Ta'addanci: Shugaban Nijar, Tchiani Ya Fito da Sababbin Zarge Zarge a kan Faransa
- Shugaban mulkin soja na jamhuriyyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya zargi Faransa da ba ‘yan ta’adda makamai da jiragen yaki
- Ya ce Faransa na kokarin hana hadin gwiwar kasashen Sahel (AES) samun nasara saboda yana kallonsu a matsayin barazana gare ta
- Tchiani ya ce makasudin Faransa shi ne hana kasashen Sahel mallakar albarkatun kasa bayan ta kwashe shekaru tana morarsu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Niger – Shugaban mulkin soja na kasar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya bayyana cewa Faransa na bai wa kungiyoyin ‘yan ta’adda makamai.
Ya kara da zargin cewa haka kuma kasar tana taimaka wa miyagun mutanen da jiragen yaki don hana zaman lafiya a yankin Sahel da Tafkin Chadi.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a shafin X cewa, Tchiani ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na kasa a karshen mako.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin Nijar a kan kasar Faransa
Janar Abdourahmane Tchiani ya ce Faransa, tare da hadin kan wasu kasashen Yammacin duniya, na kokarin hana ci gaban AES, wacce ta kunshi Nijar, Mali da Burkina Faso.
Ya ce:
“Faransa da kawayenta suna kokarin su tabbatar daya daga cikin kasashenmu ta fadi, domin su sake samun damar dawowa ta bayan gida."
Ya kara da cewa, Faransa na sama wa ISWAP da Boko Haram makamai, domin su ci gaba da tayar da zaune tsaye a Najeriya, Nijar, Mali, Burkina Faso da Chadi.
Ya kuma zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna kusanci da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron duk da wannan zargi.
Tchiani ya ce ana hura wuta a Sahel
Tchiani ya ce a watan Janairu 2025, an tura mayakan Boko Haram 150 zuwa wasu wurare a iyakokin Benin, inda su ka ci gaba da karfi.
Ya ce:

Kara karanta wannan
Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027
“Daga baya sun kara yawan ‘yan ISWAP zuwa 200, sannan zuwa 250 domin su kai hare-hare a Nijar da yankin Sahel gaba daya. Faransa ce ta ba su makamai sannan aka girke su a Udullibi, kusa da iyakokinmu da suka shiga.”
Ya tunatar da irin gudunmawar da sojojin Nijar da Chadi suka bayar wajen yaki da ta’addanci a Najeriya, musamman a Borno.

Source: Facebook
Ya tunatar da cewa Janar Muhammadu Toumba na Nijar da wani kwamanda daga Chadi suka jagoranci kwashe ISWAP daga Damasak zuwa Malam Fatori.
Tchiani ya bayyana cewa Faransa da kawayenta na ganin nasarar AES a matsayin barazana, don haka suka mara wa ta'addanci baya don yankin kada ya zauna lafiya.
Ya kuma zargi Faransa da kwasar albarkatun kasa irin su uranium, zinari da albarkatun ruwa na tsawon shekaru, amma ta bar mutanen Nijar cikin fatara.
Janar Abdourahmane Tchiani ya bukaci al’ummar Nijar da sauran kasashen AES da su ci gaba da kasancewa masu himma da hadin kai don ci gaba da cin gashin kansu.
Shugaban Nijar ya dura kan Najeriya
A baya, mun wallafa cewa Shugaban gwamnatin soja na Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya sake zargin Najeriya da wasu kasashen duniya da jawo mata matsala.
Ya yi zargin suna hada kai da Faransa da Amurka domin daukar nauyin ayyukan ta’addanci a cikin kasarsa, domin hana jama'a zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijar.
A wata hira da ya yi ta sa’o’i uku, Tchiani ya ce ana kitsa wasu makirci da shawarwari na sirri a Najeriya domin ganin Nijar ta fada cikin rikici da tabarbarewar kwanciyar hankali.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

