Yemen: Wani Harin Sama daga Isra’ila Ya Yi Ajalin Firaminista Sukutum da Guda
- Luguden bam na sojojin Isra’ila ya kashe Firaministan Houthi mai ikirari, Ahmed Ghaleb Nasser al-Rahawi
- Rahotanni sun ce ministocin harkokin wajen Houthi, shari’a, matasa da wasanni, al’amuran jama’a da kwadago na cikin wadanda suka mutu
- Kisan Rahawi ya kasance babban rashi ga Houthi, amma manyan shugabannin ƙungiyar ciki har da Abdul-Malik al-Houthi ba su mutu ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sanaa, Yemen - Wani harin sama daga kasar Isra'ila ya yi ajalin wani babban jami'in gwamnatin kasar Yemen.
Luguden bam na Isra’ila ya kashe mai ikirarim kujerar Firaminista, Ahmed Ghaleb Nasser al-Rahawi.

Source: UGC
Isra'ila ta kashe wasu jami'an gwamnatin Yemen
Rahoton BBC News ya tabbatar da cewa hari ya rutsa da wasu jami’an ƙungiyar Houthi a babban birnin Yemen, Sanaa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar Houthi da Iran ke mara wa baya ta tabbatar da mutuwar Rahawi, tana cewa jiragen yakin kasar Isra’ila sun kai hari kan taro a yankin Sanaa.
Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ta ce harin ya “kashe” Rahawi da wasu manyan jami’an kungiyar bayan samun bayanan sirri kan matsuguninsu.
Majiyoyi sun ruwaito cewa ministocin harkokin waje, shari’a, matasa da wasanni, al’amuran jama’a da kwadago na cikin wadanda aka kashe.

Source: Getty Images
Ministoci sun samu raunuka a harin Isra'ila
Ofishin shugaban Houthi, Mahdi al-Mashat, ya ce wasu ministoci sun samu raunuka, yayin da aka nada Muhammad Ahmed Miftah a matsayin sabon Firaminista.
Rahawi, wanda aka nada a watan Agustan 2024, ana kallonsa a matsayin mutum mai rauni, bai daga cikin manyan masu yanke hukunci.
Ba Abdul-Malik al-Houthi, shugaban kungiyar, ba ministan tsaro ko shugaban hafsoshin soji sun mutu a harin da aka kai ranar Alhamis.
IDF ta ce har yanzu tana tantance illar cikakken harin da aka kai kan wuraren da ‘yan Houthi ke iko da su a Sanaa.
Tasirin kungiyar Houthi a Yemen
‘Yan Houthi sun rike yawancin yankin Arewa maso Yammacin Yemen tun 2014, bayan hambarar da gwamnatin da duniya ta amince da ita daga Sanaa.
Tun barkewar rikicin Isra’ila da Hamas, Houthi sun karawa Isra’ila hare-hare, suna jefa makamai da jiragen yaki marasa matuki tare da kai hari kan jiragen ruwa.
Isra’ila ta mayar da martani da kai hare-hare sau da dama kan wuraren Houthi a Yemen, domin dakile karfin sojin kungiyar, The Times of Israel ta ruwaito.
Kisan Rahawi ya kasance daya daga cikin manyan rashe-rashe da Houthi suka yi watannin nan, duk da haka shugabancin ƙungiyar ya tsira.
Amurka ta kawo wa kasar Falasdinu cikas
Mun ba ku labarin cewa kasar Amurka ta hana shugabannin Falasɗinu shiga taron UNGA a New York, ciki har da Shugaba Mahmoud Abbas.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da soke biza da ƙin bayarwa ga jami’an PLO da PA kafin taron Majalisar Dinkin Duniya.
Wannan mataki ya biyo bayan shirin wasu ƙasashen Yamma na amincewa da ƙasar Falasɗinu a hukumance.
Asali: Legit.ng

