An Saka Ranar da Trump zai Hana 'Yan Najeriya Shiga Kasar Amurka
- Gwamnatin Amurka ta sanar da fara wani sabon mataki na takaita ba da biza ga ’yan Najeriya daga farkon shekarar 2026, a wani yunkuri da ta ce na ƙarfafa tsaro
- Matakin ya shafi wasu nau’o’in biza na yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu da musayar ilimi, tare da wasu keɓantattun rukunai da ba za su shiga cikin dokar ba
- Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da rade-radi kan sauye-sauyen manufofin shige da ficen Amurka, lamarin da ya jawo hankalin masu shirin tafiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da takaita ba da biza ga ’yan Najeriya daga 1, Janairu, 2026, bisa wata sanarwar shugaban ƙasa da aka fitar domin ƙarfafa tsaron ƙasa da na iyakoki.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tura tawaga Morocco yayin da Najeriya za ta fafata da Tanzania a AFCON 2025
Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki ne da misalin ƙarfe 12:01 na dare, kamar yadda tanadin sanarwar shugaban ƙasa mai lamba 10998 ya tanada.

Source: UGC
Ofishin jakadancin Amurka ya wallafa a X cewa Najeriya na daga cikin ƙasashe 19 da abin ya shafa, ciki har da wasu ƙasashen Afirka, Caribbean da Latin Amurka.
Mutanen da za a hana zuwa kasar Amurka
Ofishin jakadancin Amurka ya bayyana cewa matakin zai shafi bizar baƙi ta B-1 da B-2, waɗanda ake amfani da su wajen kasuwanci da yawon buɗe ido, da kuma bizar B-1/B-2 haɗe.
Haka kuma, Punch ta wallafa cewa an ce bizar ɗalibai da musayar ilimi ta F, M da J suna cikin waɗanda aka saka a cikin takaitawar da aka yi.
Baya ga hakan, sanarwar ta nuna cewa dokar ta kuma shafi bizar zama ta dindindin, wato bizar ƙaura, sai dai an tanadi wasu keɓantattun yanayi da ba za su shiga cikin wannan takaita ba.
Ofishin jakadancin ya ce manufar ita ce a sake duba hanyoyin tantance masu neman biza kafin ba da damar shiga Amurka.
'Yan Najeriya da za su iya shiga Amurka
Gwamnatin Amurka ta fayyace cewa ba kowa ba ne zai shiga cikin wannan mataki. Daga cikin waɗanda aka ware akwai mutanen da ke da fasfo biyu amma suke neman biza da fasfon ƙasar da ba ta cikin jerin ƙasashen da aka takaita.
Haka kuma, gwamnatin kasar ta ce mazauna Amurka na dindindin ba su cikin waɗanda dokar za ta shafa.

Source: Facebook
Sanarwar ta kuma nuna cewa an ware wasu nau’o’in biza na musamman, ciki har da na ma’aikatan gwamnatin Amurka, da kuma mahalarta wasu manyan gasa na wasanni na duniya.
An kuma jaddada cewa duk wanda yake da biza mai inganci kafin 1, Janairu, 2026, ba za a soke masa ita ba, zai iya shiga Amurka daga Najeriya ko wata kasa.
Amurka ta fasa sura sojoji Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta fasa turo sojoji Najeriya kan tsaro.
'Yan majalisar kasar da suka zo Najeriya sun ce rashin tsaro ya shafi Musulmi da Kirista a yankuna daban-daban.
Sun bayyana cewa Amurka za ta hada kai da Najeriya wajen warware matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
