana Wata ga Wata: Kotu Ta Maye Gurbin Shugaban Venezuela Bayan Amurka Ta Kama shi
- Kotun koli ta kasar Venezuela ta nada mataimakiyar shugaban kasa, Delcy Rodríguez, a matsayin shugabar rikon kwarya bayan sojojin Amurka sun kama Nicolás Maduro
- Kotun ta jaddada bukatar tabbatar da ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnati da kuma kare ikon kasa, sakamakon rashin Maduro
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa Amurka za ta rika kula da harkokin Venezuela na wani dan lokaci, inda za a mayar da hankali kan gyaran ababen more rayuwar man fetur da kuma sauyin shugabanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Venezuela - A ranar Asabar, 3 ga Janairu, 2026, sashen kundin tsarin mulki na kotun kolin Venezuela ya bayar da umarni cewa mataimakiyar shugaban kasa, Delcy Rodríguez, ta karbi ragamar shugabancin kasar na rikon kwarya, bayan kama Nicolás Maduro da sojojin Amurka suka yi da safiyar wannan rana.
A cikin hukuncin da ta yanke, kotun ta bayyana cewa Rodríguez za ta karbi “ofishin Shugaban Jamhuriyar Bolivaria ta Venezuela, domin tabbatar da ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnati da kuma cikakken kare kasa.”

Kara karanta wannan
Bayan yiwa shugaba Maduro daukar amarya, Amurka za ta kwashe man fetur a Venezuela
Rahoton Reuters ya ce kotun ta kara da cewa Rodríguez za ta “karba tare da aiwatar da dukkan iko, nauyi da hurumin da ke tattare da mukamin shugaban kasa a matsayin shugabar rikon kwarya, domin tabbatar da ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnati da kare kasa gaba daya.”

Source: Getty Images
Kotun ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da tattauna lamarin domin “aiwatar da tsarin doka da ya dace wajen tabbatar da dorewar kasa, tafiyar da gwamnati da kuma kare ikon kasa, a sakamakon tilastaccen rashin halartar Shugaban Jamhuriya.”
Sojojin Amurka sun kama Nicolás Maduro
Idan baku manta ba, an kama Maduro ne a wani samame da sojojin Amurka suka kai da sassafe, inda aka fitar da shi daga Venezuela ta jirgin sama.
Wata majiya da ta san abin da ke faruwa ta ce jirgin da ke dauke da shi ya sauka a filin jirgin Stewart da ke jihar New York da misalin karfe 5:00 na yamma agogon yankin, daga nan kuma aka shirya kai shi birnin New York.
Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar Asabar ya bayyana cewa Amurka za ta rika kula da harkokin Venezuela har sai an shirya sahihin sauyin shugabanci.
A kalamansa:
“Za mu rika tafiyar da kasar har zuwa lokacin da za a samu sauyi mai aminci, nagari kuma cikin adalci.”
Da yake zantawa da manema labarai a gidansa na Mar-a-Lago da ke jihar Florida, Trump ya kara da cewa:
“Ba ma son mu tsoma baki wajen saka wani, sannan mu sake komawa irin halin da aka shafe shekaru ana ciki.”
Yadda Trump ke son tafiyar da Venezuela
Trump bai yi karin bayani sosai ba kan yadda Washington ke shirin “tafiyar da” Venezuela, ganin cewa mataimakiyar shugaban kasa, majalisa da sojojin kasar na nan a matsayinsu, kuma sun nuna adawa da matakin Amurka a fili.
Ya ce shirin zai hada da shigar da kamfanonin man fetur na Amurka cikin kasar, tare da ci gaba da tabbatar da haramcin hulda da “duk wani man fetur na Venezuela,” da kuma sanya sojojin Amurka cikin shirin ko-ta-kwana.
A cewarsa:
“Za mu shigar da manyan kamfanonin man fetur na Amurka, mafi girma a duniya, su zuba biliyoyin daloli, su gyara gurbatattun ababen more rayuwa, musamman na man fetur, sannan su fara samar wa kasar kudaden shiga.”
Ya kara da cewa za a aiwatar da wannan ne “tare da wani gungu” da yawancinsu manyan jami’an gwamnatin Amurka ne, inda za a fi mayar da hankali kan gyaran ababen more rayuwar man fetur da kuma tabbatar da cewa “an kula da walwalar al’umma.”
Asali: Legit.ng
