Majalisar Isra'ila Ta Karanta Kudirin Hukuncin Kisa ga Falasdinawa
- Majalisar Isra’ila ta amince da kudurorin da suka shafi kisa ga Falasdinawa da rufe kafafen yada labaran waje
- Kudurin farko ya shafi zartar da hukuncin kisa ga Falasdinawa da ake zargi da kashe Isra’ilawa saboda ƙiyayya
- Kudurin na biyu kuma zai bai wa gwamnati ikon rufe kafafen yada labaran duniya ba tare da umarnin kotun kasar ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tel Aviv – A matakin farko, majalisar dokokin Isra’ila ta amince da kudurori guda biyu da suka jawo muhawara, wanda daya ya shafi hukuncin kisa ga Falasdinawa.
Rahotanni sun nuna cewa ɗayan kuma ya shafi rufe kafafen yada labaran kasashen waje ba tare da izinin kotu ba.

Source: Getty Images
TRT ta rahoto cewa wadannan kudurori sun samu goyon bayan manyan abokan Benjamin Netanyahu daga bangaren ‘yan ra’ayin rikau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin yanzu kuma, kudurorin za su tafi kwamitin majalisa domin karin tattaunawa kafin amincewa ta karshe.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun bayyana damuwa cewa wadannan kudurori na nufin takura Falasdinawa tare da kara zurfafa wariyar launin fata da ake yi a yankunan da Isra’ila ta mamaye.
Batun hukuncin kisa ga Falasdinawa
Financial Times ta ce kudurin farko dai Ministan tsaro na kasa, Itamar Ben-Gvir, daga jam’iyyar Jewish Power ne ya gabatar da shi.
Kudirin ya nemi bai wa kotuna damar zartar da hukuncin kisa ga Falasdinawa da ake zargi da kashe Isra’ilawa “saboda ƙiyayya ko manufar cutar da Isra’ila.”
An amince da kudurin a karatu na farko da kuri’u 39 masu goyon baya da 16 masu adawa daga cikin mambobin majalisar 120.
Ben-Gvir ya bayyana hakan a matsayin matakin nasara da cewa:
“Wannan tarihi ne. Mun yi alkawari, mun cika.”
Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun soki wannan mataki, suna cewa an yi niyya ne don takura Falasdinawa da kuma halasta wariyar siyasa da addini a kasa mai rikici.
An yi hayaniya a majalisar Isra'ila
Taron majalisar ya rikide zuwa hayaniya bayan dan majalisa, Ayman Odeh, ya yi muhawara da Ben-Gvir har kusan ya kai ga fada.
Wannan lamari ya kara bayyana tsananin rarrabuwar kawuna da tashin hankali a cikin majalisar Isra’ila.
Idan wannan kuduri ya zama doka, zai kasance karo na farko da Isra’ila za ta aiwatar da hukuncin kisa tun bayan kisan Adolf Eichmann a shekarar 1962.
Isra'ila na son rufe kafafen yada labarai
Majalisar ta kuma amince da wani kuduri da zai ba da ikon dindindin ga gwamnati ta rufe kafafen yada labaran kasashen waje da take ganin “na barazana ne ga tsaron Isra’ila.”
Kudurin wanda dan majalisar jam’iyyar Likud, Ariel Kallner, ya gabatar, ya wuce karatu na farko da kuri’u 50 masu goyon baya da 41 masu adawa.

Source: Getty Images
Sai dai masana shari’a sun gargadi cewa wannan doka za ta tauye ‘yancin kafafen yada labarai da kuma take tsarin kundin dokar kasa.

Kara karanta wannan
Gwamna Fintiri zai tura dalibai 100 karatu kasar waje, zai kashe Naira Biliyan 2.7
Amurka ta sa Isra'ila kai hari Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban Amurka ya fito karara ya nuna cewa su suka dauki nauyin kai hari Iran.
A watan Yunin 2025 ne kasar Isra'ila ta kaddamar da hari Iran, inda aka rika musayar wuta tsakanin kasashen na 'yan kwanaki.
Yayin da aka kaddamar da hare haren, Amurka ta musa cewa tana da hannu a lamarin, amma yanzu Trump ya dauki nauyin kai harin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

