Isra'ila: An kai Hari kan Jirage 51 da ke Dauke da Kayan Agaji zuwa Gaza

Isra'ila: An kai Hari kan Jirage 51 da ke Dauke da Kayan Agaji zuwa Gaza

  • Masu kai tallafin Flotilla sun ce an harba wasu makamai ga jiragen ruwa da ke kan hanyar Gaza domin kai kaya ga Falasdinawa
  • Rahotanni sun nuna cewa an jefa jirage marasa matuka, an katse hanyoyin sadarwa, an kuma fesa sinadarai a kan wasu jiragen
  • Isra’ila ta bayyana cewa jiragen na kan hanyar tashin hankali, tana mai neman a mika mata tallafin domin isar da shi zuwa Gaza

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gaza - Wasu jiragen ruwa da ke ɗauke da tallafi zuwa Gaza a ƙarƙashin sunan Global Sumud Flotilla sun gamu da hare-haren jirage marasa matuka.

An ruwaito cewa hare-haren sun faru ne a lokacin da jiragen ke tsaye a gabar Tekun Girka, inda aka jefa abubuwa.

Jiragen Sumud Flotilla da ke kan hanyar zuwa Gaza
Jiragen Sumud Flotilla da ke kan hanyar zuwa Gaza. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta ce zuwa yanzu babu tabbacin samun rauni ko mutuwa, amma masu shirya tafiyar sun ce hare-haren na nufin tsoratarwa da kawo rudani.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara, an yi awon gaba da mutane masu yawa

An kai hari kan masu zuwa Gaza

Wani ɗan ƙasar Brazil da ke cikin masu shirya tafiyar, Tiago Avila ya bayyana cewa an kai hare-hare 10 kan wasu jirage.

Rahoton New York Times ya nuna cewa ya ƙara da cewa an kuma fesa wasu sinadarai da ake zargin masu kai harin ne suka yi amfani da su.

Haka kuma, wani ɗan gwagwarmayar Amurka mai suna Greg Stoker ya tabbatar da cewa jirginsu da ke bakin gabar Crete ya gamu da hare-haren jirage marasa matuka.

Ya ce an jefa ƙaramin abu mai fashewa a kan jirgin, sannan an katse musu sadarwar VHF inda aka maye gurbin ta da saƙonnin da suka haɗa da waƙoƙi.

Matsayar Isra’ila kan 'yan Flotilla

Duk da cewa hukumomin Isra’ila ba su yi karin bayani kan hare-haren da ake magana a kai ba, ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta ce jiragen Flotilla suna bin hanya mai tashin hankali.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga dauke da makamai sun sace dan majalisa a Filato

Tel Aviv ya nemi a mika kayayyakin tallafi ga Isra’ila domin isar da su zuwa Gaza ta tashar Ashkelon Marina cikin lumana.

Wani yankin Gaza da Isra'ila ta kai wa hari
Wani yankin Gaza da Isra'ila ta kai wa hari. Hoto: Getty Images
Source: AFP

Isra’ila ta yi gargadin cewa idan jiragen suka ƙi wannan tsari, za ta ɗauki matakai na hana su shiga yankin, tana mai cewa za ta yi duk abin da ya dace don kare lafiyar fasinjojin.

Sai dai Avila ya soki wannan matsaya, yana mai cewa ba za a iya amincewa da Isra’ila ba domin tana da hannu wajen kashe-kashen da ake yi a Gaza.

Tallafin da 'yan Flotilla za su kai Gaza

Tawagar Flotilla da ta ƙunshi jiragen ruwa 51 ta taso ne daga Italy a farkon watan nan da manufar karya takunkumin da Isra’ila ta sanya wa Gaza da kuma isar da tallafi kai tsaye.

Tun kafin wannan lokaci, jiragen sun riga sun fuskanci hare-hare a Tunisia inda suka tsaya na ɗan lokaci kafin su ci gaba da tafiya zuwa Gaza.

Kasashe sun amince da kafa Falasdinu

A wani rahoton, kun ji cewa Isra'ila na cigaba da samun rashin karbuwa a duniya kan hare haren da take kai wa Gaza.

Kara karanta wannan

Rashawa: Amurka za ta rika daukar mataki mai tsauri kan manyan Najeriya

Kasashen duniya da a baya ba su amince da kafa kasar Falasdinawa ba, musamman a Turai sun yarda da kasar a yanzu.

Faransa da Birtaniya sun bayyana cewa sun yarda da kasar Falasdinawa duk da sukar da Amurka da Isra'ila ke yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng