Musulunci Ya Yi Rashi, Malamin da Ya Yi Limanci a Dakin Ka'aba Ya Rasu

Musulunci Ya Yi Rashi, Malamin da Ya Yi Limanci a Dakin Ka'aba Ya Rasu

  • Shahararren malamin hadisi Sheikh Abdul Wakeel ibn Sheikh Abdul Haq al-Hashimi ya rasu a Makkah a ranar Litinin
  • Dubban Musulmi daga sassa daban-daban na duniya sun yi jimami da addu’o’i ga marigayin, suna roƙon Allah ya gafarta masa.
  • Masu ilimi da mabiya addini sun bayyana shi a matsayin gwarzon ilimi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ilimin hadisi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudiyya - Musulmi daga sassa daban-daban na duniya sun shiga cikin jimami da alhini bayan rasuwar Sheikh Abdul Wakeel ibn Sheikh Abdul Haq al-Hashimi.

An bayyana shi a matsayin shahararren malamin hadisi kuma tsohon ladani da limamin Masallacin Harami.

Malamin Musulunci, Sheikh Abdul Wakeel da ya rasu
Malamin Musulunci, Sheikh Abdul Wakeel da ya rasu. Hoto: @insharifain|@IbnAlMufti
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanai kan rasuwar malamin ne a cikin wani sako da shafin Saudiyya na Inside the Haramain ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Makari: An fara ruguza yunkurin hada kai tsakanin malaman Izala da Darika a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya shafe rayuwarsa wajen yada ilimin hadisi da koyar ɗalibai da dama daga ƙasashe daban-daban.

An yi jana'izar Malamin a Makkah

An yi wa Sheikh Abdul Wakeel sallar jana’iza bayan sallar Asubah a Masallacin Harami, sannan aka birne shi a Makkah, inda daruruwan Musulmi suka taru domin jana'izarsa.

An bayyana cewa mutuwar shehin malamin ta bar babban gibi a tsakanin malamai da daliban ilimi, musamman lura da gudumawar da ya bayar wajen limanci a Harami.

A 'yan kwanakin nan ana ta rasa manyan malaman da addinin musulunci yake ji da su.

An yi jimamin rashin limamin Ka'aba

Bayan sanar da rasuwar Sheikh Abdul Wakeel, malamai da ɗalibai daga ko’ina cikin duniya suka bayyana alhinin su tare da yi masa addu’a.

Wani malamin addini a Saudi Arabia, Sheikh Abu Awzaa’ee Abdus-Salaam ya rubuta a Facebook cewa:

“Mun rasa babban malami a Makkah, malaminmu mai koyar da karatu sosai.

Kara karanta wannan

Duniyar Musulunci ta yi rashi: Babban malamin addini ya rasu a Gombe

"Lallai idanu na zubar da hawaye, zukata sun yi rauni, amma ba za mu fadi wani abu da ba zai gamsar da Ubangijinmu ba.”

Haka nan, Usman Waziri ya yi addu’a da cewa:

“Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya amshi ayyukansa na alheri, ya sanya shi a Aljannah.”
Musulmai suna bauta a dakin Ka'aba a kasar Saudiyya
Musulmai suna bauta a dakin Ka'aba a kasar Saudiyya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Addu’o’in jama’a daga sassa daban-daban

Mutane daga nahiyoyi daban-daban sun bayyana jimami a kafafen sada zumunta, musamman a karkashin sanarwar da kasar Saudiyya ta yi.

Rukiyat Kareem ta rubuta cewa:

“Allah ya amshi komawarsa gare shi, ya gafarta masa kuma ya sanya shi cikin Aljannah Firdausi.”

Ahmed Ibrahim ya ce:

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya sanya shi cikin masu hutu na dindindin a Firdausi.”

Ibrahim M. Bukhari kuma ya bayyana cewa:

“Allah ya gafarta masa, ya ɗaga darajarsa a cikin Aljannah.”

Shi ma Syed Kabir ya yi addu’a yana mai cewa:

“Allah ya ba shi matsayin mafi girma a cikin Aljannah, domin ya kasance shahararren malamin Musulunci.”

Ana shirin hada kan Musulman Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa limamin masallacin kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya fara kokarin hada kan Musulmai.

Kara karanta wannan

'An bar Arewa a baya,' Remi Tinubu za ta bude kamfani a Legas, an fara korafi

Farfesa Makari ya gana da wasu shugabannin kungiyoyin addini a Najeriya, ciki har da Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Haka zalika tawagar neman hadin kan Musulman ta ziyarci Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi a jihar Kaduna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng