Ladanin Masallacin Manzon Allah SAW, Sheikh Faisal Nouman Ya Rasu

Ladanin Masallacin Manzon Allah SAW, Sheikh Faisal Nouman Ya Rasu

  • Saudiyya ta sanar da cewa Sheikh Faisal Nouman da ya shafe kusan rabin rayuwarsa yana ladanci a Masallacin Annabi SAW ya rigami gidan gaskiya
  • Rahotanni sun nuna cewa malamin ya fito ne daga gidan da suka gaji kiran sallah, inda kakansa da mahaifinsa suka taba rike wannan matsayi mai daraja
  • Rasuwarsa ta jawo addu’o’i daga sassa daban-daban na duniya, yayin da jama’a ke tuna irin tawali’u da jajircewarsa wajen yi wa addini hidima

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia – Daya daga cikin mashahuran masu kiran sallah a Masallacin Annabi SAW, Sheikh Faisal Nouman, ya koma ga Mahaliccinsa bayan dogon lokaci yana hidimar addini a masallaci mafi tsarki na biyu a Musulunci.

Sheikh Faisal Nouman ya samu mukamin mai kiran sallah a masallacin Madina a shekarar 1422AH, daidai da 2001, inda ya shiga cikin jerin bayin Allah da aka amince da su wajen kiran sallah Masallacin Manzon Allah SAW.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: An hango jirgin leken asirin Amurka yana shawagi a Najeriya

Ladanin Masallacin Annabi SAW
Ladanin masallacin Madina, marigayi Sheikh Faisal Nouman. Hoto: Inside the Haramain
Source: Facebook

Shafin Saudiyya na Facebook ya sanar da cewa rasuwarsa ta zo ne bayan ya shafe shekaru 25 yana wannan hidima, daga shekarar 1422 zuwa 1447AH.

Tarihin ladanin masallacin Annabi SAW

Sheikh Faisal Nouman ba sabon shiga ba ne a hidimar kiran sallah a Madina, domin ya fito daga gidan da suka gaji wannan aiki na ibada.

Kakansa na daga cikin wadanda suka taba yin kiran salla a Masallacin Annabi SAW, abin da ya kafa tubalin wannan gado a cikin zuriyarsu.

Mahaifinsa ma ya bi wannan tafarki tun yana dan karami, inda aka nada shi ladan yana da shekaru 14 kacal. an ce wannan ya nuna irin jajircewa da kaunar ibada da ta shiga cikin wannan gida tun shekaru masu yawa da suka wuce.

An bayyana cewa mahaifin Sheikh Faisal ya shafe shekaru da dama yana kiran sallah a Masallacin Annabi har sai da ya rasu yana da sama da shekaru 90, bayan ya sadaukar da kusan dukkan rayuwarsa ga wannan aiki.

Kara karanta wannan

Babu su Gwanja da aka saki sunayen mawakan Najeriya da ake gayyata manyan taruka

Sheikh Faisal ya shekara 25 a matsayin ladan

Rahoton Daily Sun ya nuna cewa Sheikh Faisal Nouman ya rike gadon wannan aiki na kiran sallah kamar yadda aka daura masa.

A tsawon shekaru 25 da ya shafe yana ladan, an ce kunnuwan masu ibada daga sassa daban-daban na duniya da ke zuwa Madina domin ziyara da ibada sun saba da muryarsa.

Masallacin Annabi SAW a Madina
Masallacin Manzon Allah SAW da ke Madina. Hoto: Inside the Haramain
Source: Getty Images

An ce a duk tsawon wannan lokaci, Sheikh Faisal ya kasance mai saukin kai, yana nisantar neman daukaka da nuna kai, duk da matsayinsa a wuri mai daraja kamar Masallacin Annabi SAW.

Bayan tabbatar da rasuwarsa, jama’a daga kasashe daban-daban sun fara aikawa da sakonnin addu’a, suna rokon Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sanya aljanna ta zama makomarsa.

Alkalin Najeriya ya rasu a Saudiyya

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Shugaban alkalan Najeriya, mai sharia'a Ibrahim Tanko ya rasu a kasar Saudiyya.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon alkalin ya rasu ne bayan fama da jinya mai tsawo da ya yi a kasa mai tsarki.

Shugabanni, alkalai da gwamnatoci sun yi alhini bisa rasuwarsa, tare da rokon Allah ya gafarta masa kurakuransa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng