Trump Ya Jefa Bama Bamai a Venezuela, Ya Cafke Shugaban Kasa Maduro da Matarsa

Trump Ya Jefa Bama Bamai a Venezuela, Ya Cafke Shugaban Kasa Maduro da Matarsa

  • An ji fashe-fashe a wurare da dama a birnin Caracas na Venezuela, inda aka ga hayaki yana tashi sama da wasu muhimman wurare na soja
  • Shaidu sun ce wasu sansanonin soja da filin jiragen sama na soja na cikin wuraren da aka kai wa hari, lamarin da ya haddasa fargaba a unguwanni
  • Halin da ake ciki ya zo ne a lokacin da ake takaddama tsakanin Amurka da Venezuela, wata majiya ta ce Donald Trump ya kama shugaban kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Venezuela – An wayi gari da rahotannin fashe-fashe da tashin hayaki a saman babban birnin Venezuela, Caracas, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da rudani.

Rahotanni daga shaidun gani da ido sun nuna cewa fashe-fashen sun faru kusan lokaci guda a wurare daban-daban na babban birnin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kutsa dajin Sambisa, sun yi kaca kaca da Boko Haram

Shugaban Amurka da na Venezuela
Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro da Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake fama da tsananin takaddama tsakanin Venezuela da Amurka, inda Washington ke kara matsin lamba kan gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro ta fuskar soja da tattalin arziki.

Amurka ta kai hari kasar Venezuela

Rahotanni sun bayyana cewa wasu unguwanni da ke kusa da wuraren da abin ya shafa sun shiga cikin duhu sakamakon katsewar wutar lantarki.

Wasu mazauna sun ce sun ga jiragen sama na shawagi a sararin samaniya, duk da cewa babu cikakken bayani a hukumance.

Wata ‘yar jarida, Vanessa Silva, wadda ke zaune a Caracas, ta ce ta ji wani kara da abubuwan fashewa daga tagar gidanta.

Ta bayyana karar a matsayin mai karfi fiye da tsawa, inda ta ce ta sa gidanta ya girgiza. A cewarta, kasancewar Caracas a kwari ya sa karar ta yadu a ko’ina cikin birnin.

Ta kara da cewa bayan fashewar abubuwa, shiru ya lullube birnin, amma mutane na ci gaba da aika sakonni domin tantance lafiyar juna.

Kara karanta wannan

Gyare gyare da alkawuran da majalisar wakilai ta gaza cikawa a 2025

Kasar Amurka ta cafke shugaban Venezuela

Rahotanni daga abokan hulda na kafafen yada labarai sun ce jami’an gwamnatin Amurka sun san da labarin fashe-fashe da jiragen sama a Caracas da sassafe.

An ce hakan na zuwa ne bayan makonni na matsin lamba daga gwamnatin Shugaba Donald Trump kan Shugaba Maduro na kasar.

A cewar rahoton, Shugaba Trump ya zargi gwamnatin Venezuela da hannu a safarar miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka da ke shafar Amurka.

Rahoton Al-Jazeera ya ce Trump ne ya ba da umarnin kai hare-hare kan wasu wurare a cikin Venezuela, ciki har da cibiyoyin soja kuma sun cafke shugaban kasar da matar shi.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Martanin gwamnatin Venezuela

Gwamnatin Venezuela ta fitar da wata sanarwa inda ta yi watsi da abin da ta kira farmakin soja daga Amurka. A cikin sanarwar, gwamnatin ta ce tana Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin mummunan farmaki kan kasar.

Shugaba Nicolas Maduro ya ayyana dokar ta-baci a kasa, yana mai cewa hare-haren wani yunkuri ne na kwace arzikin man fetur da ma’adinan Venezuela.

Kara karanta wannan

Amurka ta kai hari Venezuela, Trump ya tayar da fargabar barkewar yaƙi

Trump ya kai hari kasar Venezuela

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin kasar Amurka ta tabbatar da kai hari wani waje da ake loda jiragen ruwa a kasar Venezuela.

Hakan na zuwa ne bayan barazanar kai hari ta kasa da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa kasar a kwanakin baya.

A sanarwar da Donald Trump ya fitar bayan harin, Trump ya bayyana cewa sun yi nasara wajen ruguza wasu wurare a kasar Venezuela.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng