Isra'ila Ta Samu Koma Baya, Birtaniya da wasu Manyan Kasashe 2 Sun Amince da Falasdinu

Isra'ila Ta Samu Koma Baya, Birtaniya da wasu Manyan Kasashe 2 Sun Amince da Falasdinu

  • Falasdinawa sun samu tagomashi a burinsu na ganin sun samu kasa mai 'yanci da cin gashin kanta
  • Kasashen Birtaniya, Canada da Australia sun amince da Falasdinu a matsayin kasa mai 'yanci a hukumance
  • Sai dai, matakin bai yi wa kasar Isra'ila dadi ba, inda ministan tsaronta ya fito ya soki amincewa da Falasdinu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Landan, Birtaniya - Kasashen Biritaniya, Canada da Australia sun amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai 'yanci.

Kasashen uku sun amince da kasar Falasdinu ne a ranar Lahadi, 21 ga watan Satumban 2025.

Birtaniya ta amince da kasar Falasdinu
Hoton Firaministan Birtaniya, Keir Stermer da Firaministan Canada, Mark Carney Hoto: @MarkJCarney, @Keir_Starmer
Source: Twitter

Jaridar Reuters ta rahoto cewa ana yi wa matakin kallon wanda aka ɗauka sakamakon gajiya da yakin Gaza da kuma kokarin karfafa mafitar kafa kasashe biyu.

Sai dai, ana tsammanin matakin zai fusata Isra’ila da babban abokiyarta, Amurka.

Birtaniya, Canada sun amince da kasar Falasdinu

Kara karanta wannan

kafa kasar Gaza: Kasashen Afrika 4 da ba su goyi bayan Falasdinu ko Isra'ila ba

Shawarar da kasashen uku manya na Yammacin duniya, waɗanda a baya suka kasance abokan Isra’ila suka ɗauka, ta sanya su cikin kasashe kusan 140 da ke goyon bayan burin Falasɗinawa na kafa kasa mai cin gashin kanta daga yankunan da Isra’ila ta mamaye.

Shugaban Birtaniya, Keir Steirmer ta dauki matakin ne don dawo da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

"A yau, domin dawo da shirin samar da zaman lafiya tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila, da kuma samar da kasa biyu, Birtaniya ta amince da kasar Falasɗinu a hukumance."

- Keir Starmer

Yayin da yake sanar da matsayin kasarsa, Firaministan Canada, Mark Carney, ya ce matakin zai karfafa masu neman zaman lafiya da kawar da kungiyar Hamas.

“Wannan mataki ba shi da alaƙa da halatta ta’addanci, kuma ba lada ba ne a gare shi."

- Mark Carney

Ana sa ran wasu kasashe, ciki har da Faransa, za su bi sahu a wannan makon yayin babban taron majalisar dinkin duniya a birnin New York.

Canada ta amince da kasar Falasdinu
Firaministan kasar Canada, Mark Carney Hoto: @MarkJCarney
Source: Twitter

Falasɗinawa sun yi maraba da amincewar

Shugaban Falasɗinu, Mahmoud Abbas, ya yi maraba da wannan mataki, yana mai cewa zai taimaka wajen share hanya ga kasar Palasɗinu ta rayu kusa da kasar Isra’ila cikin tsaro, zaman lafiya da makwabtaka mai kyau.

Kara karanta wannan

'Yan fansho sun fusata, suna shirin fara zanga zanga tsirara a fadin Najeriya

Sai dai ministan tsaro na Isra’ila, Itamar Ben-Gvir, ya bayyana matakin da Biritaniya, Canada da Australia suka ɗauka a matsayin lada ga 'yan kungiyar Hamas sakamakon harin da su ka kai a Oktoba 2023.

A cewar alkaluman Isra'la, harin ya kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu 251.

Bayan haka, yaƙin da Isra’ila ta kaddamar ya kashe sama da Palasɗinawa 65,000, mafi yawansu fararen hula, a cewar hukumomin lafiya na Gaza.

Hakazalika ya haifar da yunwa, rusa mafi yawan gine-gine da tilasta yawancin jama’a barin gidajensu sau da dama.

An zargi Isra'ila da kisan kare dangi

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamitin bincike na majalisar dinkin duniya ya zargi Isra'ila da kisan kare dangi a Gaza.

Rahoton kwamitin ya bayyana cewa akwai niyyar a hallaka al'ummar Falasdinu a Gaza ta hanyar kisa da muzguna musu.

Shaidun da aka tattara sun nuna cewa akwai manufar share al'ummar Gaza daga doron kasa a yakin da Isra'ila take yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng