Ecuador: Matasa kusan 500 Sun Rufe Shugaban Kasa da Jifa da Duwatsu

Ecuador: Matasa kusan 500 Sun Rufe Shugaban Kasa da Jifa da Duwatsu

  • Wasu mutane kimanin 500 ne suka kewaye motar shugaban ƙasar Ecuador, Daniel Noboa, inda suka jefa duwatsu a kan motarsa
  • Gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa motar tasa ta samu matsala yayin da jami’an tsaro suka cafke mutane biyar da ake zargi
  • Gwamnatin Ecuador ta bayyana cewa za a gurfanar da masu hannu a lamarin bisa zargin laifin ta’addanci da yunƙurin kisan kai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ecuador – Shugaban ƙasar Ecuador, Daniel Noboa, ya tsira daga wani yunƙurin kai masa hari da wasu masu zanga-zanga suka yi a yankin Canar da ke tsakiyar ƙasar.

Lamarin ya faru ne yayin da shugaban ya isa garin El Tambo domin halartar wani taron da ya shafi aikin tsaftace muhalli da magudanan ruwa.

Ecuardor
Shugaban kasar Ecuador bayan kai masa hari. Hoto: @CynthiaGelliber
Source: Twitter

Rahoton Al-Jazeera ya bayyana cewa wasu mutane kusan 500 ne suka kewaye motar shugaban, inda suka fara jifan motocin rukunin tawagarsa da duwatsu.

Kara karanta wannan

Rigiji gabji: Atiku ya nemi a binciki Tinubu da ministocinsa kan takardun bogi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministar harkokin cikin gida ta ƙasar, Mónica Palencia Manzano, ta tabbatar da cewa motar shugaban ta samu matsala.

A kaiwa shugaban Ecuador hari

A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Ecuador ta ce harin yunƙuri ne da nufin hana shugaban isar da wani muhimmin aiki ga al’umma.

Rahoton Yahoo News ya nuna cewa gwamnatin ta ce:

“Sun bi umarnin masu tsattsauran ra’ayi suka kai hari kan motocin shugaban da ke ɗauke da fararen hula.”

Gwamnatin ta bayyana cewa duk wanda aka kama cikin lamarin zai fuskanci tuhuma ta ta’addanci da kuma yunƙurin kisan kai.

Har ila yau, an tabbatar da cafke mutane biyar da ake zargi da hannu a harin da aka kaiwa shugaban kasar.

Shugaban kasar Ecuardor yana wani jawabi
Shugaban kasar Ecuador yana wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An yi wa shugaban ruwan duwatsu

Bidiyon da ofishin shugaban ya wallafa a kafafen sada zumunta ya nuna motocin shugaban na tafiya cikin jerin gwanon masu zanga-zanga yayin da wasu ke ɗaga duwatsu suna jifarsu.

Kara karanta wannan

Kano ta dauki sabon kambu, ta zama ta 2 a tara kudin shiga a jihohin Najeriya

An ga gilashin motar shugaban ya fashe sakamakon jifa, yayin da wani hoto kuma ya nuna motar SUV mai launin azurfa da gilashinta ya fashe.

Sai dai babu tabbacin cewa an yi amfani da bindiga a yayin harin, ofishin shugaban ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kare lafiyar Noboa cikin kwarewa.

SHUGABA Noboa da ƙoƙarin da yake yi

Daniel Noboa, wanda shi ne shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a tarihin Ecuador, ya sake lashe zaɓe a watan Afrilu bayan fafatawa da ɗan adawa, Luisa Gonzalez.

Wannan ne wa’adinsa na farko cikakke tun bayan da ya karɓi mulki don kammala wa’adin tsohon shugaban, Guillermo Lasso.

Daga lokacin da ya hau karagar mulki, Noboa ya maida yaki da aikata laifuffuka da fataucin miyagun ƙwayoyi a matsayin ginshiƙin mulkinsa.

Shugaban Malawi ya sha kaye

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Malawi, Lazarus McCarthy Chakwera ya sha kaye a zaben kasar da aka yi.

Lazarus McCarthy Chakwera ya amince da shan kaye tun kafin a bayyana sakamakon zaben kasar a hukumance.

Kara karanta wannan

Shettima ya ba da mamaki da ya kira Sanusi II da Sarkin Kano a taro a Abuja

Legit Hausa ta rahoto cewa mutane da kungiyoyi a fadin duniya sun yaba masa bisa amincewa da shan kaye da ya yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng