Musulmi Sun Shiga Fargaba a Spain bayan Kawo Dokokin da za Su iya Hana Ibada
- Hukumomin garin Jumilla a Spain sun haramta gudanar da bukukuwan Sallah a wuraren jama’a kamar cibiyoyin da ake haduwa
- Rahotanni sun nuna cewa jam’iyyar PP ce ta gabatar da kudurin, yayin da Vox ta kaurace masa, wasu jam’iyyun kuma suka yi watsi da shi
- Biyo bayan lamarin, al'ummar Musulmai sun bayyana matakin a matsayin wariyar addini da tauye hakkin ‘yan asalin kasar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Spain - Garin Jumilla da ke Kudu maso gabashin Spain ya shiga ce-ce-ku-ce bayan da hukumomi suka haramta amfani da wuraren gwamnati don yin bukukuwan addini.
Wannan mataki ya fi shafar bukukuwan karamar sallah da babba, wadanda Musulmi ke gudanarwa bayan azumin Ramadan da lokacin layya.

Source: Getty Images
The Guardian ta wallafa cewa masu rajin kare hakkin Musulmai da dimokuradiyya sun bayyana matakin da cewa ya sabawa kundin tsarin mulkin Spain wanda ke tabbatar da ‘yancin addini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haramta bukukuwan Musulunci a Spain
An kafa dokar ne a garin Jumilla mai mutane kimanin 27,000, ciki har da kashi 7.5 da suka zo daga kasashen Musulmi.
Jam’iyyar PP ce ta gabatar da kudurin, yayin da jam’iyyar Vox ta kaurace daga kada kuri’a, wasu jam’iyyun hamayya kuma suka yi watsi da shi.
Kudurin ya ce:
“Ba za a sake amfani da wuraren motsa jiki ko cibiyoyin al’umma wajen gudanar da al’amuran addini, al’adu ko na zamantakewa da ba su cikin tsarin mu ba, sai dai idan gwamnati ce ta shirya su”.
Zargin wariya da cin zarafin Musulmai
Shugaban kungiyar Musulmi ta kasar, Mounir Benjelloun Andaloussi, ya bayyana matakin a matsayin wariyar addini da cin zarafin Musulmi.
Rahoton New York Times ya nuna cewa ya ce:
“Ba sauran addinai suke hari ba, addininmu ne kawai suke nema su tauye”.
Ya kara da cewa:
“Bayan shekara 30 na rayuwa a Spain, yau ne karo na farko da na fara jin tsoro.”
Wasu ‘yan siyasa da tsofaffin shugabanni a yankin sun bayyana damuwa da wannan sauyin, inda tsohuwar shugaba a garin Jumilla, Juana Guardiola, ta ce:
“Me ake nufi da ‘yan kasarmu? Yaya ake ciki game da addinin Musululunci."

Source: Getty Images
Tarihin Musulunci a Jumilla da Spain
Garin Jumilla ya kasance karkashin mulkin Larabawa na tsawon shekaru bayan mamayar kasar a karni na takwas.
Alfonso X na Castile ne ya kawo karshen wannan mulki a karni na 13, bayan da aka kulla yarjejeniya da sarakunan Larabawa da ke garin a wancan lokaci.
Spain dai na da dogon tarihi da alaka Musulunci, inda al’adun Musulunci suka shafi gine-gine da tsarin rayuwa a yankuna da dama.
Malamin Musulunci ya rasu a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Abubakar Umar Kokoshe ya rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa malamin ya rasu ne bayan fama da ya yi da jinya a garin Argungu na jihar Kebbi.
Iyalan marigayi Sheikh Abubakar Giro Argungu da sauran malaman addini a Najeriya sun yi ta'aziyya wa iyalan marigayin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

