An Taso Firaministan Isra'ila a Gaba bayan Gama Yaƙi da Iran, Ya Fara Roƙon Arziƙi
- Bayan kammala yaƙi da Iran, Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanayahu zai fuskanci shari'a kan zarge-zargen rashawa
- Netanyahu ya roki kotu ta taimaka da ɗage wannan shari'a duba da yanayin da ƙasar ke ciki na yaƙi da kungiyar Hamas da ke Gaza
- Kwanan nan ne aka ji Shugaban Amurka, Donald Trump ya bukaci a dakatar da wannan shari'a ko kuma a yi wa Netanyahu afuwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Israel - Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya roki kotu ta ɗage zaman sauraron shari'ar da ake masa saboda ƙalubalen da ya fuskanta a ƴan kwanakin nan.
Netanyahu ya yi wannan roko ne ta hannun lauyansa, Amit Hadad a daidai lokacin da ake shirin gurfanar da shi a gaban kotun kan zarge-zargen rashawa.

Source: Getty Images
Firaministan ya roki a ɗage gurfanar da shi

Kara karanta wannan
Jagororin adawa sun dura a kan Trump, an gargade shi kan shiga shari'ar Netanyahu
Tashar France 24 ta rahoto cewa Amit Hadad, ya roƙi a dage zaman da Netanyahu zai gurfana ya yi bayani saboda “halin da ake ciki a yankin da kuma duniya baki ɗaya.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Muna roƙon kotu, cikin girmamawa da ta soke zaman sauraron shaidar Firaminista da aka shirya yi cikin makonni biyu masu zuwa,” in ji Amit Hadad.
Lauyan ya ce Netanyahu yana cikin wani yanayi da ya sa dole ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya wajen kula da harkokin ƙasa, diflomasiyya da tsaro.
Ya ƙara da cewa ya kamata kotu ta duba rikicin da Isra'ila ta yi da Iran da kuma ci gaba da fafatawa da Hamas a Gaza inda har yanzu ake riƙe da fursunonin ƙasar.
Trump ya roki a yi wa Netanyahu afuwa
A ranar Laraba, shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana shari’ar da ake yi wa Netanyahu a matsayin “farautar siyasa” wato wani shiri na siyasa don bata masa suna.
Trump ya ce:
“Ya kamata a soke wannan shari’a nan take, ko kuma a yiwa Netanyahu afuwa, domin shi babban jarumi ne."

Source: Getty Images
Bayan wannan kalamai na shugaban Amurka, Netanyahu ya mika godiya ga Trump bisa “irin goyon bayan ban mamaki da yake ba Isra’ila da al’ummar Yahudawa.”

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An kama wani ɗalibin Jami'a bisa zargin yiwa Iran leken asiri a Isra'ila
“Ina fatan ci gaba da yin aiki tare da kai wajen yaƙi da makiyanmu, ’yantar da fursunoninmu, da kuma samar da zaman lafiya," in ji shi.
Jagoran adawa a Isra'ila ya gargaɗi Trump
Sai dai shugaban hamayya a Isra’ila, Yair Lapid, ya gargadi Trump da kada ya tsoma baki cikin al’amuran cikin gida na ƙasar Isra'ila.
“Muna gode wa Shugaba Trump, amma bai kamata ya tsoma baki cikin shari’ar da ke faruwa a ƙasarmu mai ‘yanci ba,” in ji Lapid.
Benjamin Netanyahu shi ne Firayim Ministan da ya fi kowanne jimawa a kan mulki a tarihin Isra’ila, kamar yadda Al-Jazeera ta tattaro.
An sha dage wannan shari’a da ta fara a watan Mayu 2020, kuma har yanzu Netanyahu yana musanta duk wnai laifi da ake zarginsa da aikatawa.
Netanyahu ya yi ikirarin samun nasara kan Iran
A wani labarin, kun ji cewa Firaministan Isra'ila ya yi ikirarin cewa ƙasarsa ce ta yi nasara a yakinnta da Iran, wanda ya shafe kwanki 12 ana musayar wuta.
Netanyahu ya bayyana cewa Isra’ila ta samu nasara mai cike da tarihi kan Iran, wadda za ta kasance abin tunawa na tsawon zamani.
Firaministan ya ƙara da cewa Isra’ila na fuskantar barazanar rugujewa nan gaba kadan da ba ta gaggauta ɗaukar mataki ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng