Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Halin da Ake Ciki bayan Yunkurin Juyin Mulki a Benin

Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Halin da Ake Ciki bayan Yunkurin Juyin Mulki a Benin

  • Hankula sun tashi a kasar Benin bayan da wasu sojoji suka yi ikirarin hambarar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon
  • Sai dai, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa masu yunkurin juyin mulkin ba su karbe iko ba a kasar da ke yankin Afrika ta Yamma
  • Kasar Benin dai na da tarihin juyin mulki da yunkurin juyin mulki tun shekaru da dama da suka gabata

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Benin - Sojoji a kasar Benin a ranar Lahadi sun sanar da cewa sun hambarar da Shugaba Patrice Talon.

Sai dai, masu tsaron lafiyarsa sun ce yana cikin koshin lafiya, kuma rundunar sojojin kasar na sake samun cikakken iko.

Sojoji sun yi yunkurin karbe iko a Benin
Shugaban kasar Benin, Patrice Talon Hoto: Patrice Talon
Source: Twitter

Tashar France24 ta ce wata majiya kusa da Shugaba Patrice Talon ta shaida wa AFP cewa shugaban yana cikin tsaro.

Kara karanta wannan

IBB ya gano matsalar Arewa, ya fadi dalilin rashin tsaro, talauci a yankin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da safiyar Lahadi, wasu sojoji da suka kira kansu “kwamitin sojoji na sake gina kasa” (CMR) sun bayyana a gidan talabijin na gwamnati cewa sun yanke shawarar “Patrice Talon ya daina zama shugaban kasa daga yau.”

Wane hali ake ciki a Benin?

Majiyar ta ce sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin ba su da yawa sosai, kuma gidan talabijin na kasa kawai suka karbe.

"Wannan wani karamin rukunin mutane kawai da ke da iko da gidan talabijin. Rundunar sojoji ta kasa na dawo da iko. Birnin Cotonou da kasar baki ɗaya suna cikin tsaro.”
“Kawai lokaci ne kaɗan kafin komai ya koma daidai. Ana ci gaba da kawar da barazanar.”

- Wata majiya

Wani jami’in soja ya tabbatar da cewa ana kula da lamarin, kuma masu yunkurin juyin mulkin ba su karbe fadar shugaban kasa ko ofishinsa ba.

Ofishin jakadancin Faransa ya bayyana a shafin X cewa “an ji harbe-harbe a Camp Guezo” kusa da fadar shugaban kasa, kuma ta ja hankalin ’yan kasar Faransa da su zauna a cikin gidajensu domin tsaro.

Kara karanta wannan

Ya matso kusa da Najeriya: Sojoji sun sake juyin mulki a Afrika ta Yamma

An sha yin juyin mulki a Benin

Tashar RFI ta ce tarihin siyasar Benin cike yake da juyin mulki da yunkurin juyin mulki tun shekaru da dama.

Patrice Talon, ɗan kasuwa mai shekaru 67 da ake kira “Sarkin audugar Cotonou”, yana shirin mika mulki a watan Afrilu na badi bayan kammala shekaru 10 a kan mulki.

A lokacin mulkinsa ya kawo ci gaban tattalin arziƙi amma ya kuma zo da karuwar hare-haren 'yan jihadi.

Shugaba Talon na shirin sauka daga mulki

Patrice Talon, wanda ya hau mulki a 2016, yana karshen wa’adinsa na biyu wanda zai kare a 2026, wanda shi ne mafi tsawo da kundin tsarin mulki ya tanada.

Fadar shugaban kasa ta musanta juyin mulkina Benin
Shugaba Patrice Talon da sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a Benin Hoto: @PatriceTalonPR
Source: Twitter

Babban jam’iyyar adawa ba ta shiga jerin masu neman maye gurbinsa ba, wanda hakan ya sa jam’iyya mai mulki za ta yi takara ne da 'yan adawa “masu matsakaicin ra’ayi”.

Patrice Talon ya samu yabo wajen bunƙasa tattalin arziƙin Benin, amma masu suka na zarginsa da mulkin kama-karya da takura ’yan adawa.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi Ahmad ya ce ya daina shiga daji tattaunawa da 'yan bindiga

Yammacin Afirka ta fuskanci juyin mulki da dama a 'yan shekarun nan, musamman a kasashen makwabta na Arewacin Benin watau Nijar da Burkina Faso. Hakazalika an yi Mali, Guinea da Guinea-Bissau.

Sojojin Nijar sun yanke alaka da Benin

A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun sanar da yanke alakar sojoji da kasar Benin.

Sojojin na Nijar sun sanar da haka ne a talabijin na kasar kan yanke alaka da kasar Benin wadda ke makwabtaka da ita.

Hakazalika, a cikin sanarwar da suka fitar, sojojin sun ce duk wata yarjejeniya ta kare a tsakaninsu da kasar Benin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng