Trump Ya Kaddamar da Hare Hare a Kasar Syria bayan Kashe Sojojin Amurka

Trump Ya Kaddamar da Hare Hare a Kasar Syria bayan Kashe Sojojin Amurka

  • Sojojin Amurka sun fara kaddamar da babban farmaki a kasar Syria domin lalata sansanonin ISIS da makaman da suke amfani da su
  • Shugaba Donald Trump ya ce martanin yana da tsanani kuma zai ci gaba har sai an murkushe karfin ISIS a yankunan da suke kokarin sake kafuwa
  • Jiragen yaki da makamai masu linzami daga Amurka da wani sansani a Jordan na daga cikin kayan da aka yi amfani da su a farmakin da aka kai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Sojojin Amurka sun sanar da fara wani gagarumin farmaki a kasar Syria, da nufin kawar da mayakan kungiyar ISIS da lalata muhimman cibiyoyinsu.

Matakin ya biyo bayan wani hari da aka kai wa sojojin Amurka da abokan aikinsu a Syria a makon da ya gabata, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyu da kuma wani tafinta.

Kara karanta wannan

Za a fara alkunut, malamai sun yi wa Amurka martani kan Shari'a da Hisbah

Shugaba Donald Trump na Amurka
Jirgin sojojin Amurka da shugaba Donald Trump. Hoto: @CENTCOM|Getty Images
Source: Twitter

White House ta wallafa a X cewa shugaba Donald Trump ya sha alwashin daukar fansa bayan harin, yana mai cewa Amurka ba za ta yi shiru ba kan duk wani hari da ake kai wa dakarunta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Amurka ta kai farmaki kasar Syria

A cewar jami’an tsaro, harin da ya janyo wannan martani ya faru ne a Palmyra, Syria, a ranar 13, Disamba 2025, yayin wani aiki na yaki da ta’addanci.

Shugaba Trump ya a ce Amurka za ta yi “martani mai tsanani sosai” kan ‘yan ta’addan da ke da alhakin kisan sojojinsu.

Bayan kai farmaki Syria, Trump ya jaddada cewa an fara aiwatar da alkawarin da ya dauka bayan harin a yanzu haka kuma an kashe 'yan ISIS da dama.

A cikin sakon, Trump ya ce zai kai farmaki kai tsaye kan manyan sansanonin ISIS a Syria, yana mai bayyana kasar a matsayin wuri da ya jima yana fama da tashin hankali.

Kara karanta wannan

Trump: Sashen kamfanin Tiktok zai koma karkashin kulawar Amurka

Manufar hare-haren Amurka a Syria

Wani babban jami’in Amurka ya bayyana cewa manufar aikin ita ce kai farmaki kan wuraren da ISIS ke kokarin sake tara karfi, tare da lalata sansanoninsu da hanyoyin sadarwarsu a fadin yankuna da dama.

An ce wannan farmaki na daya daga cikin manyan hare-haren da Amurka ta kai a Syria a baya-bayan nan, kuma yana nuna sauyin dabarun yaki da ta’addanci a yankin.

Wasu sojojin kasar Amurka
Wasu dakarun sojojin Amurka a bakin aiki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Makaman da Amurka ta yi amfani da su

Rahotanni sun nuna cewa sojojin Amurka sun yi amfani da jiragen yaki irin su A-10 da F-16, tare da jiragen helikwafta na Apache da kuma makaman HIMARS masu linzami.

Bugu da kari, jiragen yaki F-16 na kasar Jordan sun bayar da tallafi a sararin samaniya, lamarin da ke nuna hadin gwiwa tsakanin Amurka da abokan aikinta a yankin.

NBC ta ce wasu jami’ai sun ce ana sa ran hare-haren za su ci gaba na tsawon makonni ko ma har zuwa wata guda, gwargwadon yadda ake samun bayanan sirri kan motsin ISIS.

Kara karanta wannan

Amurka ta kai hari ta kashe mutane bayan Trump ya sa wa Najeriya takunkumi

Amurka ta hana 'yan Najeriya biza

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta fitar da sababbin dokoki game da harkar shige da fice da ta shafi 'yan Najeriya.

Shugaba Donald Trump ya sanar da hana 'yan Najeriya shiga Amurka saboda cewa akwai matsalar 'yan Boko Haram a kasar.

Hana bizar da Amurka ta yi za ta shafi daliban Najeriya masu zuwa karatu, 'yan kasuwa, masu yawon bude ido da sauransu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng