Maryam Bukar: 'Yar Arewa Ta Zamo Jakadiya Ta Farko a Majalisar Dinkin Duniya
- Matashiya 'yar Arewa, Maryam Bukar ta samu matsayin jakadiyar zaman lafiya ta duniya ta farko a majalisar dinkin duniya
- Majalisar dinkin duniya ta yaba da yadda fasaharta ta waƙe ke kawo zaman lafiya da haɗin kai musamman ga matasa da mata
- 'Yan Najeriya ciki har da ma’aikatar mata ta kasa sun taya ta murna bisa wannan karramawa da aka yi mata
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Matashiya 'yar Najeriya, Maryam Bukar Hassan ta kafa tarihi bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ta a matsayin jakadiyar zaman lafiya ta duniya.
Maryam ta yi fice wajen amfani da fasahar waƙa da zane wajen jan hankalin jama'a kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya, daidaito tsakanin al'umma, da ƙarfafa matasa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Abba ta dura kan bangaren lafiya, za a gyara asibitoci sama da 200 a faɗin Kano

Source: Facebook
Bincike ya nuna cewa a ranar Juma'a, 25 ga watan Yuli majalisar dinkin duniya ta tabbatar da labarin a shafinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani taron da aka gudanar a birnin New York, jami’an MDD sun yaba da rawar da Maryam ke takawa wajen amfani da kalmomi masu kyau domin kawo haɗin kai a tsakanin al’ummomi.
Maryam Bukar ta kafa tarihi a UN
Maryam Bukar ce mace ta farko da ta zama jakadiyar zaman lafiya gaba ɗaya a tsarin Majalisar Dinkin Duniya.
Za ta yi amfani da fasahar da Allah ya ba ta wajen karfafa zaman lafiya da fahimta tsakanin al’umma a duniya.
Majalisar dinkin duniya ta ce Maryam za ta halarci wani taro da aka shirya gudanarwa a birnin New York.
UN ta yaba da fasahar Maryam Bukar
Sakataren majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan zaman lafiya, Jean-Pierre Lacroix, ya bayyana cewa:
“Sadaukarwar Maryam wajen tallata zaman lafiya ta hanyar zane da waƙe zai ƙara haskaka muhimmancin mata da matasa wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa.”

Kara karanta wannan
Janar Tukur Buratai ya tsage gaskiya, ya fadi abin da ke shigar da matasa ta'addanci
Shi ma sakataren majalisar dinkin duniya mai kula da harkokin siyasa da zaman lafiya, Rosemary DiCarlo, ya ce fasaha tana da tasiri wajen motsa zukata.
Ya ce:
“Maryam ta tabbatar da cewa zane da waƙe na iya kawo zaman lafiya da ƙarfafa haɗin kai.”

Source: Facebook
Najeriya ta taya Maryam Bukar ta murna
Ma’aikatar harkokin mata ta Najeriya ta taya Maryam murna bisa samun wannan karramawa daga majalisar dinkin duniya.
Ma’aikatar ta wallafa a X cewa:
“Wannan matsayi hujja ce kan sadaukarwar Maryam wajen amfani da waƙe da fasaha domin kawo zaman lafiya da adalci.”
Haka zalika, wasu daga cikin ’yan Najeriya a kafafe sada zumunta sun bayyana cewa wannan nasara ta Maryam abin alfahari ce da ke ƙara daga murya da baiwar matasa a duniya.
Tinubu ya yaba wa matan Super Falcons
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba da kokarin matan Super Falcons da suka wakilci Najeriya a Morocco.
Bola Tinubu ya yi jawabi ne yayin karbar tawagar matan bayan lashe kofin zakarun Afrika karon na 10.
Shugaban kasar ya bayyana cewa bai so kallon wasan ba a karon farko saboda tsoron hawan jini idan aka sha Najeriya.
Asali: Legit.ng