Zargin Kisan Kiristoci: Trump Ya Yi Barazanar Daukar Matakin Soji a Najeriya
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar aika sojojin Amurka zuwa Najeriya idan gwamnati ta gaza daukar matakai
- Hakan na zuwa bayan Amurka ta nuna damuwa kan zargin yiwa Kiristoci kisan kiyashi wanda ya tayar da hankula
- Trump ya ce zai hana Najeriya tallafin ketare, ya kuma dauki mataki “mai tsauri cikin gaggawa” kan masu tayar da kayar baya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washinton DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana shirin da ya yi domin daukar mataki kan Najeriya.
Trump ya yi barazanar kai farmakin sojoji a Najeriya tare da dakatar da duk wani tallafin kasashen waje idan gwamnatin Najeriya ta cigaba da “barin ana kashe Kiristoci.”

Source: Twitter
Trump ya wallafa a kafar sada zumunta da Reuters ta gano yayin da ake zargin Najeriya da kisan Kiristoci a kasar.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Sanata Ndume ya dora laifi kan gwamnatin Tinubu da Majalisar Dattawa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barazanar da Trump ya yi ga Najeriya
A ranar Juma’a 31 ga watan Oktobar 2025 kuma, Trump ya yi barazanar sanya takunkumi kan Najeriya, yana bayyana ta a matsayin “kasa mai matsalar ‘yancin addini.”
Sai dai gwamnatin Najeriya ta karyata ikirarin, tana cewa kasar ba ta nuna wariyar addini kuma hare-haren suna shafar kowane bangare.
Najeriya, wacce ke da mutane miliyan 220, ita ce mafi yawan jama’a a Afrika, kuma rabin al’ummar Musulmi ne, rabin Kiristoci, inda kungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram ke kai hare-hare a kullum.
Wannan ya jawo salwantar rayuka daga bangarorin biyu, Kiristoci da Musulmi yayin hukumomi ke kokarin kawo karshensa.

Source: Getty Images
Abin da Trump ya shirya kan Najeriya
Sanarwar ta ce idan gwamnatin Najeriya ba ta dakatar da cin zarafin Kiristoci ba, zai aika sojojin Amurka “cike da makamai” domin “share ‘yan ta’adda masu kisan gilla.”
A cewarsa:
“Ina umartar Ma’aikatar Yakinmu ta fara shiri. Idan muka kai hari, zai kasance mai sauri, kamar yadda wadannan ‘yan ta’adda ke kai wa Kiristocinmu masu daraja hari!”

Kara karanta wannan
Tinubu ya maida martani ga Shugaban Amurka, Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
Masu sharhi sun ce maganganun Trump na iya tayar da tarzoma, yayin da wasu ke ganin matsalar tsaron Najeriya ta tabarbare sosai.
Hukumomi a Najeriya dai sun ce suna daukar duk matakan da suka dace domin kare ‘yancin kowa, ba tare da nuna bambanci ba, cewar rahoton Politico.
A halin yanzu, ana sa ido kan ko gwamnatin Amurka zata dauki matakin zahiri, musamman ganin irin tsaurin matakin da Trump ya yi gargadi da shi kan abin da ya kira kare ‘yancin addini.
Najeriya ta yi martani mai zafi ga Trump
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Tarayya ta ce ikirarin Donald Trump na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya ba gaskiya ba ne.
Ma'aikatar harkokin waje ta bayyana cewa ’yan Najeriya na rayuwa tare cikin zaman lafiya ba tare da bambancin addini ba.
Gwamnatin Najeriya kara da cewa za ta ci gaba da hulɗa da kasar Amurka domin inganta fahimtar juna da zaman lafiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng