Abin Boye Ya Fito: Trump zai Shawo kan Iran da Dala Biliyan 30, Manyan Alkawura
- Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Donald Trump na shirin tattaunawa da Iran don farfado da yarjejeniyar nukiliya
- Akwai yiwuwar Iran za ta samu tallafin har dala biliyan 30 don gina sabon shirin nukiliya na samar da makamashi
- Gwamnatin Trump ta ce duk tattaunawar da za a yi, za ta hada da sharadin cewa Iran ba za ta sarrafa sinadarin uranium ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Rahotanni daga wasu manyan majiyoyi sun bayyana cewa gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump na ƙoƙarin farfado da tattaunawa da Iran.
Hakan na zuwa ne duk da yanayin rashin jituwa da hare-haren soja da suka faru a kwanakin baya tsakanin Iran da Isra’ila.

Source: Getty Images
Rahoton CNN ya nuna cewa wasu daga cikin ƙasashen Larabawa da ke haɗin gwiwa da Amurka sun shiga cikin waɗannan tattaunawar ta ɓoye da wakilan Iran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin abubuwan da ake shiri tattaunawa akwai yiwuwar sassauta takunkumin tattalin arziki da Iran ke fuskanta.
Maganar zuba $30bn a Iran daga kasashe
Rahoton sirri da aka samu ya bayyana cewa an tattauna yiwuwar zuba jarin Dala biliyan 30 a wani sabon shirin nukiliya da Iran za ta aiwatar domin samar da makamashin lantarki.
An bayyana cewa kuɗin ba zai fito kai tsaye daga Amurka ba, amma za a bukaci ƙasashen kawance a yankin Gulf su dauki nauyin hakan.
Haka zalika, ana duba yiwuwar maye gurbin cibiyar Fordow da aka lalata da wani sabon tsarin da ba ya sarrafa uranium, wanda Iran ta sha nunawa cewa tana buƙata domin ci gaban fasaha.
Donald Trump zai cirewa Iran takunkumi
Cikin tayin da ke kunshe a yarjejeniyar, akwai yiwuwar cire takunkumin da zai bai wa Iran damar amfani da dala biliyan 6 da ke ajiye a wasu bankunan ƙasashen waje.

Kara karanta wannan
'Ba haka ba ne,' Iran Ta yi martani bayan Trump ya ce zai zauna da ita kan nukiliya
Majiyoyi sun ce duk da cewa Iran na da buƙatu da yawa, akwai ƙarfin gwiwa daga bangaren Amurka cewa za su iya cimma matsaya, muddin Iran za ta dakatar da shirin nukiliyarta.

Source: Getty Images
Maganar Trump kan yarjejeniya da Iran
Duk da irin ƙoƙarin da ke gudana a bayan fage, Shugaba Trump ya fito fili ya nuna cewa bai damu da cimma yarjejeniyar ba.
Wakilinsa na musamman, Steve Witkoff, ya jagoranci wata ganawa ta sirri a Fadar White House da wakilai daga yankin Gulf a ranar Juma’a da ta gabata, kafin Amurka ta kai hari Iran.
Ana sa ran idan an kammala tsara takardar sharuddan yarjejeniyar, za a iya gabatar da ita ga bangaren Iran domin samun amincewa.
Iran ta hadu da Rasha da kasar China
A wani rahoton, kun ji cewa ministocin tsaron Iran, Rasha da China sun gana a China bayan gama yaki da Isra'ila.
Hakan na zuwa ne yayin da shugabannin kasashen da ke karkashin NATO suka gana a kasar Netherlands.
Rahotanni sun nuna cewa ganawar ta mayar da hankali a kan yanayin tsaro a duniya da kuma yakin da aka yi da Iran da Isra'ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
