Trump Ya Ce an Masa Makarkashiya bayan Ya Samu Matsaloli 3 a Taron UN
- Amurka Donald Trump ya ce ya fuskanci abubuwa uku masu tayar da hankali a taron da ya halarta a New York
- Donald Trump ya ce matakan sun haɗa da tsayawar wasu na'u'rori da kuma katsewar sauti yayin jawabinsa a zauren majalisar
- Ya rubuta takarda zuwa ga shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, yana neman a gudanar da binciken gaggawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci a gudanar da bincike kan matsalolin da ya fuskanta a lokacin da ya halarci taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
Trump ya bayyana cewa wata na'ura ta tsaya cak lokacin da shi da uwargidansa Melania Trump suka nufi wucewa.

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa ya yi ikirarin cewa abubuwan ba kuskure ba ne, wani yunƙuri ne na ɓata masa suna a bainar duniya, yana mai cewa abin kunya ne babba da ya kamata a yi nadamar shi.

Kara karanta wannan
"Za ku iya rasa kimarku": Tinubu ya aika da gagarumin saƙo ga Majalisar Ɗinkin Duniya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi wa Trump dariyar matsalar na'ura
Daga cikin matsalolin da Trump ya fuskanta akwai tsayuwar na'urar da ke saukaka haurawa sama yayin da zai wuce shi da matar shi.
Al-Jazeera ta wallafa cewa Trump ya yi nuni da cewa ya samu labarin wasu jami'an majalisar dinkin duniya sun yi barkwanci kan matsalar da ya samu.
Ya bukaci a adana dukkan bidiyon da ke nuna yadda aka matsa maɓallin dakatarwa na na'urar, tare da kiran jami’an tsaro su gudanar da bincike.
“Akwai bukatar kama mutanen da suka yi hakan, domin wannan ba wasa ba ne,”
In ji shi
Jakadan Amurka a majalisar, Mike Waltz ya goyi bayan kiran shugaban kasar, inda ya ce ba za a lamunci abin da ya faru ba kuma Amurka na sa ran samun haɗin kai kan daukar mataki.

Source: Facebook
Shugaba Trump ya samu matsalar na'ura
Trump ya sake fuskantar cikas a lokacin jawabin ya koka cewa na'urar da ke nuna rubutu yayin jawabi ba ta aiki.
Daga bisani aka gyara matsalar, amma ya yi gargadin cewa “duk wanda ke kula da na'urar zai shiga cikin matsala.”
Wata majiya ta ce ofishin Fadar White House ce ke sarrafa na'urar a lokacin, inda suka haɗa kwamfutocinsu da na majalisar dinkin duniya.
Haka zalika, Trump ya nuna rashin jin daɗi kan matsalar sauti da ta faru, yana cewa shugabannin duniya ba su iya jin komai ba sai waɗanda suka yi amfani da na’urar fassara ta kunne.
Trump ya hana Iran sayayya a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Donald Trump ta hana jami'an Iran da suka je taro yi sayayya.
Rahotanni sun bayyana cewa Iran ce kadai kasar da Amurka ta sanya wa takunkumin sayayya a taron majalisar dinkin duniya na bana.
Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta dauki matakin ne domin hana shugabannin Iran damar sayen abin da talakawansu ba za su samu su saya ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
