Bayan Daure Sarki Mai Martaba, An Kara Kama Dan Najeriya da Laifi Mai Girma a Amurka
- Kwanaki kadan bayan hukunta Sarkin gargajiya daga jihar Osun, gwamnatin Amurka ta kara kama dan Najeriya da laifin damfara
- Mutumin dan kimanin shekarar 40 a duniya, Daniel Chima Inweregbu ya amsa laifukan da ake tuhumarsa a gaban kotun Amurka
- Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta bayyana yadda Inweregbu da abokansa suka rika yaudarar mutanen kasa ta hanyar amfani da sunan Larry Pham
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amurka - Wani ɗan Najeriya mai suna Daniel Chima Inweregbu, mai shekaru 40, ya amsa laifin zamba da gwamnatin Amurka ta tuhume shi a gaban kotu.
Inweregbu ya amsa laifin hada baki wajen yaudarar yan asalin kasar Amurka, laifin da aka gano sun shafe kusan shekaru biyu su na aiwatarwa.

Source: Getty Images
A cewar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka (US DOJ), Inweregbu da abokan harkallarsa sun yi amfani da shafukan saƙon intanet da imel wajen tuntubar mutane, in ji The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda dan Najeriya ya yaudari 'yan Amurka
Gwamnatin Amurka ta ce wadanda ake tuhuma suna gabatar da kansu a matsayin wani mutum mai suna Larry Pham.
"Su na amfani da intanet da imel, a farko su na tura sako, idan ka amsa sai su kulla dangantakar soyayya ta yadda ake yarda da su.
"Daga nan, sai su fara karɓar kuɗi daga hannun waɗanda suka ruɗa, suna tura kuɗin zuwa asusun bankunan da suka buɗe da kansu," in ji DOJ.
A cewar DOJ, wannan tsarin ya jawo asarar fiye da Dala $405,000 ga waɗanda aka yaudara yan kasar Amurka, rahoton Channels tv.
Hukuncin da za iya yanke wa dan Najeriya
Kotun Amurka na iya yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari tare da tara har zuwa $250,000 kan tuhuma ta farko.
Haka kuma, a kan tuhuma ta 12, yana iya fuskantar shekaru 20 da tara har zuwa $500,000.
Zai kuma biya kuɗin tara na $100 a kan kowace tuhuma da ake masa, yayin da aka tsara zaman yanke hukunci a gaban Mai Shari'a Brown a ranar 4 ga Disamba, 2025.
Laifukan da Inweregbu ya taba aikatawa
Wannan ba shi ne karo na farko da Inweregbu ya shiga hannu ba. A shekarar 2020, kotun tarayya a Legas ta yanke masa hukuncin shekara ɗaya da rabi a gidan yari, tare da zabin tara ₦300,000 kan laifin damfara.

Source: Getty Images
A wancan lokaci, kotu ta kuma umarce shi da ya biya Dala $15,000 ga ofishin jakadancin Amurka a matsayin wani ɓangare na kuɗin da ya karɓa ta hanyar zamba.
Hukuncin da zai fuskanta a yanzu na iya zama mafi tsanani, duba da adadin kuɗaɗen da aka zargi ya karba daga hannun jama'a.
Kotu ta daure Sarki daga Najeriya a Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Kotun Amurka ya yanke wa Sarkin gargajiya daga jihar Osun, Oba Joseph Oloyede hukuncin daurin watanni 56 a gidan yari.
Hakan ya biyo bayan kama shi da laifin cinue kudin tallafin COVID-19, wanda ya karba ta hanyar amfani da bayanan karya a lasar Amurna.
Rahoton ofishin lauyan Amurka ya ce tsakanin Afrilun 2020 zuwa Fabrairun 2022, Sarkin da abokinsa Edward Oluwasanmi suka tura buƙatun bogi don samun rancen tallafin Corona.
Asali: Legit.ng

