Dubu Ta Cika: An Rike 'Dan Najeriya da Ya Rikita Amurka da Damfara
- Kotun Amurka ta yanke wa Oluwaseun Adekoya hukuncin shekara 20 a kurkuku bayan an kama shi da laifin damfara
- Hukuncin ya biyo bayan binciken FBI da ya gano ya yi amfani da sunaye daban-daban wajen karkatar da kuɗin HELOC
- Hukumar ta kwace agogon Rolex, zoben Tiffany na $51,000 da wasu kayayyaki da ake zargin ya samo ta hanyar damfara
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Kotun Amurka a yankinNew York ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai suna Oluwaseun Adekoya hukuncin shekara 20 a gidan yari saboda jagorantar wata babbar damfara ta banki da kuma satar bayanan sirrin mutane.
Adekoya, mai shekaru 40, wanda yake zaune a New Jersey, ya fuskanci shari’a ne kan zargin karkatar da kuɗin HELOC da kuma amfani da bayanan jama’a ba bisa ka’ida ba.

Source: Twitter
Ma'aikatar shari'ar Amurka ta wallafa cewa an yanke masa hukuncin ne a ranar 1 ga Disamba bayan zaman shari’ar da ta ɗauki mako uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa Adekoya ya samu zama a Amurka tun 2004, amma jami’an gwamnati suka ce ya yi amfani da wannan damar ne wajen cutar da al’ummar kasar.
Lauyan gwamnati, John Sarcone, ya bayyana Adekoya a matsayin mai laifi wanda ya yi amfani da damar zama dindindin wajen damfara.
Yadda aka fara binciken damfarar da ya yi
A cewar ofishin lauyan gwamnati, binciken kan Adekoya ya fara ne a watan Mayun 2022, lokacin da Broadview Federal Credit Union da ke Albany ta gano wasu mu’amaloli na dabam a rassanta.
Bayan gudanar da bincike, FBI ta gano cewa Adekoya ne jagoran wannan aiki wanda ya shafi jihohi da dama a fadin Amurka, tare da gano wasu mutum 13 da suka taimaka masa.
The Cable ta rahoto cewa an gurfanar da waɗannan mutane ne ta hanyar shigar da wata tuhuma, kuma dukansu sun amsa laifi kafin a fara shari’a.

Source: Getty Images
Hukumomi sun ce dukkan ayyukan sa sun tsaya cak ne bayan kama shi a ranar 12 ga Disamba 2023, lokacin da aka fara aiwatar da bincike a gidansa.
Yadda aka kama dan Najeriyan a Amurka
Shaida a kotu ta nuna cewa lokacin da FBI ta zo shiga gidansa domin gudanar da bincike, Adekoya ya goge bayanan babbar wayar da yake amfani da ita wajen tsara damfarar.
Wasu rahotanni sun ce duk da haka, FBI ta samu wasu wayoyi na wucin gadi da ya yi amfani da su wajen aikata laifuffukan.
Haka kuma hukumar ta kama wasu kayayyaki da ake zargi ya mallaka ta hanyar damfara, ciki har da agogon Rolex, zoben Tiffany mai darajar $51,000 (₦73,983,300), jakunkuna da takalma, da kusan $26,000 a asusun bankinsa.
A cewar bayanan gwamnati, an kwace wadannan kayayyaki gaba ɗaya kuma za a maido shi Najeriya bayan gama zaman kurkuku.
Wakilan Amurka sun gana da hadimar Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa wasu jami'an gwamnatin Amurka da ke aiki a Najeriya sun gana da wata hadimar Bola Tinubu.
Legit Hausa ta rahoto cewa sun gana ne a birnin tarayya Abuja, kuma sun tattauna batutuwan tsaron Najeriya.
Biyo bayan zaman da suka yi, jami'an Amurka sun ce sun kara fahimtar yanayin tsaron Najeriya tare da cewa za su ba kasar hadin kai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


