Saudi Ta Yi Ruwan Bama Bamai a Yemen bayan Fuskantar Barazana

Saudi Ta Yi Ruwan Bama Bamai a Yemen bayan Fuskantar Barazana

  • Saudiyya ta ce ta kai hari a tashar jiragen ruwa ta Mukalla bayan gano makamai masu yawa da ake zargin suna da alaka da Hadaddiyar Daular Larabawa
  • Rahotanni sun nuna cewa matakin ya janyo sabuwar takaddama a yankin Gulf, inda kasar UAE ta sanar da janye dakarunta daga Yemen gaba ɗaya
  • Bayanai sun nuna cewa lamarin ya zo ne a daidai lokacin da rikicin Kudancin Yemen ke kara tsananta, musamman bayan shigar kungiyar STC yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yemen – Gwamnatin Saudiyya ta fitar da karin bayani kan harin da kawancen da take jagoranta ya kai a tashar jiragen ruwa ta Mukalla da ke kudancin Yemen, lamarin da ya janyo sabon rikici tsakanin Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Harin ya faru ne bayan Saudiyya ta zargi UAE da tallafa wa wasu kungiyoyin ‘yan aware a Yemen, zargin da ya kai ga bukatar janye dakarun Emirati daga kasar cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa dajin Sambisa, sun yi kaca kaca da Boko Haram

Yariman Saudiyya da wani waje da aka kai hari.
Yarima Salman da wani waje da aka kai hari a kwanakin baya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A martaninta, Al-Jazeera ta rahoto UAE ta sanar da cewa za ta kawo karshen dukkan ayyukan sojojinta a Yemen, tana mai cewa matakin ya zo ne bayan cikakken nazari kan halin tsaro.

Bayanan Saudiyya kan harin Mukalla

Mai magana da yawun kawancen Saudiyya, Manjo Janar Turki al-Maliki, ya ce an kai harin ne bayan gano jiragen ruwa biyu da ke dauke da abubuwan hawa sama da 80 tare da kwantena masu dauke da makamai da harsasai.

A cewarsa, bayan bincike ya nuna cewa wadannan kayayyaki sun shigo tashar Mukalla ne ba tare da sanar da Saudiyya ba, sannan daga bisani aka kwashe su zuwa sansanin al-Rayyan tare da jami’an Emirati.

Al-Maliki ya jaddada cewa an bi dokokin yaki da ka’idojin aiki na soja yayin aiwatar da harin, yana mai cewa matakin ya zama dole domin kare tsaron kasa da na yankin.

An janye sojojin UAE daga kasar Yemen

Kara karanta wannan

Bam a masallaci: Wanda ake zargi ya fadi makudan kudi da aka ba shi a Borno

Bayan harin, Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da janye dakarunta daga Yemen, tana mai bayyana cewa ta kawo karshen abin da ta kira ayyukan yaki da ta’addanci.

Wannan sanarwa ta zo ne bayan gwamnatin Yemen da duniya ta amince da ita ta bukaci UAE ta fice daga kasar cikin sa’o’i 24.

Saudiyya ta goyi bayan wannan bukata, tana mai cewa zargin UAE da ake na tallafa wa kungiyar STU barazana ne ga tsaron yankin.

Yariman Saudiyya tare da shugaban Amurka
Shugaban Amurka tare da Yariman Saudiyya a 2025. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton the Guardian ya ce kungiyar STC, wadda a baya ke goyon bayan gwamnatin Yemen a yaki da ‘yan Houthi, ta kaddamar da hare-hare kan sojojin gwamnati, tana neman kafa kasa mai cin gashin kanta a Kudancin Yemen.

Fargabar tsaro da martanin masana

Saudiyya ta bayyana damuwa kan abin da ta kira matsin lamba daga UAE ga STC domin kai hare-hare a lardunan Hadramout da Mahara, yankuna masu muhimmanci ga tsaron Saudiyya.

Wani masani kan harkokin Gabas ta Tsakiya, Hesham Alghannam, ya ce matakin Saudiyya ya nuna karara cewa yankunan Gabashin Yemen suna da matukar muhimmanci ga tsaronta.

Trump ya kai hare-hare a Venezuela

Kara karanta wannan

Yahaya Bello zai nemi kwace kujerar Sanata Natasha a zaben 2027

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya tabbatar da kai wasu jerin hare-hare kasar Venezuela da sassafe.

Mazauna babban birnin kasar sun sanar da cewa jiragen yaki sun saki bama-bamai a wasu cibiyoyin soja, inda aka rika jin karar fashe-fashe.

A wani sako da ya fitar bayan kai harin, Donald Trump ya sanar da cafke shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro tare da matar shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng