Benin Ta Dawo Hayyacinta, An Daure Sojoji da Wasu Mutum 30 bisa Yunkurin Juyin Mulki

Benin Ta Dawo Hayyacinta, An Daure Sojoji da Wasu Mutum 30 bisa Yunkurin Juyin Mulki

  • Jamhuriyar Benin ta yanke wa mutane kusan 30 hukunci bayan zarginsu da yunkurin juyin mulki da tarwatsa gwamnati mai-ci a kasar
  • Yawancin wadanda aka kama sojoji ne, kuma ana ci gaba da sa ido a kan Chabi Yayi, ɗan tsohon shugaban kasar Benin kuma jagoran adawa
  • An murkushe yunkurin ne da taimakon Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da sojojin Faransa bayan an samu labarin shirin juyin mulkin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jamhuriyya Benin – Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta yanke wa mutane kusan 30 hukuncin tsare bisa zargin hannu a wani yunkurin juyin mulki da ya ci tura a farkon wannan wata.

Yawancin mutanen da gwamnatin kasar nan ta samu nasarar daurewa sojoji ne da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Benin bayan fatattakar sojoji masu yunkurin juyin mulki

Gwamnatin Benin ta daure sojojin juyin mulki
Pascal Tigri, jagoran yunkurin kifar da gwamnatin Benin. Hoto: @fnicencool
Source: Twitter

France24 ta wallafa cewa an yanke wannan hukunci ne a ranar Talata bayan an samu nasarar dakile yunkurinsu.

Sojoji sun shiga hannu a Benin

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a ranar 7 ga Disamba, 2025 wasu sojoji sun bayyana a gidan talabijin na kasa suna ikirarin cewa sun hambarar da Shugaba Patrice Talon daga mulki.

Sai dai cikin kankanin lokaci, dakarun da ke biyayya ga gwamnati suka murkushe yunkurin, tare da samun taimako daga Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da kuma sojojin musamman na Faransa.

A yayin murkushe yunkurin, an kashe mutane da dama, yayin da ake zargin jagoran yunkurin, Laftanar Kanal Pascal Tigri, ya tsere tare da wasu sojojin da suka bijire wa umarni.

Har yanzu hukumomi na ci gaba da neman sauran mutanen da ake zargi suna da hannu a cikin yunkurin kifar da gwamanatin.

An yi shari'a da sojojin tawayen Benin

Wadanda ake zargin sun gurfana gaban wani musamman mai gabatar da kara a gaban kotun laifuffukan tattalin arziki da ta’addanci da ke birnin Cotonou a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Abin da ministan tsaro ya ce ga sojoji bayan yunkurin juyin mulki a Benin

A washegari ne aka yanke shawarar tsare su kafin fara shari’a. Ana zarginsu da manyan laifuffuka da suka hada da cin amanar kasa, kisan kai, da kuma barazana ga tsaron kasa.

An girke jami’an tsaro masu yawa a kewaye da kotun yayin zaman shari’ar, domin kauce wa duk wani rikici ko yunkurin ceto wadanda ake tsare da su.

Gwamnatin Benin ta kai sojoji kotu
Harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: @FederalHigh
Source: UGC

A wani bangare na binciken, Chabi Yayi, ɗan tsohon shugaban kasar Benin kuma jagoran adawa, Thomas Boni Yayi, ya sha tambayoyi daga hukumomi dangane da yunkurin juyin mulkin.

Daga bisani an sake shi, amma har yanzu yana karkashin bincike na yiwuwar ko yana da hannu a yunkurin hambarar da gwamnati.

Shugaba Patrice Talon, wanda ake yaba wa kokarinsa na habaka tattalin arzikin kasar, na fuskantar suka daga wasu bangarori kan zargin nuna mulkin kama-karya.

Hankalin mutane ya kwanta a kasar Benin

A baya, mun wallafa cewa bayan yunƙurin juyin mulki da ya girgiza Jamhuriyar Benin a farkon watan nan, alamu na nuna cewa hankula sun soma dawowa a birnin Kotono, cibiyar tattalin arziƙin ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa duk da tsoron da ya addabi jama’a a kwanakin farko bayan yunkurin juyin mulkin, rayuwar yau da kullum na dawowa yadda aka saba sannu a hankali.

Kara karanta wannan

'Za a kamo shi,' Benin ta gano kasar da sojan da ya so juyin mulki ya buya

Mutane da dama sun hallara a wajen wata mai sayar da jarida, Chantal Dagah, domin samun ƙarin bayani kan abin da ya faru, wanda ke nuna yadda jama'a ke neman karin bayani game da lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng