Zargin Kisan Kiristoci: Ɗan Majalisar Amurka Ya Fashe da Kuka yayin Zama game da Najeriya

Zargin Kisan Kiristoci: Ɗan Majalisar Amurka Ya Fashe da Kuka yayin Zama game da Najeriya

  • 'Dan majalisar Amurka Bill Huizenga ya nuna takaici kan yayin zaman jin ra’ayi kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
  • Ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da gazawa wajen kare mabiya addinai daga hare-haren masu tsattsauran ra’ayi
  • Akwai yiwuwar a ƙaƙabawa wasu daga cikin jami’an Najeriya takunkumi idan Majalisar Dattawan Amurka ta amince

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – Dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican a Amurka, Bill Huizenga, ya kasa boye takaici kan cewa ana kashe kiristoci a Najeriya.

Ya nuna fushi da 'tausayi' a zaman ranar Alhamis yayin da kwamitin harkokin ketare na Majalisar Wakilai da ya mayar da hankali kan Najeriya.

Bill Huizenga ya yi takaicin zargin cewa ana kashe kiristoci a Najeriya
'Dan majalisar Amurka, Bill Huizenga Hoto: Bill Huizenga
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Ɗan majalisar ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan abin da ya kira hare-haren da masu tsattsauran ra'ayin Musulunci ke kai wa Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Kai makaryaci ne': Yar siyasar Canada ta zagi ministan Tinubu, ya yi martani mai zafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan Majalisar Amurka ya soki Tinubu

Channels TV ta wallafa cewa an yi wa taken “Sake sanya Najeriya a jerin kasashen da ake kallon suna cin zarafin addini (CPC): Gargadi mai muhimmanci daga Shugaba Trump.”

Wannan na zuwa ne bayan matakin da Donald Trump ya dauka na dawo da Najeriya cikin jerin kasashen CPC kan zargin an ware kiristoci ana kashe wa.

Huizenga ya ce ya taso yana mu’amala da 'yan Najeriya, kuma ya shafe shekaru yana bibiyar matsalolin tsaron kasar.

Majalisar Amurka ta zauna kan batun Najeriya
Shugaban Amurka Donald Trump, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Donald J Trump/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Getty Images

Ya zargi ‘yan majalisar Amurka da kuma kafafen yada labarai da rage darajar tashin tashinar da ake dangantawa da addini a Najeriya.

Ya ce:

“Na yi makaranta tare da yara ’yan Najeriya, muna da makwabta da wanda suka taba yin aikin da'awar yaɗa addinin kirista a can, wadanda ke da iyalai da abokai a Najeriya, wadanda suka san abin da ke faruwa.”

Kara karanta wannan

Trump: Gwamnati ta 'dora alhakin karuwar ta'addanci a Najeriya a kan shugaban Amurka

Sai ya kara da cewa:

“Ba wai manema labarai ba kadai, har ma da wasu ’yan majalisar nan suna musanta abin da ke faruwa, ko kuma rage muhimmancinsa.”

Amurka na iya sawa Najeriya takunkumi

Huizenga ya bayyana cewa Kiristoci, Musulmai masu sassaucin ra’ayi da duk wanda masu tsattsauran ra’ayin Musulunci ke razanawa a Najeriya na bukatar tsaro.

Ya ce gwamnatin Najeriya ba ta yin abin da ya dace wajen hana hare-haren da damar matakan kare rayukan jama'ar ƙasa.

Ɗan Majalisar ya kuma kalubalanci yadda Amurka ke kula da tallafin jin kai ga mutanen da suka rasa muhallansu musamman a jihohin Binuwai da Taraba.

A Kalamansa, ya ce a Binuwai kadai akwai mutane miliyan 1.4 da ke zaman gudun hijira saboda tashe-tashen hankula.

Ya ambaci takarda daga shugaban kwamitin harkokin kudi na Majalisar Wakilai, French Hill, wacce ta jaddada bukatar takunkumi da za a iya aiwatarwa.

Za a dauki matakin ne idan Majalisar Dattawan Amurka ta tabbatar da sake sanya Najeriya a jerin CPC.

Kara karanta wannan

Ran APC ya baci, ta dura kan PDP bayan saboda taimakon Trump a Najeriya

Hakan na iya jawo kakaba takunkumi kan jami’an Najeriya da ake zargin suna da hannu a take hakkin bil’adama, lamarin da ka iya shafar hulda, kasuwanci da tallafi tsakanin Amurka da Najeriya.

Muhara kan Najeriya ya raba ƴan majalisa

A wani labarin, kun ji cewa an gudanar da zaman sauraron korafi kan matakin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauka a kan zargin kisan kiristoci a Najeriya.

Chris Smith, shugaban zaman, ya ce 89% na Kiristocin da ake kashewa a duniya suna Najeriya, tare da nuni da cewa tun daga 2009 an kashe Kiristoci sama da 52,000.

Johnny Olszewski ya yi nuni cewa ba duk hare-haren ne na addini ba ne — kuma Musulmai da Kiristoci na fuskantar haɗari saboda Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng