'Za a Kamo Shi,' Benin Ta Gano Kasar da Sojan da Ya So Juyin Mulki Ya Buya
- Wani jami’in gwamnati ya ce shugaban yunkurin juyin mulkin Benin ya gudu zuwa Togo bayan barin wuta da dakarun Najeriya suka yi
- Gwamnatin Benin na shirin neman a mika mata sojan, yayin da ECOWAS ta tura sojoji domin tabbatar da tsaro a mahimman wurare
- Rahotanni sun ce dakarun Faransa sun bada gudunmuwa bayan rundunar Benin ta yi fafutukar korar sojojin da ke son kifar da gwamnati
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Benin – Wani babban jami’in gwamnatin Benin ya bayyana cewa Laftanar Kanar Pascal Tigri, wanda ya jagoranci yunkurin juyin mulki ra a ranar Lahadi ya buya a kasar Togo.
Yunkurin karɓe mulkin ya zo ne a lokacin da yammacin Afirka ke fama da juyin mulki cikin shekaru biyun da suka gabata, lamarin da ya tayar da hankula game da makomar dimokradiyya a yankin.

Source: Twitter
Jami’in kasar Benin ya shaida wa BBC cewa gwamnati za ta nemi a mika mata Laftanar Kanar Pascal Tigri nan gaba kadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar jami’an gwamnati, Najeriya ta tura jiragen yaki domin korar ‘yan tawaye daga sansanin soja da gidan talabijin bayan gwamnatin Patrice Talon ta nemi taimako.
A safiyar Lahadi ne wasu sojoji suka bayyana a talabijin suna ikirarin karɓe iko, yayin da ake jin harbe-harbe a kusa da fadar shugaban kasa.
Jagoran juyin mulkin Benin ya tsere Togo
Jami’in gwamnatin Benin ya ce sun san inda Tigri yake a Lomé, babban birnin Togo, a yankin da shugaban kasar Togo, Faure Gnassingbé, yake zaune.
Ya kara da cewa za su nemi a mika shi zuwa kasarsa ta hanyar hukuma, duk da cewa ba a samu tabbaci daga Togo ba tukuna.
Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan, amma ECOWAS, wanda Togo ke cikinta, ta yi tir da yunkurin juyin mulkin.
Yarjejeniyar kasashen yankin ta ce ko da yaushe za a kare dimokradiyya daga wadanda ke so su kifar da gwamnati ta hanyar karfin iko.
A yanzu haka ECOWAS ta riga ta tura dakarunta daga Najeriya, Ghana, Saliyo da Ivory Coast domin tabbatar da tsaro a muhimman wurare na kasa, alamar cewa ba za ta sake bari a kifar da gwamnati ba.
Me ya haddasa yunkurin juyin mulkin?
‘Yan tawayen sun bayyana cewa sun yi yunkurin ne saboda yadda gwamnati ke tafiyar da tsaro a Arewacin Benin, inda sojoji suka dade suna fuskantar hare-haren ‘yan ta'adda daga yankunan Nijar da Burkina Faso.

Source: Twitter
Haka kuma sun koka da tsarin kula da iyalan sojojin da suka mutu, karin haraji, da yanke tallafin jinya kamar jinyar cutar koda da gwamnati ta daina daukar nauyinta.
Juyin mulki: Faransa ta taimaki kasar Benin
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Faransa ta tabbatar da cewa ta taimakawa kasar Benin yayin fama da matsalar masu son juyin mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa wani hadimin shugaba Emmanuel Macron ne ya bayyana haka bayan hana juyin mulki a kasar.
Sai dai duk da tabbatar da kai agaji kasar, gwamnatin Faransa bata yi bayani dalla-dalla game da gudumawar da ta bayar ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


