Amurka Ta Fitar da Bayanai kan Dan Bindigan da Ya Harbi Sojojin Kasar

Amurka Ta Fitar da Bayanai kan Dan Bindigan da Ya Harbi Sojojin Kasar

  • Rahotanni sun ce ana zargin wani dan Afghanistan ne mutumin da ya harbi sojojin Amurka da ake aiki a White House
  • Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Amurka ta tabbatar cewa an shigo da shi ne ta wani shirin Joe Biden a Satumban 2021
  • Harin ya sake tada ce-ce-ku-ce kan tsaro da yadda aka karɓi dubban ‘yan Afghanistan ba tare da cikakken tantancewa ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Rikici ya barke a babban birnin Amurka bayan wani mutum daga Afghanistan, Rahmanullah Lakamal, ya bude wuta ya harbi sojoji biyu a kusa da fadar White House.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Amurka ta ce an shigo da Lakamal ne cikin dubban ‘yan Afghanistan da aka karɓa a lokacin gwamnatin Joe Biden.

Kara karanta wannan

Trump ya yi magana a fusace bayan 'dan bindiga ya harbi sojojin Amurka

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka yayin wani taro a kwanakin baya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ma'aikatar ta wallafa cewa an aiwatar da shirin ne bayan ficewar sojojin Amurka daga Afghanistan, ya karɓi sama da mutane 70,000 cikin gaggawa a 2021.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan sabon harin ya sake kunna muhawarar da ake yi a Amurka game da tsaro da kuma shirin karɓar baki cikin gaggawa.

Yadda aka harbi sojojin Amurka 2

Rahotanni sun nuna cewa sojojin suna bakin aikinsu ne a kusa da hanyoyin gwamnati lokacin da Lakamal ya bude musu wuta a yammacin Laraba.

Rahoton CNN ya nuna cewa jami'an FBI sun tabbatar da cewa sojojin suna cikin mawuyacin hali a asibiti.

Harin ya faru ne a daidai lokacin da ake ta muhawara kan yadda ake tura sojoji biranen Amurka saboda karuwar laifuffuka.

An ce lamarin ya kara tayar da kura a siyasa, musamman tsakanin tsohuwar gwamnatin Biden da masu adawa da ita.

Tsohon shugaban Amurka, Joe Biden
Tsohon shugaban Amurka, Joe Biden na wani jawabi. Hoto: The White House
Source: Getty Images

Wani jami’in tsaro ya shaida cewa an harbi wanda ake zargin yayin kama shi, kuma yana da raunuka amma ba masu tsanani ba. Yanzu haka ana ci gaba da tsare shi domin bincike.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An harbi sojoji a kusa da fadar shugaban Amurka, White House

Tarihin shigowar mutumin kasar Amurka

Hukumomin tsaro sun bayyana cewa wanda ake zargi shi ne Rahmanullah Lakanwal mai shekaru 29, wanda ya zauna a jihar Washington kafin kai harin.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Amurka ta yi karin haske a kan mutumin da ake zargin tana mai cewa:

“Mutumin da ya harbi sojojin ba’amurke ne daga Afghanistan, kuma yana cikin wadanda aka karɓo cikin gaggawa ta shirin Operation Allies Welcome.”

Wani rahoto ya kara da cewa Lakamal ya shiga Amurka ne a 2021 lokacin da ake kokarin ceto mutanen da ke cikin hadari bayan faduwar gwamnatin Afghanistan.

An ce yawancin mutanen da aka karɓa sun yi aiki tare da sojojin Amurka a matsayin masu fassara ko masu wayar da kai.

Sai dai shirin ya gamu da suka daga jam’iyyar Republican da masu lura da harkokin gwamnati, wadanda suka ce an yi gaggawa ba tare da bin matakan tsaro yadda ya kamata ba.

Kara karanta wannan

Cikin rashin imani, Boko Haram sun guntule kan mata saboda zargin tsafi

Kiristan Najeriya ya yi wa Amurka martani

A wani labarin, mun kawo muku cewa wani Kirista dan Najeriya ya yi Allah wadai da kalaman shugaban Amurka, Donald Trump.

'Dan Najeriyan mai suna JJ Omojuwa ya yi magana ne a kasar Canada yayin tattaunawa da wani Sanatan Amurka.

Ya ce bai kamata shugaban Amurka ya yi maganganu marasa dadi game da Najeriya ba yayin karin haske kan rashin tsaron kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng