Sanata Barau Ya Kausasa Harshe kan Harin 'Yan Bindiga a Kano

Sanata Barau Ya Kausasa Harshe kan Harin 'Yan Bindiga a Kano

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya nuna damuwarsa kan sabon harin da 'yan bindiga suka kai a jihar Kano
  • Sanata Barau ya bayyana cewa ba za su tsaya su zura idanu su bari wasu tsageru na tsallakowa daga jihohi makwabta suna addabar mutanen Kano ba
  • ​Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bukaci hukumomin tsaro da su yi duk mai yiwuwa domin hana kutsen da 'yan bindigan suke yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi magana kan hare-haren 'yan bindiga a Kano.

Sanata I. Barau Jibrin ya yi kira ga hukumomin tsaro da su bi sahun ’yan bindiga masu addabar wasu kauyuka a kananan hukumomin Tsanyawa da Shanono na jihar Kano.

Sanata Barau ya koka kan harin 'yan bindiga a Kano
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin Hoto: @barauijibrin
Source: Facebook

Sanata Barau ya yi magana kan harin 'yan bindiga

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Kano, sun yi kisa da sace mutane

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban majalisar dattawan ya sanya a shafinsa na X a ranar Lahadi, 30 ga watan Nuwamban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake mayar da martani kan harin da ’yan bindiga suka kai Yankamaye a Tsanyawa ranar Asabar da daddare, Sanata Barau ya roki hukumomin tsaro da su kara zage damtse tare da kai farmaki ga miyagun da suka fito daga jihohi makwabta.

Sanata Barau ya yi ga jami'an tsaro

Sanata Barau ya ce dole ne a dakatar da kutse da shigowar ’yan ta’adda cikin yankunan biyu.

“Na samu labarin tayar da hankali game da kashe wata mata da kuma sace mutane uku a kauyen Yankamaye da ke Tsanyawa ta jihar Kano da ’yan bindiga daga jihohi makwabta suka yi da daren Asabar lokacin da mutane suka kwanta barci."
“Wannan lamari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan makamancin irin wannan hari a kauyen Biresawa, shima a Tsanyawa."
"Don haka ina kira ga hukumomin tsaro waɗanda sau da dama suka yi artabu da wadannan miyagun a yankin, da su kara kaimi wajen ceto waɗannan mutanen sannan su murƙushe ’yan ta’addan. Su kai farmaki gare su.”

Kara karanta wannan

Martanin Barau da gwamnatin Kano ta nemi a cafke shi saboda zargin ingiza rashin tsaro

Sanata Barau ya nuna damuwa kan harin 'yan bindiga a Kano
Sanata Barau Jibrin na jawabi a wajen taro Hoto: @barauijibrin
Source: Twitter
“Ba za mu yarda waɗannan miyagun da ke gudowa daga jihohi makwabta sakamakon samamen sojoji su zo su tada mana hankali ba."
"Dole ne a tsayar da wannan kutse da shigowa yankin. Tsaron rayuka da dukiyoyin mutanenmu shi ne babban abin da muke so mu tabbatar. Ba za mu yi wasa ba wajen ganin an cimma hakan.”

- Sanata Barau Jibrin

Sanata Barau ya yi wa Gwamna Abba martani

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi wa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, martani kan matsalar rashin tsaro.

Sanata Barau I. Jibrin, ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya daina siyasantar da batun tsaro da ke damun jihar.

Hakazalika mataimakin shugaban majalisar dattawan ya karyata zargin gwamnatin jihar Kano, yana mai cewa kamata ya yi ta nuna bidiyon da ta ke cewa ya yi kalaman da za su iya ta’azzara rashin tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng