Trump zai Yi Amfani da Dalolin Kudi a Wani Shirin Korar Falasdinawa daga Gaza
- Shirin sake fasalin Gaza na gwamnatin Donald Trump ya yi nuni da yiwuwar ba wa Falasdinawa kudi domin barin yankin
- Ana tunanin kafa sababbin garuruwa masu fasahar zamani da cibiyoyin kasuwanci bayan kwashe mazauna yankin zirin Gaza
- Kasashen Larabawa na iya kalubalantar wannan tsari yayin da wasu suke ba da goyon baya ga wani shiri dabam na biliyoyin Daloli
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Donald Trump na duba wani shiri mai cike da ce-ce-ku-ce da zai iya sauya tsarin rayuwa a Gaza bayan yakin da ake ciki.
Shirin, wanda ake kira Great Trust ya kunshi biyan Falasdinawa kudi domin su bar yankin zuwa wasu kasashe.

Source: Getty Images
Rahoton the Independent ya nuna cewa tsarin ya kuma tanadi gina birane masu dauke da gine-ginen zamani, wuraren shakatawa da cibiyoyin kasuwanci a bakin tekun Gaza.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai akwai yiyuwar shirin ya gamu da suka daga kasashen makwabta na Larabawa, wadanda ke ganin bai dace a tilasta wa al’ummar Gaza barin gidajensu ba.
Trump zai biya kuɗi domin a bar Gaza
A cikin shirin, an tsara cewa za a ba kowane mutum miliyan 2 da ke zaune a Gaza kusan $5,000 domin su yi hijira zuwa wasu kasashe ko wuraren da aka tanada.
Rahoton Times of Israel ya nuna cewa baya ga hakan, za a tallafa musu da kudin haya na tsawon shekaru hudu da kuma kayan abinci na shekara guda.
Bayan kwashe mutanen, tsarin da Trump ya kawo zai fara share Gaza domin kafa garuruwa masu tsari na zamani guda shida zuwa takwas.
A tsarin, za a yi gine-ginen gilashi masu hawa-hawa, filayen wasa, gidajen shakatawa, masana’antar motoci masu lantarki da cibiyoyin sadarwa na zamani.
Yadda ake so a mayar da yankin Gaza

Kara karanta wannan
Malaman Musulunci da Kirista sun 'karyata' ikirarin da Tinubu ya yi a Kasar Brazil
Wani bangare na shirin ya kunshi gina sabuwar babbar hanya domin girmama yariman Saudiyya Mohammed bin Salman.
Haka kuma za a samar da wata babbar hanya a sunan shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, Mohammed bin Zayed al-Nahyan.
Rahotanni sun nuna cewa kamfanin Boston Consulting ne ya fitar wannan tsari a kwanakin baya.

Source: Getty Images
An fitar da tsarin ne karkashin jagorancin 'dan kasuwar Isra’ila, Michael Eisenberg da tsohon jami’in leken asirin soja, Liran Tancman.
Hanyoyin samun kudin sauya Gaza
An bayyana cewa shirin ba zai dogara da kudin gwamnatin Amurka kai tsaye ba, sai dai hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
A shirin, Isra'ila za ta cigaba da da’awar kare bukatunta a Gaza, yayin da jami’an tsaron waje da kamfanonin tsaron kasashen Yamma za su rike al’amura har sai an horar da ‘yan sanda.
Kalubalen da shirin zai iya fuskanta
A cewar rahotanni, idan aka amince da wannan tsari, akwai yiwuwar kalubale daga kasashen Larabawa musamman Saudiyya da UAE.
Wadannan kasashen sun fi nuna goyon baya ga wani shiri daban da ake kira Egypt Plan, wanda ya kai darajar Dala biliyan 53, amma bai bukaci kwashe mazauna Gaza ba.

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi gaskiyar abin da ke kai shi kasashen waje bayan dawowa daga Brazil
Nnamdi Kanu ya nemi taimakon Trump
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu ya roki Donald Trump da wasu shugabanni su shiga maganarsa.
Kanu ya bukaci shugaba Donald Trump ya saka baki gwamnatin Najeriya ta sake shi bayan shafe shekaru a rufe.
A lokacin marigayi shugaba Muhammadu Buhari aka samu nasarar kama Nnamdi Kanu a kasar Kenya kuma aka dawo da shi Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
