Trump Ya Ga Ta Kansa, An Masa Ihu ana Zanga Zanga a London

Trump Ya Ga Ta Kansa, An Masa Ihu ana Zanga Zanga a London

  • Dubban mutane sun taru a London don nuna adawa da ziyarar shugaban Amurka Donald Trump karo na biyu
  • Gamayyar ƙungiya mai adawa da Trump da ke da ƙungiyoyi sama da 50 a karkashinta ne ta shirya masa zanga zanga
  • Rundunar ‘yan sanda ta ce mutane 5,000 ne suka halarci gangamin tare da jami’ai fiye da 1,600 da aka tura wurin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

London – Dubban mutane ne suka fito a titunan birnin Landan domin nuna adawa da ziyarar shugaban Amurka, Donald Trump karo na biyu a Birtaniya.

Masu zanga-zangar suna ɗauke da alamu da ke nuna ƙin amincewa da manufofin Trump da suka haɗa da kin wariyar launi da yaki da sayar da makamai ga Isra’ila.

Trump na zaune da Sarki Charles yayin da wasu ke zanga zanga a gefe
Trump na zaune da Sarki Charles yayin da wasu ke zanga zanga a gefe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC ta ce an shirya gagarumin tattaki ne ta hannun ƙungiyar adawa da Trump, wadda ta haɗa ƙungiyoyi masu fafutuka sama da 50.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Isra'ila, Saudi ta kulla yarjejeniyar tsaro da Pakistan mai nukiliya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ‘yan sanda ta London ta ce ta tura jami’an tsaro fiye da 1,600 ciki har da 500 daga wasu sassa don tabbatar da tsaro yayin zanga-zangar.

An yi wa Trump zanga zanga a London

Masu zanga-zangar sun tattaru ne tun daga ginin BBC kafin su nufi Whitehall, inda suka rika ɗaga hotuna da rubuce-rubuce masu cewa “ba mu son Trump” da kuma “ba mu son wariya”.

CNN ta rahoto cewa jami’an rundunar ‘yan sanda sun ce sun yi mu’amala da masu shirya taron tun kafin ranar, tare da ba su shawari da su rage cunkoso da kawo cikas ga al’umma.

Bayanin masu zanga-zangar Trump

Wata mai fafutuka, Zoe Gardner, ta bayyana cewa Trump na wakiltar “duk abin da suke ƙi”, tana mai cewa gwamnati na bukatar nuna jarumta wajen adawa da manufofinsa.

Reverend Poppy Hughes ta ce kasancewarta a wurin na da alaƙa da koyarwar Kiristanci ta zaman lafiya da tausayi.

Kara karanta wannan

Karfin hali: 'Yan bindiga sun gabatar da manyan bukatu 3 kan sulhu a Katsina

Sai dai a cikin taron, an samu wani mai goyon bayan Trump da ya bayyana shi a matsayin “shugaba mafi daraja”. Maganarsa ta gamu da ihu da ƙin amincewa daga sauran jama’a.

Masu zanga zanga kan adawa da kisan kare dangi a Gaza
Masu zanga zanga kan adawa da kisan kare dangi a Gaza. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dalilan adawa da Trump a London

Wakilan kungiyar Stop Trump Coalition sun bayyana cewa manufar zanga-zangar ita ce ƙin siyasar Trumpism da ke fifita ra'ayin Trump kan kare dimokuradiyya.

Baya ga haka kuma suna fatan ƙarfafa akidar dimokuraɗiyya da ke gina zaman lafiya, adalci na zamantakewa da haɗin kai na ƙasa da ƙasa.

Sun ce kowace gwamnati da za ta rusuna ga Trump da wariyar launi, a zahiri tana buɗe ƙofa ga rashin adalci.

Saudi ta haka kai da Pakistan

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta kulla yarjejeniyar tsaro da Pakistan mai makamin nukiliya.

Hakan na zuwa ne bayan wani hari da Isra'ila ta kai kasar Qatar duk da yadda ta ke da alaka mai kyau da Amurka a zahiri.

Yarjejeniyar da kasashen suka kulla ta hada da bayar da kariya ta kowane bangare a duk lokacin da aka kai hari ga daya daga cikinsu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng