Yaƙin Isra'ila: Kalaman Shugaban Amurka kan Harin da Ya Kai Iran Sun Bar Baya da Ƙura

Yaƙin Isra'ila: Kalaman Shugaban Amurka kan Harin da Ya Kai Iran Sun Bar Baya da Ƙura

  • Kalaman shugaban Amurka, Donald Trump kan hare-haren da ya kai Iran sun tayar da ƙura a ƙasar Japan a gabashin nahiyar Asiya
  • Manyan mutane da shugabanni a Japan sun yi tir da kalaman sakamakon kasarsu ce kaɗai aka taɓa harba wa bama-baman nukiliya
  • Trump dai ya kwatanta harin da ya kai Iran da bama-baman nukiliyar da aka harba wa birane biyu a Japan lokacin yaƙin duniya na biyu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Japan - Kasar Japan ta bayyana rashin jin daɗinta kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi wanda ya tuna mata raunin da aka mata a 1945.

Trump dai ya kwatanta hare-haren da Amurka ta kai Iran da harin bama-baman nukiliya da aka jefa wa biranen Hiroshima da Nagasaki na ƙasar Japan a 1945.

Kara karanta wannan

Bayan tsagaita wuta, Iran ta kama masu yi wa Isra'ila leken asiri 6, ta kashe su

Donald Trump ya jawo ma kansa raddi daga Japan.
Japan ta soki kalaman Trump na kwatanta harin da ya kai Iran da na yakin duniya na II Hoto: @DonaldTrump
Source: Getty Images

Tribune Online ta tattaro cewa wannan kwatance bai yi wa shugabanni a Japan daɗi ba, inda suka yi wa Trump rubdugun martani, suna kira da ya janye su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Wancan harin ne ya kawo ƙarshen yaƙin. Ba na son in ba da misalin Hiroshima, ko Nagasaki, amma kusan hakan ne ya faru," in ji Trump.

Kalaman shugaban Amurka sun tada ƙura

Wannan furuci na Trump ya fusata manyan mutane a Japan, waɗanda har yanzu suna jin raɗaɗin bama-baman nukiliyar da aka harba masu a yaƙin duniya na II.

Shugaban garin Nagasaki, Shiro Suzuki ya ce:

"Idan wannan kalma da Trump ya faɗa na nufin yana goyon bayan amfani da nukiliya, to wannan abin ƙyama ne gare mu saboda mun taɓa fuskantar hakan."

Mimaki Toshiyuki, ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira daga harin kuma ɗan tawagar da ta taɓa lashe Nobel Peace Prize, ya ce kalaman Trump sun wuce gona da iri.

Kara karanta wannan

An taso Firaministan Isra'ila a gaba bayan gama yaƙi da Iran, ya fara roƙon arziƙi

“Na ji matuƙar takaici. Abin da ke zuciyata yanzu fushi ne kawai,” in ji Teruko Yokoyama, wata mace da ta tsira daga harin.

An yi zanga-zanga kan furucin Trump a Japan

A matsayin martani ga kalaman Trump, wasu daga cikin waɗanda suka tsira daga harin nukiliya a Japan, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Hiroshima ranar Alhamis, inda suka nemi Trump ya janye furucinsa.

Haka kuma, ‘yan majalisar birnin Hiroshima sun amince da ƙuduri a wannan rana, wanda ke ƙin yarda da duk wani furuci da ke neman halasta amfani da makaman nukiliya.

Da aka tambayi ko Japan za ta shigar da ƙorafi a hukumance, Sakataren Gwamnatin Japan, Hayashi Yoshimasa, ya ce Tokyo ta sha bayyana matsayinta kan nukiliya ga gwamnatin Amurka.

Shugaban Amurka, Donald Trump.
Gwamnatin Japan ta jaddada matsayarta na adawa da amfani da makamin nukiliya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A rahoton BBC, Trump ya yi wannan kwatanci da ya jawo surutu ne yayin da yake mayar da martani kan wani rahoton sirri, wanda ya nuna cewa hare-haren Amurka ba su yi tasiri kan shirin nukiliyar Iran ba.

Sai dai Trump ya nace cewa harin ya “lalata gaba ɗaya” damar Iran, kuma ya koma da shirin nukiliyarta “shekaru masu yawa baya."

Kara karanta wannan

Jagororin adawa sun dura a kan Trump, an gargade shi kan shiga shari'ar Netanyahu

Japan ce kaɗai ƙasa a duniya da ta taɓa fuskantar harin bama-baman nukiliya, wanda ya sa ta ke ci gaba fafutukar hana amfani da wannan makamai.

Jerin ƙasashen da suka mallaki nukiliya

A wani labarin, mun kawo maku jerin sunayen ƙasashen da suka mallaki makamin ƙare dangi, wanda aka fi sani da nukiliya da adadin da suke da shi.

Ƙaasashen da ke da wannan makami mai haɗari watau nukiliya sun kai tara, tun bayan kera na farko a 1945 wanda ya tilasta samar da yarjejeniyar NPT.

Amurka da Rasha na da kimanin kaso 87 cikin 100 na duka makaman nukiliya da ake da su a duniya a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262