Amurka Ta Shiga Matsalar Jiragen Sama yayin da Trump ke Barazana ga Najeriya

Amurka Ta Shiga Matsalar Jiragen Sama yayin da Trump ke Barazana ga Najeriya

  • An samu jinkiri da soke tashin fiye da jirage 10,000 a fadin Amurka, lamarin da ya zama mafi muni tun bayan rufe gwamnatin kasar
  • Ma’aikatar sufuri ta gargadi cewa matsalar na iya tsananta idan gwamnatin ta ci gaba da kasancewa a kulle
  • ‘Yan majalisar dattawa da fadar White House sun fara tattaunawa don kawo karshen wannan matsalar da ta haifar da cikas a kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington, DC – Jiragen sama fiye da 10,000 sun yi jinkiri ko soke tashinsu su a fadin Amurka a ranar Lahadi, a yayin da ake cigaba da rufe gwamnati da ya shafi filayen jirage sama 40.

Bisa bayanan hukumomi, wannan ne karo na farko da aka samu cikas mai girma a rana guda tun bayan da aka rufe gwamnati da ya tilasta rage tashi a filayen jirage da dama.

Kara karanta wannan

Donald Trump Ya Sa Sojojin Kasar Amurka Sun kai Hari Sun Kashe Mutane

Mutane na jiran jirage a Amurka
Yadda matafiya suka makale a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

USA Today ta ce hakan ya haifar da rudani ga matafiya a birane daban-daban, yayin da hukumomi ke gargadi cewa lamarin na iya raguwa zuwa matakin da ba zai iya biyan bukatar matafiya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matsalar tashin jiragen sama a Amurka

Rahotanni sun nuna cewa da karfe 10:00 na dare a ranar Lahadi, an samu jinkirin fiye da jirage 10,000 da aka tsara za su tashi a Amurka.

Har ila yau, sama da jirage 3,200 ne aka soke tashinsu gaba daya a wannan rana saboda matsalar da ake fuskanta.

BBC ta rahoto cewa a ranar Asabar da ta gabata, tashin sama da jirage 1,400 aka soke, yayin da aka samu jinkirin fiye da 6,000.

A ranar Juma’a kuwa, rahotanni sun nuna cewa yawan jinkirin tashin jiragen sama da aka samu a Amurka ya haura 7,000.

Ma’aikatar kula da zirga-zirgar jiragen sama (FAA) ta sanar cewa za ta rage yawan tashi a filayen jirage zuwa kashi 10% saboda gajiya da rashin albashin ma’aikatan kula da zirga-zirga.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta kawo tsarin da jiragen kasa za su yi aiki a kowace jihar Najeriya

Kokarin da gwamnatin Amurka ke yi

Rahotanni sun bayyana cewa a daren Lahadi, wasu sanatoci ‘yan jam’iyyar Democrat sun cimma matsaya da ‘yan Republican tare da fadar White House domin nemo hanyar kawo karshen lamarin.

Wannan ne karo na farko cikin wata guda da aka samu tattaunawa mai ma’ana tsakanin bangarorin biyu, inda ake fatan hakan zai zama matakin farko na kawo karshen rikicin da ya addabi kasar.

Filin jirgin saman Amurka
Wasu matafiya a filin jirgin saman Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai har yanzu ana cikin ce-ce-ku-ce a majalisar dokoki kan yadda za a kawo karshen wannan rikici wanda ya kai kwanaki 39 – mafi tsawo a tarihin Amurka.

Matafiyan Amurka sun koka da jinkiri

A filin jirgin sama na Denver, wasu matafiya, Kat da TJ Leahy, sun bayyana cewa jirginsu na dawowa Tampa, Florida, zai yi jinkiri.

Yayin da suke jira a filin jirgin saman, sun ce sun zabi yin hutu a Colorado maimakon Turai saboda yanayin sanyi.

Halin rashin biyan albashi ga ma’aikatan gwamnati ya kara jefa bangaren zirga-zirgar jiragen sama cikin rudani, yayin da yawancin ma’aikatan ke fuskantar gajiya da rashin kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ware N400bn domin wasu manyan ayyuka a sassan Najeriya

Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka

A wani labarin, kun ji cewa Koriya ta Arewa ta fitar da gargadi ga Amurka tare da barazanar kai farmaki.

Hakan na zuwa ne bayan wani jirgin ruwan sojojin Amurka ya bulla wani yanki na Koriya ta Kudu a kwanan nan.

Koriya ta Arewa ta zargi Amurka ta hada baki da Koriya ta Kudu domin kawo mata cikas a kan lamuran tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng