Falasdinu: Isra'ila Ta Kashe Kiristoci, Kwace Musu Gidaje bayan Rusa Coci a Gaza
- Kwamitin kula da harkokin coci na Falasdinawa ya zargi Isra’ila da kai farmaki kan Kiristoci a Gaza da sauran yankuna
- Ya ce Isra’ila ta kai hare-hare kan manyan coci da cibiyoyin addini da asibitoci da ke karkashin kulawar Kiristoci
- Kwamitin ya bayyana cewa Kiristoci sun ragu daga kaso 12.5 a 1948 zuwa kaso 1 a yankunan da Isra’ila ta mamaye a yanzu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gaza – A ranar Lahadi, 28, Satumba, 2025, hukumar kula da harkokin coci ta shugaban Falasdinawa ta fito da kakkausar suka kan Isra’ila.
Ta yi magana tana mai cewa Isra'ila ta ruguza tushen Kiristoci a Gaza da sauran yankuna ta hanyar hare-hare kan coci, gidaje da cibiyoyin addini.

Source: Getty Images
Rahoton Anadolu ya nuna cewa sanarwa ta fito ne bayan Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi ikirarin cewa Isra’ila ita ce kasa guda tilo a Gabas ta Tsakiya da ke kare Kiristoci.

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda na yi wa Kiristocin Najeriya kisan kiyashi? Minista ya tsage gaskiya
Kwamitin ya karyata ikirarin, yana mai bayyana shi a matsayin karya da ya saba wa tarihi, tare da zargin Isra’ila da kisan kiyashi, kora daga gidaje da kuma mallakar ƙasashen Kiristoci.
Raguwar Kiristoci a yankin Gaza
Kwamitin ya bayyana cewa kafin barkewar rikicin 1948 da ake kira Nakba, Kiristoci sun kai kaso 12.5 na yawan jama’ar Falasdinu.
Amma a yau, ya ce Kiristoci sun ragu zuwa kaso 1.2% a dukkan yankin, da kuma kaso 1% a yankunan da Isra’ila ta mamaye a 1967.
A cewar kwamitin, wannan koma baya ya samo asali ne daga manufofin kora, kwace filaye, rufe wuraren bautar Kiristoci da cin zarafi da gwamnati ta yi a tsawon shekaru.
Kwamitin ya tuna da wasu manyan kashe-kashen da suka hada da harin Semiramis a 1948 da ya hallaka Kiristoci 25 da kuma kashe wasu 12 a garin Eilabun kusa da Nazaret a shekarar nan.
Hare-haren da suka ci gaba a Gaza
Tun bayan fara yaƙin Gaza a watan Oktoba 2023, Isra’ila ta kai hare-hare a kan manyan coci kamar Greek Orthodox, inda daruruwan fararen hula suka rasa rayukansu.
Rahoton TRT ya nuna cewa Isra’ila ta kai hari kan cibiyoyin da ke karkashin coci ciki har da Asibitin Al-Ahli Baptist da kuma cibiyar Orthodox Arab.
Kwamitin ya bayyana cewa gidajen Kiristoci da dama sun rushe, wasu iyalai sun tsere zuwa cikin coci don neman tsira, amma su ma cocin ba su tsira daga hare-hare ba.

Source: Twitter
Tasirin rikicin Gaza kan rayuwar Kiristoci
Sanarwar ta bayyana cewa tun daga watan Oktoba 2023 zuwa yau, Kiristoci Falasdinawa 44 ne suka mutu sakamakon hare-hare kai tsaye ko kuma rashin abinci da magunguna.
A yankin West Bank kuma, garin Kiristoci na Taybeh kusa da Ramallah ya sha fuskantar hare-hare daga Yahudawa ‘yan mamaya, yayin da coci-coci ke fuskantar barazana a tarihin su.
Haramta harkokin coci da kwace dukiya
Hukumar ta ce Isra’ila ta rufe asusun Orthodox Patriarchate da ke Urushalima, ta kafa haraji mai nauyi a kan kadarorin coci, tare da kwace gonaki da filaye na cocin Armeniyawa.

Kara karanta wannan
Shettima ya kalli shugabannin duniya, ya fadi matsayar Najeriya kan kafa kasar Falasdinawa
A Betlehem, inda aka haifi Yesu Almasihu, an ce Isra’ila ta zagaye garin da katanga, sansanonin soja da shinge sama da guda 150, lamarin da ke hana Kiristoci damar zuwa gonakinsu.
An kunyata Isra'ila a majalisar dinkin duniya
A wani rahoton, kun ji cewa kasashen duniya da dama sun ba Benjamin Netanyahu kunya yayin da ya shiga zauren majalisar dinkin duniya.
Mafi yawan kasashe sun fice daga zauren majalisar yayin da Benjamin Netanyahu ya shiga zai fara gabatar da bayani a zauren.
Rahotanni sun bayyana cewa an watsewa Natenyahu ne domin nuna adawa da kisan kare dangi da ya ke jagoranta a Gaza.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
