Trump Ya Fadi Shugaban Kasar da zai Iya Farmaka a Gaba bayan kai Hari Venezuela
- Shugaban Amurka Donald Trump ya yi sabuwar barazana ga shugaban Colombia, Gustavo Petro, kan batun yaƙi da kwaya
- Ya ce Colombia na samar da kwaya tana tura ta Amurka, yana mai cewa idan Petro bai hankalta ba, zai yi maganinsa
- Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta ƙara dagulewa tun bayan dawowar Trump mulki karo na biyu a watan Janairun 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake fitowa fili da kakkausar magana dangane da dangantakarsa da shugaban Colombia, Gustavo Petro.
Wannan furuci ya biyo bayan tambayar da wani ɗan jarida ya yi masa a wani zama da aka yi a fadar White House tare da 'yan kasuwa, inda aka nemi sanin ko ya tattauna da Petro a baya-bayan nan.

Source: Getty Images
A martanin da ya yi, Al-Jazeera ta rahoto cewa Trump ya ce idan Petro bai gyara halinsa ba za su saka kafar wando daya da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Trump ya gargadi shugaban Colombia
Maganganun Trump sun sake tayar da kura game da makomar alaƙar Amurka da Colombia, ƙasar da ta dade tana karɓar tallafin Amurka a yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi tsawon shekaru.
A martaninsa, USA Today ta rahoto Trump ya fara da cewa shugaban Colombia:
“Ba shi kyakkyawar mu’amala da Amurka,”
Trump ya kara da cewa Colombia na samar da kwaya a masana’antunta sannan tana tura ta cikin Amurka, yana mai cewa:
“Ya kamata ya hankalta, in ba haka ba shi ma zai biyo baya. Ina fata yana ji na. Za mu ɗauki mataki saboda ba ma son mutanen da suke kashe jama'a.”
Furucin na Trump ya zo ne jim kaɗan bayan wani samamen sojin Amurka da ya ƙwace tankar man fetur a Tekun Caribbean saboda abin da suka kira karya takunkumi da Venezuela da Iran suka yi.
Tarihin rikici tsakanin Trump da Petro
Tun daɗewa dangantaka ba ta daɗi tsakanin Trump da Petro, wanda shi ne shugaba na farko mai akida daban da ta siyasar Trump a tarihin Colombia na baya-bayan nan.
Ko bayan dawowar Trump mulki a watan Janairun 2025, dangantakar ta ƙara dagulewa, duk da cewa Colombia kasa ce da ta dade tana samun tallafin Amurka game da yaki da miyagun kwayoyi.

Source: Getty Images
Trump da magoya bayansa suna zargin Petro da rashin ɗaukar tsattsauran mataki kan dakile samar da kwaya a Colombia.
A wani taron majalissar ministoci da ya gudana a ranar 2, Disamban 2025, Trump ya yi karin haske kan yiwuwar aika soja Colombia, yana mai nuna cewa Amurka ba za ta ci gaba da zuba ido ba.
Dan majalisar Amurka ya yabi Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar Amurka Riley Moore ya gana da mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro a Abuja.
Hakan na zuwa ne bayan tawagar Amurka ta dura Najeriya domin tattara bayanai game da zargin kisan Kiristoci da ake magana a kai.
Dan majalisar ya yaba wa shugaban kasa Bola Tinubu game da matakan da ya ke dauka kan tsaro bayan ceto daliban da aka sace a Neja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


