'Ba Haka ba ne,' Iran Ta Yi Martani bayan Trump Ya Ce zai Zauna da Ita kan Nukiliya

'Ba Haka ba ne,' Iran Ta Yi Martani bayan Trump Ya Ce zai Zauna da Ita kan Nukiliya

  • Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen Iran ya ce ba su da wani shirin ganawa da Amurka a mako mai zuwa
  • Wannan ya saba da furucin Shugaba Donald Trump wanda ya ce za su gana da Iran don cimma yarjejeniya
  • Fadar White House ta ce har yanzu ba a tsara wata ganawa ba, duk da cewa ana ci gaba da tuntuɓar juna ta hannun wasu ƙasashe

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Kasar Iran ta bayyana cewa ba ta da wani shiri na ganawa da Amurka a mako mai zuwa, sabanin ikirarin da Shugaban Amurka, Donald Trump.

Shugaba Donalad ya yi ikirarin cewa za su gana da wakilan Tehran don tattauna makomar yarjejeniyar nukiliya.

Iran ta ce bata san da zaman da Amurka ta ce za ta yi da ita ba
Iran ta ce bata san da zaman da Amurka ta ce za ta yi da ita ba. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Reuters ta wallafa cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan talabijin na gwamnati.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: Trump zai shawo kan Iran da dala biliyan 30, manyan alkawura

Ministan ya ce Tehran na nazari kan amfanin wannan ganawa da kuma ko tana cikin maslahar ƙasar.

Araqchi ya ce sun riga sun gudanar da zaman tattaunawa guda biyar da suka katse bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliya na Iran.

Iran na nazarin tattaunawa da Amurka

Ministan ya bayyana cewa hare-haren da aka kai sun haifar da gagarumar illa ga cibiyoyin nukiliya na ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa hukumomi na ci gaba da tantance yadda hakan zai shafi matsayin Iran a matakin diflomasiyya.

Abbas Araqchi ya ce barnar da aka yi ba ƙarama ba ce, yana mai nuna cewa nazarin da ake yi yanzu zai zama jigo wajen yanke matsayar ko za a koma teburin tattaunawa da Amurka.

Shi dai shirin nukiliya na Iran, a cewar Tehran, domin samar da makamashi ne ga fararen hula, yayin da Amurka da Isra’ila ke zargin cewa ana amfani da shi ne wajen kera makaman nukiliya.

Kara karanta wannan

Bayan yaƙi da Isra'ila, Shugaba Trump ya faɗi abin da Amurka za ta tunkari Iran da shi

Maganar White House kan zama da Iran

A nata bangaren, mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce babu wata ganawa da aka tsara da Iran a halin yanzu, duk da ikirarin Shugaba Trump.

Rahoton CBS ya nuna cewa White House ta ce:

“Babu wani lokaci na zama da aka tsara yanzu haka,”

Leavitt ta fadi haka ne yayin taron manema labarai a ranar Alhamis, tana mai cewa sun tattauna da wakilin musamman na yankin Gabas ta Tsakiya.

Fadar White House ta karyata maganar Trump ta ganawa da Iran
Fadar White House ta karyata maganar Trump ta ganawa da Iran. Hoto: Donald J. Trump
Source: Getty Images

Ta kara da cewa:

“Idan akwai wata ganawa, za mu sanar da ku kamar yadda muke yi a kullum.”

A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a taron NATO da aka gudanar a birnin Hague na ƙasar Netherlands, Shugaba Trump ya ce za su gana da Iran domin tattauna yiwuwar yarjejeniya.

Donald Trump zai yi wa Iran tayin $30bn

A wani rahoton, kun ji cewa, shugaban Amurka Donald Trump na shirin yi wa Iran tayin Dala biliyan 30.

Kara karanta wannan

Trump ya yi tonon silili a taron NATO, ya ce Isra'ila ta sha wuta a hannun Iran

Baya ga haka, Donald Trump na shirin cire jerin takunkumi da aka kakabawa Iran a shekarun baya.

An gano hakan ne a cikin wasu takardun sirri da White House ke tattarawa a kokarin shawo kan Iran ta dawo teburin sulhu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng