Venuzuela Ta Fara Shirin Gwabza Yaki da Sojojin Amurka, Ta Tara Makaman Rasha
- Venezuela ta fara baza makamai da dabarun yaki domin kare kanta idan Amurka ta kai mata hari ta sama ko ta ƙasa
- Gwamnatin kasar na fuskantar ƙarancin kayan aiki da ma’aikata, abin da ya sa ake neman dabarun tun da wuri
- Bayan dabarar guerilla, akwai wata dabara da za su yi da nufin haifar da hargitsi yayin da za su gwabza fada da Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Venezuela - Rahotanni daga majiyoyi sun nuna cewa rundunar tsaron Venezuela na shiri tare da ɗaukar tsofaffin makaman Rasha da sauran kayan yaki.
Ta fara shirin ne domin neman kare ƙasa ta hanyar dabarun yaki na guerilla idan Amurka ta kai wa ƙasar hari.

Source: Getty Images
Rahoton Reuters ya ce wannan mataki na zuwa ne yayin da kasar ke fuskantar ƙarancin kayan aiki da ma’aikata.
Barazanar Trump ga kasar Venezuela
Donald Trump ya nuna yiwuwar kai hare-haren ƙasa a Venezuela bayan wasu hare-hare da Amurka ta kai kan jiragen ruwa a yankin Caribbean.
Baya ga kai hari ta sama, wasu rahotanni sun nuna cewa ana ganin karin tarin sojojin Amurka a yankin.
Sai dai daga baya shugaba Donald Trump ya musanta cewa yana tunanin kai farmaki a cikin ƙasar Venezuela.
Shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, wanda ya hau mulki tun 2013, ya ce Trump na ƙoƙarin kifar da gwamnatinsa, kuma ya jaddada cewa sojojin ƙasar da jama’a za su tsayawa kare ƙasarsu.
Dabarun yaki da Venezuela ta dauka
Rahotanni sun bayyana cewa ƙarancin horo, ƙarancin albashi da lalacewar kayan yaki sun raunana rundunar sojojin Venezuela.
An ce wasu manyan hafsoshin rundunoni ma sun kai ga tattaunawa da manoman yankuna domin su samu abincin ciyar da sojojinsu, saboda kayan tallafin gwamnati ba su wadatuwa.

Kara karanta wannan
Kotu ta bada belin tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, ya fito bayan mako 3 a kurkuku
Wannan yanayi ne ya sa gwamnati ke jingina da dabaru guda biyu; dabarar guerilla da kuma wata dabara da ba a ambata a bainar jama’a ba sosai.

Source: Getty Images
A cewar rahoton Tell Magazine, dabarar guerilla za ta rarraba ƙananan rundunoni a sama da wurare 280, domin aiwatar da farmaki idan aka kai hari daga waje.
Dabara ta biyu, mai suna “anarchization,” za ta haɗa jami’an leƙen asirin ƙasa da magoya bayan jam’iyyar gwamnati da ke ɗauke da makamai, domin haifar tashin hankali a titunan birnin Caracas.
A cewar majiyoyi biyu, manufar ita ce a hana wa duk wata ƙasa daga waje damar shimfiɗa iko ko gudanar da aiki cikin sauƙi.
Wannan shirin na lafiya da abin da jami’an gwamnati suka taɓa ambata a gidajen talabijin, inda suka yi ishara da cewa Venezuela na da tsarin tsawon juriya idan wata ƙasa ta kai mata hari.
Martanin gwamnatin kasar Venezuela
Ma’aikatar sadarwa ta Venezuela, wacce ke kula da tambayoyi na manema labarai, ba ta mayar da martani kan tambayoyin da aka mata ba.

Kara karanta wannan
Hanyoyin da Tinubu da Nuhu Ribadu suka bullo wa barazanar harin Amurka sun fara jan hankali
Amma jami’an gwamnati sun sha bayani cewa barazanar Amurka “ba ta da tushe,” tare da jaddada cewa Venezuela na son zaman lafiya.
Faston Najeriya ya yi kira ga Trump
A wani labarin, kun ji cewa shugaban PFN, Bishop Wale Oke ya yi magana kan farmakin da Donald Trump ya ce zai kawo Najeriya.
Faston ya ce bai yarda da maganar kawo hari Najeriya ba, sai dai ya bukaci Trump ya tattauna da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wale Oke ya yi martani ne yayin da Amurka ta yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ba tare da gabatar da gamsassun hujjoji ba.
Asali: Legit.ng
