Nukiliyar Iran: Khamenei Ya Kira Amurka 'Yar Ta'adda' kan Kashe Mutanen Gaza

Nukiliyar Iran: Khamenei Ya Kira Amurka 'Yar Ta'adda' kan Kashe Mutanen Gaza

  • Ayatollah Ali Khamenei ya ce Iran ba za ta karbi tayin tattaunawar da Shugaba Donald Trump ya yi ba kan makamin nukiliya
  • Khamenei ya musanta ikirarin Trump cewa Amurka da Isra’ila sun lalata cibiyar nukiliyar Iran a hare haren da aka kai musu
  • Ya ƙara zargin Amurka da zama kanwa uwar gami kan farmakin da ya rutsa da rayuka a Gaza, inda ya ambaci mace-mace

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran — Ayatollah Ali Khamenei ya ƙi yarda da tayin tattaunawa da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi masa.

Jagoran ya nuna kin amincewa ne inda ya bayyana cewa tattaunawa irin wacce aka yi da matsin lamba ba yarjejeniya bace.

Khamenei da Trump
Jagoran Iran, Khamenei da shugaba Trump na Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cikin wasu sakonni da ya wallafa a X a ranar Litinin, Khamenei ya musanta ikirarin Shugaba Trump da cewa Amurka ta lalata cibiyar nukiliyar Iran.

Kara karanta wannan

'Yar ƙwaya ce fa yanzu': Sanata ya ƙaryata zargin cin zarafin matarsa a gidan aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Khamenei ya bayyana cewa duk wata yarjejeniya da aka tilasta wa Iran ba za ta yi aiki ba, domin a cewarsa tilastawa da wulakanci ne ba yarjejeniya ba.

Kalaman Ali Khamenei kan Donald Trump

Khamenei ya ambaci jawabin Trump a majalisar Isra’ila inda Shugaban Amurka ya ce zai yi kyau a samu yarjejeniya tsakanin Washington da Tehran bayan tashin hankali a Gaza.

Khamenei ya ce:

“Idan yarjejeniya na tattare da tilastawa da yarda da sakamako da aka riga aka tsara, ba yarjejeniya ba ce sai dai danniya.”

Ya ƙara da rubutu cikin fushi kan ikirarin cewa an lalata nukiliyar Iran, inda ya ce:

“To, ku ci gaba da mafarki!”

Shugaban ya kuma yi tambaya da cewa me ya shafi Amurka kan mallakar nukiliya da wasu kasashe ke yi.

Tattaunawar da Amurka ta yi da Iran

Reuters ta rahoto cewa a baya, Tehran da Washington sun gudanar da tattaunawa kai-tsaye sau biyar.

Kara karanta wannan

'An fi kashe Musulmi,' Hadimin Trump ya karyata zargin kisan Kiristoci a Najeriya

An dakatar da tattaunawar ne bayan harin da Isra'ila ta kai Iran da ya jawo yaki na kwanaki 12 da aka ce an kai wa wasu wuraren nukiliyar Tehran.

Khamenei ya nuna rashin jin daɗinsa kan irin matakan da Amurka ke ɗauka, yana mai cewa irin waɗannan hanyoyi ba su dace ba kuma suna nuna son kai.

Amurka: Maganar Khamenei kan Gaza

Khamenei ya yi tsokaci mai tsanani kan halin da ake ciki a Gaza, inda ya ambaci adadin mace-macen yara da ake yi a yankin.

“Kun kashe yara kuma kuce kuna yaki da ta’addanci? Ku ne ‘yan ta’adda!”

in ji shi.

Ya zargi Amurka da bayar da kayan yaki ga Isra’ila da kuma zama abokin laifi a kashe-kashen da aka yi wa farar hula a Gaza.

Wani yanki na Gaza
Yadda Isra'ila ta ruguza yankunan Gaza. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta kai hare-hare Gaza

A wani rahoton, kun ji cewa Isra'ila ta kai hare-hare Gaza inda ta kashe Falasdinawa da dama ciki har da yara.

Hakan na zuwa ne bayan zama da aka yi a kasar Masar domin kawo karshen zubar da jini da aka yi a Gaza.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta jero abubuwan da suka jawo karyewar farashin abinci warwas

Kasashe da dama sun yi Allah wadai da shugaban Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan harin da ya kai bayan kulla yarjejeniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng