AU Ta Mayar da Martani ga Trump kan Ikirarin ana Kishe Kiristoci a Najeriya

AU Ta Mayar da Martani ga Trump kan Ikirarin ana Kishe Kiristoci a Najeriya

  • Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU), Mahmoud Ali Youssouf, ya karyata ikirarin Donald Trump cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya
  • Ya ce Musulmai ne suka fi fuskantar hare-haren Boko Haram, ba Kiristoci ba kamar yadda ake Amurka da Trump ke faman yadawa
  • Kungiyar AU ta yi kira ga shugabannin duniya da su daina yada bayanan bogi da ke iya haddasa rikicin addini a kasashe daban-daban

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

New York, US – Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU), Mahmoud Ali Youssouf, ya yi watsi da zargin tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.

Shugaban ya bayyana ikirarin da Trump da wasu daga cikin 'yan majalisar Amurka ke yada wa a matsayin labari mara tushe bllantana makama.

Kara karanta wannan

"Ba a fahimce shi ba": Shugaban CAN a Arewa ya warware barazanar Trump kan Najeriya

AU ta caccaki Donald Trump
Shugaban AU, Youssouf, Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: African Union/Donald J Trump
Source: Facebook

TRT Hausa ta wallafa cewa Youssouf, ya yi wannan bayani ne yayin taron manema labarai a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) da ke birnin New York a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

AU ta soki kalaman Trump

Channels TV ta wallafa cewa Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU), Mahmoud Ali Youssouf ya ce lamarin da ke faruwa a Arewacin Najeriya ya fi shafar Musulmai fiye da Kiristoci.

A kalamansa:

“Duk wanda ya san tarihin rikicin Boko Haram ya sani cewa Musulmai ne suka fara fuskantar hare-haren su, ba Kiristoci ba.”

Ya ce ba daidai ba ne a kwatanta rikicin da ke Najeriya da irin na ƙasashen da ke fama da zaluncin kabilanci kamar Sudan ko Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC).

Ya ce:

“Dole shugabanni su yi nazari kafin su yi irin wadannan kalmomi masu zafi, domin hakan na iya tayar da rikici tsakanin mabiya addinai."

AU ta kare Najeriya

Kungiyar AU ta jaddada cewa rikicin Boko Haram rikici ne na ta’addanci da rashin tsaro, ba na addini ba, kamar yadda wasu ke kokarin fada.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

Ta ce dakarun ƙasar sun dade suna yaki da ‘yan ta’addan masu tsattsauran ra’ayi, wadanda suka kashe dubunnaan mutane tsawon shekaru 15 da suka wuce.

AU ta ce ana kashe Musulmi fiye da kiristocin Najeriya
Hoton Shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Wannan martani na AU ya zo ne bayan Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka da ta fara shirin kai hari kan Najeriya saboda zargin kashe kiristoci saboda addininsu.

Trump ya kuma yi barazanar cewa idan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kasa hana wannan zargi, Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Najeriya.

Ya kara da cewa har ma ta iya tura sojojinta domin, a cewarsa, kawar da ‘yan ta’addan Musulmai masu tsattsauran ra’ayi.

Gwamnatin Tinubu: Ana ganawa da Amurka

A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin Najeriya ta ce tattaunawar diflomasiyya da Amurka na tafiya yadda ya kama kuma tana haifar da sakamako mai kyau bayan zargin Donald Trump.

Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotanni daga Amurka sun zargi gwamnatin Najeriya da yin shiru kan abin da suka kira kisan Kiristoci — zargin da gwamnatin Najeriya ta karyata kai tsaye.

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Babachir ya fasa kwai kan rawar da Buhari da Tinubu suka taka

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa an bude hanyoyin sadarwa tsakanin manyan jami’an diflomasiyya na kasashen biyu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng