'Dan Najeriya Ya Jefa Kansa a Badakalar 'Kudin Gado' a Amurka, Kotu Ta Yanke Hukunci

'Dan Najeriya Ya Jefa Kansa a Badakalar 'Kudin Gado' a Amurka, Kotu Ta Yanke Hukunci

  • An kama dan Najeriya mai suna, Ehis Lawrence Akhimie da laifin damfarar mutane Dala miliyan 6 a kasar Amurka
  • Bayan ya amsa laifinsa, kotun Amurka ta yanke wa mutumin hukuncin daurin watanni 97 a gidan yari
  • Ofishin Antoni Janar ya bayyana yadda Akhimie tare da abokansa suka yaudari Amurkawa da sunan za a fito masu da kudin gadon yan uwansu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Kotun Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai suna Ehis Lawrence Akhimie hukuncin fiye da shekaru takwas a gidan yari.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan kama shi da laifi a damfarar kudin gado ta sama da Dala miliyan 6 daga fiye da mutum 400, yawancinsu tsofaffi.

Kotun kasar Amurka.
Hoton gudumar kotu tare da tutar kasar Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin Antoni Janar na Amurka reshen Kudancin Florida ya fitar kwanan nan, in ji rahoton Bussiness Day.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kisa a Gombe, sun sace mutum 2 da matar aure

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun Amurka ta daure 'dan Najeriya

Sanarwar ta bayyana cewa kotu ta daure Akhimie mai shekara 41 a gidan yari na watanni 97 a ranar 11 ga Satumba, bayan ya amsa laifin hada baki wajen damfarar mutane.

Bisa bayanan kotu, Akhimie tare da abokan aikinsa sun rika tura wasiku na yaudara ga mutane a Amurka suna yin karyar cewa su jami’an banki daga ƙasar Spain.

A cikin wasikun, sun rika shaidawa mutane cewa suna da gadon miliyoyin Daloli daga ’yan uwa da aka ce sun rasu a ƙasashen waje, cewar rahoton Vanguard.

Yadda dan Najeriya ya damfari Amurkawa

Sai dai kafin a saki kuɗin, Akhimie da abokan aikinsa sun umarci waɗannan mutanen su biya kuɗaɗe da suka kira na haraji, kuɗin jigila, da sauran kudin aiki.

Sanarwar ta bayyana cewa:

“Akhimie da a abokan laifinsa sun yi amfani da wasu mutane da aka taba damfarar su, sun tara kuɗaɗen da waɗanda aka yaudara suka tura domin a yi cuku-cuku a fito masu da kudin gadon.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki bayin Allah suna ibada, an rasa rayukan mutane 22 a Nijar

"Har yanzu wadanda aka damfara ba au ga wannan kudin gado da aka ce za a turo masu ba
"A karshe, Akhimie ya amince cewa ya damfari fiye da Dala miliyan 6 daga sama da mutum 400, da yawa daga cikinsu tsofaffi ne ko kuma masu rauni.”

Gwamnatin Amurka ta tsoma baki kan laifin

Mai gabatar da ƙara na gwamnatin Amurka, Jason Quiñones, ya bayyana laifin a matsayin cin amana da tauye mutunci.

“Makirci irin wannan ba wai kawai damfara ba ce, ya taba mutuncin tsofaffinmu. Ofishinmu yana tare da waɗanda aka cuta," in ji shi.
Shugaban Amurka, Donald Trump.
Hoton shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana jawabi a wurin taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shi ma Ray Rede, mukaddashin shugaban hukumar binciken shige da fice ta HSI reshen Arizona, ya ƙara da cewa:

“Damfarar tsofaffi da sauran masu rauni ba wai kawai cin amana ba ne, har ma cin zarafin ɗan Adam. Adalci zai yi nasara, kuma duk mai laifi zai fuskanci hukunci."

Tsohon Manajan NNPCL ya yi laifi a Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa kotun Amurka ta kama wani tsohon Manaja a kamfanin NNPCL, Paulinus Okoronkwo, da laifin karɓar rashawa ta Dala miliyan 2.

Kara karanta wannan

Watanni bayan ya rasu, an gano gidan da tsohon gwamna a Najeriya ya mallaka a Landan

Kotu ta gamau da hujjojin da aka baje a gabanta cewa ya karbi cin hancin ne daga kamfanin man fetur na Addax Petroleum, wani reshe na kamfanin Sinopec na China.

Mai shari'a Jaji John Walter ya sanya ranar 1 ga Disamba don yanke hukunci yayin da Okoronkwo na iya fuskantar shekaru 10 a gidan yari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262