Jirgin Sama Dauke da Sojoji Ya Yi Mummunan Hatsari, Dakaru 20 Sun Mutu a Georgia

Jirgin Sama Dauke da Sojoji Ya Yi Mummunan Hatsari, Dakaru 20 Sun Mutu a Georgia

  • Sojojin Turkiyya 20 sun rasu bayan jirgin C-130 da ke dauke da su ya yi hatsari a kasar Georgia, daga Azerbaijan zuwa Turkiyya
  • Hatsarin ya zama mafi muni da rundunar sojin Turkiyya ta fuskanta tun a 2020, lokacin da sojojin Rasha suka kashe sojojin kasar
  • Gwamnatocin Turkiyya, Georgia da Azerbaijan sun fara bincike tare da kamfanin Lockheed Martin, wanda ya kera jirgin.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Turkiyya - Gwamnatin Turkiyya ta tabbatar da mutuwar sojoji 20 bayan wani jirgin sojin C-130 Hercules ya yi hatsari a kasar Georgia a ranar Talata, 11 ga Nuwamba, 2025.

Jirgin, wanda ya taso daga Azerbaijan zuwa Turkiyya, ya kife kusa da iyakar Georgia, inda ya bar tarkacen karafa a cikin wani fili da mai yawan ciyawa.

Jirin saman sojojin Turkiyya ya yi hatsari a Georgia
Hoton jirgin saman da ya kwasp gawarwakin sojojin Turkiya da suka yi hatsari a Georgia, Hoto: Anadolu / Contributor
Source: Getty Images

Jirgin sojin Turkiyya ya yi hatsari a Georgia

Kara karanta wannan

Wike ya sake kare kansa bayan arangama da soja, ya fadi yadda yake kallon sojoji

A cikin jawabinsa na kai tsaye, shugaban kasa Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa an gano akwatin black box na jirgin kuma an fara bincike nan take, in ji rahoton Reuters.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun gano gawarwakin shahidai 19, muna ci gaba da neman wanda ya rage,” in ji Erdogan.

Hatsarin ya zama mafi muni da rundunar sojin Turkiyya ta fuskanta tun shekarar 2020, lokacin da sojojin Rasha masu goyon bayan Siriya suka kashe sojojin Turkiyya 33 a Idlib.

Bidiyon da aka dauka daga wurin hatsarin ya nuna motocin gaggawa da motocin soji suna yawo a kusa da bangaren jirgin da ya kone, yayin da jami’an ceto ke ci gaba da neman wadanda suka mutu.

Jirgin C-130 Hercules ne ya kashe sojoji

Turkiyya ta ce tana aiki tare da hukumomin Georgia da Azerbaijan don gudanar da bincike mai zurfi kan abin da ya haddasa hatsarin jirgin.

Kamfanin Lockheed Martin na Amurka, wanda ya kera jirgin C-130, ya ce yana ba da tasa gudunmawar wajen gudanar da binciken.

Jirgin C-130 Hercules na da injuna huɗu, kuma ana amfani da shi wajen jigilar kaya, dakarun soji da kayan aiki, har ma da ayyukan farmaki da leken asiri.

Kara karanta wannan

A.M Yerima da Wike: Jerin mutane 4 da ke da karfin ikon bai wa soja umarni a Najeriya

Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta ya nuna lokacin da jirgin ke katantanwa a sararin samaniya, wanda masana ke ganin cewa wutsiyar jirgin ce ta karye.

Ma'aikatan ceto daga Turkiyya na ci gaba da neman wadanda suka mutu a hatsarin jirgin sojin kasar a Georgia.
Hoton jami'an Turkiyya a lokacin da suke kokarin nemo gawarwakin sojojin da suka yi hatsarin jirgi a Georgia. Hoto: Anadolu / Contributor
Source: Getty Images

Binciken farko ya nuna hatsari ne, ba kai hari ba

Wani masani, Jarrod Phillips, tsohon jami’in rundunar sojin sama ta Amurka, ya ce hotunan sun nuna kamar jirgin yana zubar da mai kafin ya yi ƙoƙarin saukar gaggawa.

Rahoton FlightRadar24 ya tabbatar cewa jirgin da ya yi hatsarin yana da shekaru 57 da kera shi, kuma rundunar sojin kasar Turkiyya ta fara amfani da shi ne a shekarar 2010.

Shugaba Erdogan ya yi ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, yana mai cewa gwamnati za ta gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin hatsarin da kuma inganta jiragen sojin kasar.

Turkiyya na neman kama Netanyahu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Turkiyya ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, bisa tuhumar kisan kare-dangi a Gaza.

Hukumar kula laifuffuka ta Istanbul ta ce akwai mutane 37 da ake zargi, ciki har da ministoci da manyan hafsoshin sojan Isra’ila.

Kara karanta wannan

Tsofaffin Janar sun nuna fushi kan Wike game da rikici da sojan Najeriya

Kasar Isra’ila dai ta mayar da martani da cewa wannan mataki na urkiyya ba komai ba ne face wani salon siyasa daga Shugaba Reccap Erdogan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com