Sunan Muhammad Ya Kara Farin Jini, Ya Zama Wanda Aka fi Radawa Jariran Ingila
- Bincike ya gano cewa yawan jariran da aka radawa suna Muhammad ya karu da kashi 23 cikin 100 a shekarar 2024
- Rahotanni sun nuna cewa suna Muhammad ya rike matsayi na daya a karo na biyu bayan ya doke Noah da Oliver
- A daya bangaren kuma, rahoto ya nuna cewa suna Olivia ya ci gaba da zama na farko ga ’ya'ya mata tun shekarar 2006
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
England - Hukumar Kidayar Jama ta Ingila da Wales (ONS) ta bayyana cewa suna Muhammad ne ya fi kowanne suna shahara a tsakanin jariran da aka haifa a shekarar 2024, karo na biyu a jere.
A cewar rahoton, an sanya wa jarirai maza 5,721 sunan Muhammad wanda ya nuna karin kashi 23 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Source: Getty Images
Daily Mail ta rahoto cewa suna Noah ya zo na biyu, yayin da Oliver ya biyo baya a na uku — duka kamar yadda aka gani a shekarar 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen da suka shahara bayan Muhammad
Rahoton Arab News ya ce babu jaririn da aka radawa suna Keir a shekarar da ta gabata, sabanin 2023 da aka samu guda hudu da sunan, bayan zaman Keir Starmer Firaminista.
A bangaren mata, sunayen Olivia da Amelia ne suka rike mataki na daya da na biyu a karo na uku a jere.
Sai dai rahoton ya tabbatar da cewa Isla ya fita daga cikin sunaye uku mafi shahara, inda Lily ya maye gurbinsa.
Tun daga 2006, Olivia ya kasance cikin manyan sunaye uku mafi shahara a tsakanin mata, a bana, an sanya wa yara mata 2,761 wannan suna.
Tarihin shaharar suna Muhammad a Ingila
Rahoton ya nuna cewa wannan shi ne karo na biyu da aka samu suna Muhammad ya dare kololuwa a jerin sunaye.
Suna Muhammad na ci gaba da kasancewa cikin sunayen da ake yawan amfani da su fiye da kowanne a cikin shekaru 10 da suka wuce.
Bincike ya nuna cewa Mohammed ya fara bayyana a cikin jerin sunaye 100 da aka fi amfani da su tun 1924, inda ya zo na 91.

Source: UGC
Daga shekarun 1960 ne aka fara ganin karin yawan amfani da sunan, kuma Muhammad ya shiga cikin manyan sunaye a shekarun 1980.
Yanzu sunan ya zama mafi shaharan sunaye, inda ake rubuta shi da Muhammad, Mohammed ko Mohammad, kuma yana da ma’anar “abin yabo” ko “wanda ake godiya gare shi.”
Dalilan shaharar suna Muhammad
Masana na alakanta karuwar suna Muhammad da yawaitar al’ummar Musulmi a Birtaniya, musamman sakamakon hijira zuwa yankin.
Haka zalika ana gani akwai tasirin fitattun ’yan wasa kamar Mo Farah, Mohamed Salah, da Muhammad Ali.
An fitar da sabon fassarar Kur'ani
A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addinin Musulunci a Najeriya ya wallafa sabon tafsirin Kur'ani mai girma.
Dr Dauda Awwal ya bayyana cewa ya shafe shekara sama da 20 yana kokarin fassara Kur'ani a wani salo na dabam.
Legit ta rahoto cewa malamin ya bayyana cewa ya fassara Kur'ani zuwa harshen Yarbanci tare da amfani da wasu harsuna.
Asali: Legit.ng

