Waye Larry Ellison? Makusancin Shugaban Ƙasa da Ya Fi Kowa Kudi Yau a Duniya

Waye Larry Ellison? Makusancin Shugaban Ƙasa da Ya Fi Kowa Kudi Yau a Duniya

Amurka - Sababbin alkaluman da aka fitar ranar Laraba, 10 ga watan Satumba, 2025 sun nuna cewa an sauke Elon Musk daga matsayin wanda ya fi kowa kudi a duniya.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Larry Ellison, wanda ya shafe shekaru sama da 50 yana gina kamfaninsa na Oracle, shi ne ya zama babban attajirin duniya.

Larry Ellison
Hoton attajirin da ya fi kowa kudi a duniya, Larry Ellison Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hakan na kunshe a cikin jerin attajiran duniya da Bloomberg ta fitar bayan dukiyar Ellison ta yi tashin ban mamaki.

A ranar Laraba, dukiyar Ellison ta karu da Dala biliyan 100, abin da ya sa jimillar kudinsa ya kai Dala biliyan 393 ((kimanin Naira tiriliyan 591.9 a kudin Najeriya).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya sa ya kere wa Elon Musk, wanda ke da Dala biliyan 385 (kimanin ₦578.4trn) a halin yanzu, in ji rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Duniya ta yi sabon attajirin da ya fi kowa kudi, an sha gaban Elon Musk mai N570tr

Ellison, mai shekaru 81, shi ne babban mai hannun jari na kamfanin Oracle, inda hannun jarinsa ya yi tashin gwauron zabo, wanda ba a taba gani ba tun shekarar 1992.

Asali da haihuwa

An haifi Larry Ellison a ranar 17 ga Agusta, 1944 a birnin New York na Amurka, mahaifiyarsa Florence Spellman, ba ta yi aure ba kuma bayahudiya ce.

Mahaifinsa na haihuwa ɗan asalin Italiya ne, matukin jirgin ruwan rundunar sojin Amurka.

Yana ɗan watanni tara kacal ya kamu da cutar huhu, lamarin da ya sa mahaifiyarsa ta mika shi ga kawunta da ƙanwarta domin su ɗauke shi a matsayin ɗa.

Ilimi

Ellison ya yi karatu a South Shore High School a Chicago, kafin daga bisani ya shiga Jami’ar Illinois a Urbana–Champaign, inda ya fara karatu a matsayin ɗalibi a fannin likitanci.

A can ne aka zaɓe shi a matsayin dalibin kimiyya na shekara, amma bai kammala karatun ba ya bar makarantar saboda rasuwar mai rikonsa.

Daga baya ya yi ɗan lokaci a Jami’ar Chicago, inda ya yi karatun lissafi da ilimin halitta, sannan ya fara sha’awar ƙirar kwamfuta. Wannan ne ya buɗe masa ƙofa zuwa duniyar fasaha.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon babban jami'in sojin Najeriya kuma jigon APC ya rasu

Yadda Larry Ellison ya zama attajirin duniya

Hanyar Ellison zuwa wannan matsayi ta fara ne tun a 1977, lokacin da ya kafa kamfanin Software Development Laboratories tare da abokan aikinsa Bob Miner da Ed Oates a California.

Rahoton CNN ya nuna cewa a wancan lokacin, CIA ta ba su kwangilar gina wata manhajar adana bayanai mai suna “Oracle.”

Kamfanin ya sauya suna zuwa Oracle a 1982, sannan ya shiga kasuwar hannun jari a 1986.

Tsawon shekaru, Oracle ya fuskanci nasarori da ƙalubale a fannin fasaha, amma a halin yanzu yana samun babbar riba daga buƙatun fasahar Artificial Intelligence (AI).

Ellison ya shugabanci kamfanin Oracle daga 1978 zuwa 1996, kuma sau biyu yana riƙe kujerar shugaban kwamitin gudanarwa.

A 2014 ya sauka daga mukamin Shugaba (CEO), amma har yanzu shi ne shugaba kuma babban jami'in fasaha na kamfanin.

Dukiya, kasuwanci da nishaɗi

Ellison bai takaita kansa a harkar kasuwanci kaɗai ba, a 2012, ya sayi kashi 98% na tsibirin Lana’i a Hawaii, wanda aka ruwaito Bill da Melinda Gates sun yi aure a can.

Kara karanta wannan

"Ba ruwan Tinubu," An jingina harajin fetur da gwamnatin marigayi Umaru Yar'adua

Haka zalika ya kasance babban mai sha’awar jirgin ruwa. A 2013, ƙungiyar Oracle Team USA da ya tallafa wa ta lashe gasar America’s Cup.

Ya kuma kafa SailGP a 2018, gasar jiragen ruwa masu sauri wacce ta ja hankalin mashahurai kamar Anne Hathaway da ɗan kwallon Faransa Kylian Mbappé.

Ellison ya kuma farfaɗo da gasar tennis ta Indian Wells a California, wacce ake kira “fifth slam” saboda shahararta.

Siyasa da taimakon jama’a

A siyasance, attajirin mai kudin ya sha bayar da tallafi ga jam’iyyar Republican da ƙungiyoyin ra’ayin mazan jiya.

A 2022, ya ba da Dala miliyan 15 domin tallafa wa Sanata Tim Scott a takarar shugaban ƙasa, kuma a baya ya tallafa wa tawagar yakin neman zaben Marco Rubio.

Shugaba Trump da Larry Ellison.
Hoton shugaban Amurka, Donald Trump da attajirin duniya, Larry Ellison a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yanzu haka yana da kusanci da Shugaba Donald Trump, inda a farkon 2025, ya je Fadar White House tare da shugabannin manyan kamfanonin fasaha yayin da aka yi yarjejeniya kan gina cibiyar AI a Amurka.

Baya ga siyasa, Ellison ya sha bada gudummawa ga fannin lafiya. A 2016 ya ba da Dala miliyan 200 domin kafa cibiyar bincike da jinyar cutar daji a Jami’ar Kudancin California.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Bako daga kasar waje ya yi mutuwar da ba a yi tsammani ba a Abuja

Ya za a yi da dukiyar Ellison bayan mutuwa?

A 2010, Ellison ya rattaba hannu kan Giving Pledge, shirin da Bill Gates ya jagoranta, inda ya yi alƙawarin ba da akalla kashi 95% na dukiyarsa ga ayyukan alheri.

Duk da haka, kwanan nan attajirin ya ce zai karkatar da wani ɓangare zuwa cibiyar fasaha da ya kafa tare da Jami’ar Oxford.

Ngozi Okonjo-Iweala ta shiga tarihi

A wani rahoton, kun ji cewa Dr. Ngozi Okonjo-Iweala wanda ta rike Ministar kudi da tattalin arziki a Najeriya ta fito a jerin mata 100 da su ka fi kowa tasiri a duniya.

Haka zalika Jaruma Mo Abudu tana cikin matan da su ka fi karfi a duk duniya bayan ficen da tayi a wasu fina-finai da ta shirya a Nollywood.

An tattaro cewa matan da da suka fi tasiri a duniya sun yi suna ne a harkokin kasuwanci, siyasa, wasani, nishadi da, fasaha.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262